← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 131

Sashe 103

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dukkan su juyawa sukayi suna kallon sa ya d'aga gira guda biyu yayi murmushi mai kama da dariya kafin ya sauke numfashi ya kalli kowa na falo sai kuma ya tab'e baki har lokacin murmushi yake yi ya mik'e tsam ya zuba hannu a aljihu yana kallon su d'aya bayan d'aya yace, "Ki daina rantsewa Mama kar azumin kaffara yayi miki yawa a kanki, k'anwata ki bar kuka" ya fad'a yana kallon Suhaima kafin ta taka zuwa tsakiyar falon yana kallon kowa.

Mama suman tsaye tayi ta kasa motsi sai kallon Hydar da take yi da ya juye mata ya koma tamkar wani cikakken d'an ta'adda a kamannin sa. Hydar ya kalle su yace, "Eh duk abinda kace nayi na aikata gaskiya Hafiz yake fad'a ba k'arya ba" ya fad'a yana kallon Hafiz d'in yana murmushin rainin hankali.

"Nine master planer, kun jima kuna so ku ganni yau gani a tsaye a gaban ku kunyi murnar ganina?" Ya fad'a yana kallon su tare da wara musu hannayen sa. Ganin duk sun kasa magana sai ya kyalkyale da dariya ya dafa hannun sa sai ya kalli mahaifin sa yace, "Ina so mahaifina yasan AliyuHydar baiso kashe shi ba, inda yaso ganin bayan sa tamkar yadda zan take kiyashi haka zan take duk wanda naso. A wannan tafiyar babu nufin kisa sai dai za'a sha wahala."

Ya kalli Asad da yake kallon sa yace, "Ina sonka Asad kamar yadda nasan zuciyar ka tana zafi a wannan lokacin kana ji inama mafarki kake ba gaskiya ba, yadda kake qaunar Hydar baza kaso hakan ta kasance ba amma ta kasance domin ba mafarki kake yi ba. Kai kana tunanin a banza na goya maka baya ka auri wannan?" Ya fad'a yana nuna Rauda da yatsan sa ba tare da ya kalle ta ba har lokacin Asad yake kallo.

Sai kuma ya sake yin ya cize bakin sa yace, "Nayi ne sabida mafita tawa badan wai kana sonta ba sai dan ta silar soyayyar ta Mama ta tsane ka tayi maka baki ta daina fighting akan baka kujerar mulkin garin nan. Amma sai naga Mama bata saduda ba hukuncin ta akan yarinyar ne a kanka ba shiyasa na canja shiru. Tun dawowar ka nasan waye ya dawo kake raina min hankali wai matsayin kaine Aliyu baka san Aliyun ma a tafin hannuna yake ba balle kai, ka tuna yar da wayar ka da kayi a Cairo? Koda yake a yanzu nasan kasan nine na cire ta daga jikin ka dan nisanta ka da Mama."

"Duka abinda yake faruwa na sani, ka dawo ka koma Aliyu kake fita daga gidan nan matsayin Aliyu wasu suna d'auka da gaske Aliyu ne dan ko sarkin mota ya d'auka Aliyu yake d'auka yake fita dashi har yake kai masa wannan" ya fad'a yana sake nuna Rauda da yatsan sa sai yayi murmushi yana cize bakin sa yana binsu da kallo d'aya bayan d'aya.

"Duka ku kwnatar da hankalin ku ai yanzu aka fara kuna tunanin wai komai yazo k'arshe ne? Hmmm hatta wannan zaman da akayi yau yana daga cikin plan d'in master planer akwai na gaba wanda zai gigita ku gabad'aya ku. In har Hydar bai zauna a kan kujerar katagum ba babu wanda zai zauna ya kwana lafiya, ku rubuta wannan ku ajjiye!. Wannan yana nan tafe kuma zai zo in bai zo ba kuma ba sunana Hydar ba" Yana fad'a ya fita da baya kamar walqiya basu sake ganin koda kalar rigar jikin sa ba.

Luuuuuu Mama tayi ta zube a wajan a sume Suhaima tayi kanta a guje Asad ya taso shima da sauri ya rik'e ta amma ina ta suma ko numfashi bata yi, Fulani Rukayya da take zaune tana hawaye ta girgiza kai tace, "Dole ki suma Rabi'atu, abin suma ne ya same ki. In ma da abinda yafi suma kyayi abubuwan sun wuce tunani." Asad da yake hankali a tashe ya tara yatsun sa a kofofin hancin ta yaji bata numfashi hankalin sa ya kuma tashi sosai yace, "Muje asibiti" ya fad'a yana tallafo Mama.

"Asad ka bar Suhaima da Suhail su kaita asibitin ina buk'atar zaman ka a wajan nan, sannan a bincika inda Jidda take a ji ya yanayin jikin nata" Mai martaba ya bada umarni jin hakan Suhail Asad da Suhaima suka kai Mama mota suka tafi shi kuma ya dawo duk jikin sa a sanyaye da zai samu dama ya keb'e kansa babu abinda zai hana bai fashe da kuka ba.

Dawowa yayi ya zauna mai martaba ya kalle shi ya kalli Aliyu da yake a kwance idanun sa a kulle yayi murmushi yace, "Asad ka zama namiji ka danne zuciyar ka bana son ganin rauni a tare da kai ko kad'an." Mutanen falon ya kalla gabad'aya yace, "Ban amince wani hadimi ya samu wannan labarin ba dalilin da ya saka nace kowa yazo nan kenan, bana so maganar nan ta fita in kuma ta fita na samu labarin wanda ya fitar da ita akwai mummunan mataki a kansa. Yadda kowa yake d'auka Asad ne yake mulki aje a hakan bana so kowa yasan da canje akayi, bana so!" Ya sake fad'a da kakausar murya.

