Sashe 86
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ummulkhairi ta bawa tace taje ta siyo ta had'a su da Khalil tace ya rakata, jikin Ummulkhairi a sanyaye suka tafi suka je suka siyo a pharmacy da yake can bakin titi suka siyo duka abinda ta rubuta suka d'auko hanyar dawowa gida. Farar mota suka gani a ajjiye suka zo giftawa ta motar suka ji ance, "Khalil ko?." Juyawa sukayi dukkan su suka had'a ido da wanda yake zaune a ciki ya sauke glass kad'an ya kalle su da murmushi Ummulkhairi tace, "Ina wuni."
"Lafiya" ya amsa a tak'aice Khalil yace, "Kai ba wannan ne sarki ba?, wallahi shine, Anty Khairi sarki ne fa" ya fad'a a rud'e yana kallonta. Murmushi yayi kad'an yace, "shiii" alamun yayi shiru ya daina magana.
Khalil yana ta murmushi yaga sarki Asad ya sauke numfashi yana bin su da kallo kafin yace, "Ina kuka je?." Khalil yace, "Mun siyo magani za'a bawa Anty Rauda bata da lafiya, Baba yayi mata duka har bakinta sai da ya fashe. Kasan wai me akace?" Sai yayi shiru yana kallon sa.
Hankalin sa ya tattara gabad'aya akan Khalil ya girgiza kai alamun a'a Khalil yace, "Ance wai tana da ciki shine Baba ya mata duka jikinta duk ya fashe" ya fad'a kamar zaiyi kuka.
"Kai Khalil baka da hankali?" Khairi ta fad'a tana talle masa k'eya taja hannun sa tana fad'in, "Wallahi na sake ji ka fad'awa wani wannan maganar sai na fad'awa Baba ya zane ka kaima, banza mai surutun tsiya" ta fad'a suna yin gaba tana jan hannun sa.
"Duka!" Ya maimaita a fili yana kallon su har sukayi masa nisa bai d'auke idanun sa daga kansu ba, ransa yaji yayi mugun b'aci nan take abinda ya fito yi a sirrance ya fita daga ransa ya ya d'aga bak'in glass d'in motar yadda duk nacin ka baza ka gane waye a ciki ba ya juya motar ya bar unguwar yana ji zuciyar sa na tafasa gabad'aya komai ya tsaya masa jin kalmar duka bayan ance tana da ciki kuma.
Bayan sun koma aka yiwa Umma allura aka bata magani sai tayi bacci itama Raudan suka lallab'a ta Allah ya taimaka tayi baccin gidan ya zama shiru babu wanda yake magana kowa da nasa tunanin a zuciyar sa.
Sai yamma Rauda ta farka jikinta yayi mata tsami ta tashi zaune babu kowa a d'akin ta kalli fuskar ta a mudubin d'akin fuskar ta ta kumbura sosai ga jini a idanun ta ya taru sabida marin da tasha a hannun Baba. Sakkowa tayi daga kan gadon amma sai ta kasa tsayuwa sabida k'afar ta bazata iya d'aukar ta ba tayi saurin dafa bango tana tafiya kanta ko d'ankwali zuwa d'akin Umma.
A falo ta tarar dasu har Umma suna zaune a gefen ta suna ta bata hak'uri suka hango Rauda tana tafiya tana layi kamar zata kifa, fuskar ta da suka a kunbure shine ya sake karya musu zuciya ta k'araso gaban Umma ta zube maganar ta bata fita sosai tace, "Umma dan Allah ki...." Umma ta runtse idanunta tace, "Ki tashi ki bani waje Rauda wallahil azim bana son ganin ki, bana son kallon fuskar ki ki tashi kafin na saka k'afa nayi ball dake a wajan nan." Yayar mu ta taso ta d'aga Rauda daga wajan tace, "Koma ki huta ranta a b'ace yake sosai bazata saurare ki ba."
