Sashe 55
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kama wacce ta tuna wani abun sai ta zabura da jajayen idanun ta ta fita zuwa saman Baba gabanta yana fad'uwa, a zaune ta ganshi yayi shiru alamun ransa a b'ace yake tayi sallama taga ya d'ago ya kalle ta bai amsa ba ta k'arasa ciki ta zauna akan carpet tace, "Dan Allah Baba kayi hak'uri, wallahi Allah ban cewa Asad ya sake ni ba shine ya sake ni tun muna Egypt sannan kuma ya dawo yau ya k'arashe saki biyun da suka rage na rantse da Allah babu laifina balle laifin Umma, kayi hak'uri ka yafe mana" ta k'arasa fad'a cikin kuka sosai dan zuciyar ta tayi rauni.
Shiru Baba yayi bai amsa ba ta kuma cewa, "Dan Allah Baba kayi hak'uri wallahi bani da laifi ko kad'an" sai ta fashe da kuka mai tsuma zuciya ta kifa kanta a cinyoyin ta tana kuka. Baice kanzil ba ta jima tana kukan kafin ta goge idanunta ganin kallon ta baiyi ba ta tashi ta sauka daga saman nasa ta koma d'akin ta tayi lamoo a kan gado babu alamun bacci a cikin idanunta.
*☆☆☆*
"Kin tabbatar kin zuba masa a cikin ruwan yasha?." Jidda rik'e da waya a hannunta tace, "Wallahi Mum yasha har na wankan ma dana zuba masa yayi wankan dashi, nayi mamakin yadda ya sauko lokaci d'aya haka." Mum tayi y'ar dariya tace, "k'yale Jidda tukunna ma kenan, ai na rantse da Allah sai Rabi tayi kuka da idanunta, sai ta gwammace bata bawa Asad kujerar sarautar nan ba."
"Shiyasa nake yin Mum wallahi, Allah yaja da ranki."
"Amin. Kedai kiyi duk abinda nace miki kar ya dame ki dan kinga baya neman ki akwai dalilin hakan sa kuma za'ayi maganin abun nan kusa."
"To Mum."
"To sai da safe ki tashi ki tafi b'angaren sa ki tabbatar ki shafe jikin ki da wad'an nan turarukan."
"Okay Mum, Bye" tana fad'a ta kashe wayar tana farin ciki.
Shiryawa tayi kamar ko yaushe ta d'ora hijjabi ta fito jakadiyar ta tana take mata baya zuwa b'angaren mai martaba ta k'ofar cikin gidan dan farin ciki take ji dashi tafi so kowa ya ganta bazata bi ta inda baza'a ganta ba. Sunzo tsakiyar harabar gidan wutar gidan gabad'aya ta d'auke d'uf duhu ya mamaye duka gidan a guje ma'aikatan gidan akayi wajan wuta dan a gyara dan kowa yayi mamakin d'aukewar ta.
Ba tsammani Jidda taji an jata wani waje an toshe mata baki zatayi ihu yace, "Shiiiii! Karki ce komai." Kallon sa take idanunta a waje tana so ta banbance Asad ne ko Aliyu ya kalle ta yace, "What are you thinking about?."
"Aliyu?." Ya d'aga mata kai yace, "Yeah it's me." Ta kwace hannunta da yake rik'o tace, "Meyasa ka kawo ni nan? Sai wani ya ganmu?."
"Ki daina increase volume mana, i want to talk to you that's why na kashe wutar gidan."
"Daman kaine ka kashe wutar?."
"Yeah nine."
"For what reasons?."
Ya kalle ta yace, "stop shooting mana, ko ina kina so a ganmu ne?." Ta kalli bayanta taga babu wanda yayo wajan da suke tace, "Ina jinka."
"Asad yyi having sex dake?."
Idanun ta ta zaro tana kallon shima ya zaro idanun sa yace, "Answer me bana son wani kwana-kwana malama."
"To ina ruwan ka da wannan kake tambayata?."
"Because ina so na taimake ki ne in ba haka ba a haka zaki k'are a gidan nan babu wani cigaba sabida Asad yayi damage bazai tab'a yiwa kasancewa da wata ba; in fact bazai haihu ba."
"What?." Ya wara idanu yace, "yes ke kin san bazan miki k'arya ba, in kuma kina tunanin wasa nake ki gwada ce masa kina son ya baki hakkin ki kiga me zai faru."
"Wanne irin taimako kake fad'a zaka min?."
"Ki fara tabbatarwa then sai ki neme ni, and......" ya fad'a yana lalubo aljihun sa ya d'auko wani magani ya bata yace, "karb'i."
Ta karb'a yace, "Ki tabbatar kin bashi wannan magani yasha in kikayi sa'a zai samu lafiya iya na yau in kuma bai samu lafiya ba shikenan sai dai kiyi hak'uri." Kallon sa take kamar bata yadda ba ya rik'e hannun ta yace, "trust me bazan cutar dake ba, ina sonki ke kin sani that's why nake nema miki duk abinda kike so." Ta sauke numfashi tace, "ta yaya zan amince?."
"U know bazan cutar Asad ba ko kad'an, I love him so much so bazan cutar dashi ba."
Kai ta girgiza kana tace, "Okay I will try it now." Yayi murmushi tare da yi mata kiss a goshi yace, "That's my friend." Ya kalle ta yace, "Jeki, zan saka a dawo da hasken." Ta juya ta tafi yayi murmushi yana sosa gemun sa yana hango yadda zai same ta a b'agas ba tare da wata matsala ba.