"Sa'adatu dake da Yahuza da Hafiz babu abinda zance muku haka zalika babu abinda zan yi muku, kowa ya aikata alkhairi ya sani haka kowa ya aikata akasin sa ya sani. Aliyu da yake kwance a k'asa yanzu hankalin sa yana barazanar barin jikin sa ya zamar muku abin kallo da darasi domin tare kuke shirya komai ga kuma abinda ya same shi nan, abinda ake kira qaiqayi koma kan masheqiya kenan anyi zalincin da Asad sai kuma ya k'are a kanku. Shi Allah haka yake ikon sa baya cutar da wanda bashi da hakki yana bayan mai gaskiya a koda yaushe yana kuma bashi kariya daga mutane irin ku. Kai kayi abinda kayi sabida kanka ita kuma tayi ne sabida kawai ra'ayin tane, ina so ku jira sakamakon ku wajan Allah domin bazai barku ba, hakkin cutar da wannan bawa da kuka yi sai yayi masa sakayya ko yanzu ko nan gaba. Ta inda Allah ya taimake ku babu ran wanda aka d'auka da wallahil azim babu abinda zai hana ban saka an yanke muku hukuncin kisa ba."

Dukkan su sunyi shiru suna jin abinda yake cewa Fulani Hajiya kuka take sosai nadama tana shiga zuciyar ta a yanyin da Waziri ya d'auko wayar sa jin kiran da ake masa yayi yawa, mai martaba ya kalle shi yace, "Amsa kira, ka kuma sakata a amsakuwa." Ba musu kuwa yayi yadda yace daga cikin wayar akace, "Ranka ya dad'e tun d'azu muke neman wayar waziri bamu samu ba, gida ne babu lafiya Mai sunan Hajiya mai babban d'aki da mai sunan mai martaba aka same su a kwance a falon Waziri dukkan su kumfa na zuba daga bakin su. Labari mara dad'i ranka ya dad'e dukkan su Allah karb'i rayuwar su."

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!" Dukka jama'ar falon suka fad'a shi kuwa katse kiran yayi ya kulle idanun sa a daidai lokacin aka kwalla kiran sallar la'asar. Bud'e idanun sa keda wuya ya fara zubar da hawaye kamar k'aramin yaro yana kuka sosai mai had'e da hawaye jin lokaci d'aya y'ay'an sa guda biyu wanda yafi so a duniya sun mutu.

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, muna rok'on Allah ya jiqan su ya gafarta musu ya sa sun huta ya kuma karb'i baquncin su. Abinda ya kamata ayi yanzu in an idar da sallar la'asar za'a kai su makwancin su. Taron nan dole ya tashi a yanzu" Mai martaba ya fad'a cikin maganar mai d'auke da taushi a cikin ta.

Zabura Waziri yayi ya fita da sauri duka mutanen d'akin kowa ya fita ya bada umarnin a tafi da Aliyu gida Uncle suka fita dashi dan zuwa lokacin ko motsi ma bayayi sai numfashi kawai da yake fitarwa. Falon ya rage daga Asad sai Abba sai kuma su Baba da suke zaune suna jin abu kamar almara kansu duk ya kulle.

Abba yace, "Malam Adam da iyalan ka ina yi muku godiya akan dukkan abubuwan da suka faru, ina fatan kuma dukka ku kun fahimci abinda ya faru an kuma tabbatar babu hannun Asad a dukkan abinda ya faru. Hakika naji dad'in yadda kuka karb'i k'addarar nan hannu biyu na sake tabbatarwa a zuciyata itace matar Asad ta cikin mafarkin sa. Y'ata Rauda ina fatan kin tabbatar da har gobe kina matsayin matar sa ne ko?." Rauda hawaye take yi sosai a lokacin ta kasa magana mai martaba yayi murmushi yace, "Kar ki damu ki daina kuka ita daman rayuwa haka take, wanda ka bawa amanar kanka da rayuwar ka shine yake cutar dakai a wani lokacin. Shiyasa amana tayi karanci ba kowa ne yake tamk'a amanar wani abu nasa hannun mutane ba balle kuma rayuwar sa. Asad yaso Hydar sosai har gobe yana son sa kaf y'an uwan sa yafi son Hydar yanzu ga abinda Hydar yayi masa. Kuyi haƙuri dukkan ku abubuwan da suka faru a baya yanzu komai ya wuce in sha Allah."

"Ta silar ki komai ya bayyana y'ata shiyasa dukkan su baso son dawowar ki domin ke tamtar Inuwa kike a gare shi tun a mafarki ya sanki yake kuma rayuwa dake. Ke alkhairi ce a cikin gidan nan ta silar ki abubuwa da yawa sun bayyana wanda ba'a yi tunanin bayyanar su ba. Allah yayi muku albarka dukkan ku ya albarkaci rayuwar ku yasa kufi k'arfin dukkan maqiyan ku."

Baba ya gyara zama ya amsa da Amin kafin yace,"Allah ya taimake ka babu komai, komai ya wuce sai dai muyi fatan alkhairi nan gaba."
"Ma sha Allah. Yanzu abu na gaba da zamu fuskanta shine dawowar ta cikin gidan sarauta matsayin matar sa, ina so ayi gagarumin biki da dukka jama'a zasu shaida matar sarkin katagum ce. Ba kuma naso a d'auki lokaci nan da kwanaki uku zuwa hud'u nake so ayi komai a gama dan ina so a dawo da martabar katagum da aka rasa. Ina fatan babu takura a cikin lamarin."
Chapter 103 · 0% Book details