Shigar da ita tayi d'aki ta zaunar da ita ta zauna itama a gefen ta tace, "Rauda waye ya miki ciki? Anas ne kowa?." Sai kawai ta kuma fashewa da kuka ta kifa kanta a kafad'ar Yayar mu tana kuka sosai ita kuma tana bubbuga bayanta a hankali tausayin ta na sake shiga jikinta dan su kam sun yadda da ita tunanin su fyad'e akayi mata ba yin kanta bane.
Yaya Nafisa ta shigo da abinci da shayi mai zafi ta zauna tace, "Rauda karb'i shayi kisha sai kici abinci." Kai take girgizawa tace, "bazan iya sha ba, bazan iya ba. Dan Allah ku fad'awa Baba ya kashe ni bana son rayuwata nima."
Duk sai jikin su ya kuma yin sanyi suka dinga rarrashin ta amma baya aiki dan batayi shiru ba kuma bata ci komai ba. Wanka suka saka tayi da ruwa mai zafi sanda ta fito sai da suka tsorata da shatin bulalar jikinta duk bata da hasken fata amma fatar tayi ja sosai duk ta tashi wani wajan ya fashe.
Kaya ta saka tayi sallar la'asar a zaune bayan ta idar ta d'ora hannun ta akan cikinta tunawa da tana da ciki sai taji kamar ta had'd'iye zuciya ta mutu da bak'in cikin da take ji a ranta har gwara ma ace ta mutu ta huta kawai. Basu barta ita kad'ai ba dan zuciya zata iya d'aukar ta yiwa kanta illah.
Har magriba babu wacce ta tafi a cikin su bayan anyi sallah ne su Baba da Kawu Badamasi suka shigo aka kira kowa aka bada umarnin fito da Rauda. Suna rik'e da ita aka zaunar da ita a k'asa suma duk suna k'asa iyayen ne kawai a kan kujera. Kawu Badamasi yace, "Haba Adamu, wannan wanne irin hukunci ka yiwa wannan yarinyar? Kalli fuskar ta da idon ta yadda ya koma."
Shiru yayi suma kowa yayi shiru Kawu Badamasi ya kalle ta yace, "Rauda!." Ta d'ago a hankali ta kalle shi yace, "Subahanallah haka idon naki jini ya taru? Gaskiya baka kyauta ba duka ba hukunci bane." Shiru aka kuma yi ba'a amsa ba yace, "Rauda tsakanin ki da Allah cikin waye a jikin ki?, kinga maganar bikin akeyi ga wannan abin da ya taso a yanzu babu maganar aure dan ba'a aure da ciki. Cikin waye a jikin ki."
Shiru tayi ta kasa magana sai kuka Kawu Mansur yace, "ba kuka akace kiyi mana ba, tambaya ce guda d'aya kawai ki bamu amsa." Nan ma shiru batayi magana ba Baba ya fusata yace, "Kun gani ko? Bata jin ko wanne yare sai duka ku barni na b'alla ta in yaso sai tayi bayani." Kawu Mansur yace, "Dan Allah ka sakawa zuciyar ka salama, ka barmu zamu tambaye ta da kanmu."
"Rauda ke muke saurare cikin waye a jikin ki?." Nan ma shiru ba amsa sai kuka Kawu Badamasi ya kuma cewa, "Ko shi Anas d'in ne yayi miki?." Ta girgiza kai alamun a'a tana kuka Baba ya fusata ya mik'e ya k'arasa inda take ya d'aga hannu zai dake ta yaji ance, "Dan Allah Baba ka bar dukan ta haka!." Cak ya tsaya jin muryar wanda ya sani a kwanakin baya bai sauke hannun ba ya juyo yana kallon inda yaji maganar kowa ya zubawa k'ofar ido ana kallon wanda yake tsaye cikin zallar al'ajabi da tsoro da kuma mamaki...........