Tana dawowa inda take haske ya dawo ta nufi b'angaren Mai martaba ta hau sama ta same shi a zaune ya dafe kansa yayi shiru alamun akwai abinda yake damun sa, zama tayi kusa dashi tace, "akwai abinda yake damun sarkina?." Kallonta yayi ya girgiza kai alamun babu komai ta tashi ta kawo masa lemon da taga yana yawan sha wato five alive ta had'o da cup ta zuba masa tace, "take it pls." Kamar bazai karb'a ba sai kuma ya karb'a yasha ya ajjiye cup d'in ta bishi da kallo sai taga ya tashi ya shiga d'akin karatu baice komai ba. Murmushi tayi ta girgiza kai ta tashi ta shiga d'akin sa ta shafe jikinta da turaren ta fito falo ta zauna.
Bai jima ba ya dawo ya wuce ta zuwa d'aki ya jima da shiga tabi bayan sa ta ganshi da laptop a cinyar sa yana dannawa ta k'araso ta d'auke laptop d'in ta zauna a cinyar sa ta sak'alo hannun ta wuyan sa ta kwantar da kanta a jikin sa. Khamshin turaren ta ya bugar dashi sosai ta fara kissing d'in sa a wuya da fuskar sa a hankali. So yake ya daure ya kawar da ita daga jikin sa but turaren yayi tasiri a jikin sa sosai lokaci d'aya ya fara fita daga hankalin sa yana jin kansa yana sarawa sosai.
Kamar wanda ya tuna wani abun sai ya firgita ya ture ta daga jikin sa ya mik'e tsaye ta rik'e hannun sa tace, "Please My king." Ya sauke numfashi yace, "I'm sorry" yana fad'a ya zame hannun sa ya fita daga d'akin ta cure waje d'aya ta fashe da kuka dan a wannan lokacin ta kai mak'ura. Ta jima tana kukan ta kafin ta share hawayen ta ta d'auki hijjabin ta ta fita daga d'akin ta sauka ta fita daga b'angaren ma gabad'aya dan ranta ya b'aci.
Gabad'ayan ta wani iri take jinta ta kasa jurewa tana shiga d'aki ta d'auki wayar ta hannu na rawa ta danna number Aliyu, ba jimawa ya d'auka tace, "i need your help Aliyu." Daga can b'angaren yayi kyakykyawan murmushi yace, "Zan taimake ki kar ki damu, ki nutsu zan miki duk abinda kike so ki daina kuka" yana fad'a ya yanke wayar yana bin wayar da kallo yana juyawa ta a hannun sa yana murmushi yace, "Lokaci ya fara Asad, bazaka iya yin komai ba duk abinda ka mallaka sai ya dawo tafin hannuna" yayi murmushi ya kwantar da kansa a jikin kujera yana murmushi zuciyar sa cike da farin ciki.
FitattuBiyar
Nana Haleema.
[17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*053.*
A zaune yake a k'asa kusa da k'afafun ta kamar koda yaushe in ya kai mata ziyara ta d'ora k'afa kan d'aya da file a hannun ta tana shan khamshi ji take kamar bazata iya magana ba sabida izzar da take ji da ita a wannan lokacin, file d'in ta mik'a masa tace, "Saka min hannu akai." Asad ya karb'i file d'in yaga akwai biro a ciki yana karanta takardar daki-daki har ya fahimci ta maye ya d'ago zaiyi magana tace, "Abinda na saka ka nace kayi ba magana ba."
Ya d'an gyara zaman sa zuciyar sa cike da tunanin sanya a hannu a takardar amma babu damar musu, kallon sa take yi ganin yana juya biron tace, "baza kayi bane?." Ba yadda ya iya haka ya saka hannu ya rufe ya mik'a mata ta karb'a tana murmushi kana tace, "Sai abu na gaba, ina so filin can na baya a tasar min gini a cikin sa bazai yu ina matsayin babar ka na zauna waje mai iri d'aya da sauran ba, ya zama dole a banbanta ni."
Asad yace, "in sha Allah za'ayi." Mama tace, "Sai batun bawa Aliyu da Hydar sarauta banji kace komai bafa." Asad yace, "Aliyu yace baya so Hydar kuma baya nan shiyasa ba'a yi komai ba."
"To yanzu meye a gaba?."
"Ina da meeting da shugaban k'asa gobe a Abuja, then zan wuce Germany wajan Abba daga nan zan shiga madina akwai taron da aka gayyace ni."
Mama ta yatsine fuska jin yayi maganar mahaifin sa ita sam bata son ma abinda zai dawo da mahaifin sa kar yazo ya takura mata ya hanata rawar gaban hantsi gwara yaje can ya k'arata tace, "da matar ka zaka tafi?." Asad ya girgiza kai alamun a'a tace, "Meyasa bazaka tafi da ita ba?." Ya lumshe ido ya bud'e kana yace, "Bazan jima ba."
"Allah ya kiyaye."
"Amin. Godiya nake Allah yaja da rai" ya furta a tusashe cikin girmamawa matuk'a.
Shiru ya ratsa tsakani kafin tace, "Zaka iya tafiya."
"A huta lafiya" ya furta yana mik'ewa yana takawa a hankali ya fita daga falon aka take masa baya mutane sama da goma yana gaba ana binsa a baya ko tsuntu baya giftawa ta wajan sai in ya wuce sabida tsabar girmamawa.
Mota ya shiga aka saki jiniya aka d'auki hanyar Bauchi kai tsaye airport suka nufa har gaban private get motar taje ya fito ya shiga jirgi shida shamakin sa da Uncle suka wuce Abuja.