[17/12, 10:42 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*069.*
A tsaye yake cak fuskar sa a bayyane duk da babu annuri a cikinta amma tayi haske sai shek'e take yi idanun sa akan inda Baba yake yana shirin dukan Rauda nan kawai yake kallo dan tunanin sa a wajan yake. sanye yake da manyan kaya na sakarai daga kallon aikin jikin su basai an fad'a ba kasan ba k'aramin mutum bane zaiyi wannan shigar sai wanda ya amsa suna basarake kuma mai abin hannu.
Kansa yayi nadin buzaye ya zagaye fuskar sa da hirami kalar kayan jikin sa takalmin k'afar sa irin aikin jikin kayan sa ne yana tsaye cak cikin nustuwa da ta game ko ina na jikin sa yana kallon su.
Dukkan su mik'ewa tsaye sukayi Baba ya juyo da sauri ya k'araso wajan yana jinjina yace, "Allah yaja zamanin mai martaba barka da zuwa, bismillah" ya fad'a yana bashi hanya alamun ya wuce shi kuwa Rauda kawai yake kallo dan yanayin ta ya bashi tsoro. "Barka da zuwa ranka ya dad'e" Kawu Badamasi ya fad'a yana kallon sa cikin girmamawa suke maganar.
Sai a sannan ya d'auke idon sa daga kanta ya murmusa kad'an Baba yace, "Ranka ya dad'e tsayuwa ba taka bace, ayi mana alfarma a zauna dan Allah." Ba musu ya taka har tsakiyar falon da takalmi a k'afar sa gujerar da ta kasance babba a ciki ya zauna, Baba zai zauna a k'asa yace, "Dan Allah Baba" ya fad'a yana nuna masa kan kujerar kusa dashi alamun ya zauna. Baba yace, "Wane mutum" ya fad'a yana zama a k'asa duk kowa ya zauna a kasa sai ahi kad'ai ne a akan kujera.
"Barka da zuwa ranka ya dad'e, da fatan mai martaba yazo lafiya?." Shiru ya d'an yi kafin yace, "Alhamdulillah, fatan bamu zo a lokacin da bai kamata ba."
"Ko wanne lokaci mai martaba yaso ziyara daidai ne a wajan mu, mai martaba ya ziyarce ka ma ai babban abin alfahari ne a gare mu baki d'aya" Kawu Mansur ya fad'a da girmamawa shima.
Kwarjinin sa ya cika falon haka khamshin sa gabad'aya matan tunda suka gaisa sun kasa cewa komai har basa son dagowa ma su kalle shi sabida kwarjinin da yake musu kallon sama sai ka shirya balle magana. Shiru ya ratsa falon shi ya rasa me zaice nauyi yake ji a zuciyar sa ya kasa furta komai su kuma jiran yayi masa suke yi.
Dak'yar ya iya had'a kalmar yace, "Ina neman afuwar ku dukka akan abubuwan da suka faru a baya, ina fatan za'a yafe ni." Baba yace, "Mai martaba da kansa yake neman afuwar mu? Mu su waye da har mai martaba guda zai mana laifi..? Allah yaja da ranka ai mu bamu isa mu rik'e mai martaba a zuciyar mu ba duk abinda ya faru mun d'auka k'addara ce kuma ta riga fata." Ya girgiza kai yana cize bakin sa yana kallon mutanen falon duka fuskokin su babu annuri ga Umma a zaune kamar mara lafiya sai yaji jikin sa ya sake jin sanyi.
Ya d'an jima kafin ya kuma cewa, "Baba ina neman alfarma a wajan ka." Baba ya gigice ya gyara zama yace, "Allah ya kara maka lafiya ai umarni kawai za'a bani amma ina mai martaba ina neman alfarma a waje na."
"Akwai ambulance a waje ina so za'a kaita asibiti" ya fad'a a sanyaye ba tare da ya kalli Baban ko ita Raudan ba.