Sashe 77
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Na tsane ka! Bana sonka bana son mai sonka ko waye!. Ban tab'a yin dana sanin sanin ka a rayuwata ba sai yau, ban tab'a tsanar kaina ba sai yau, ban tab'a jin duniya tayi min zafi ba sai yau. Me nayi maka kayi min wannan hukuncin..? Me na aikata maka bayan duk tarin abinda kayi min ni ban rama ba sai kaii?. Wallahil azimi na tsane ka bana sonka da za'a bani wuk'a yanzu babu abinda zai hana ban kashe ka ba. Ka saka na aikata sab'on Allah wallahi tunda nake ban tab'a Zina ba sai yau, meyasa zakayi min haka....meyasa ka zab'i ka cutar da rayuwa duk abubuwan da kayi min a baya....? Me nayi maka..?" Ta k'arasa fad'a tana kuka sosai tana ji kamar ta had'd'iye zuciya ta mutu.
"Zina!" Ya maimaita a bayyana yana kallon ta da mamaki ganin yadda take kuka sosai da alama har zuciya maganar take fitowa. Ya matso kusa da ita ya rik'e kafad'ar ta yace, "What are you saying Rauda...? Kin san mayar dake bayan na sake ki a Cairo. Why kike kiran kasancewar mu da zina?."
Ba tare da zato ba yaji ta d'auke shi da zazzafan mari ta ja baya ta nuna shi da yatsa idanun ta sunyi mugun ja baya da idanun ta jajaye tace, "Kar ka sake tab'a ni wallahi na tsane ka, ka matso kusa dani zan iya illata ka zan iya kashe ka Asad bana qaunar ka. Kun cika son kanku da yawa ku masu kud'i da mulki kanku kawai kuka sani bakwa duba lahira balle mu talakawan ku, kana yin abu kamar bakai ba. Allah ya isa tsakanina dakai wallahi bazan tab'a yafe maka ba har Allah ya tashi duniya" ta fad'a tana yin baya zata fad'i shi kam kallonta yake har lokacin saukar yatsun ta yake ji a fuskar sa abu kamar a mafarki.
"Ka sani ko hakkina ne kawai ya rage in na yafe maka zaka shiga aljanna wallahi sai dai a kaita wuta, nayi danasanin sanin ka rayuwata, meyasa ka shigo rayuwata bayan kasan ka shigo ne dan ka tarwatsa ta?. Me nayi maka kayi min wannan hukuncin.....?" Ta fad'a tana dafa bango tana sake fashewa da kuka jiri yana sake d'aukar ta.
Ya kasa koda motsin kirki kallon ta kawai yake rana ta farko da wata ta mare shi bayan marin da Mama tayi masa a kanta, nan take zuciyar sa ta harzuk'a yana jin d'aci a zuciyar sa yana binta da kallon da yake d'auke da ma'anoni kala-kala idanun sa sun juya sunyi jajur sabida b'acin rai.
Kanta a kife a bango tana kuka mai tsuma zuciya kanta yana ciwo ga jirin da yake d'aukar ta tana jan numfashi dak'yar, d'ago kanta tayi ta sunkuya ta d'auki mayafin ta ta yafa bata sake kallon sa ba ta k'arasa wajan k'ofa kamar wasa tana murd'awa ta jita a buɗe ta juyo ta kalle shi tace, "Mazinaci bai dace da zama shugaban Al'umma ba, mai son kai bai dace da zama sarkin al'umma ba, banga nagarta da ake fad'a ba a tare dakai, banga ilmin da ake fad'a ba a tare dakai. Tirrr da masu hali irin naka ku kuma jira sakamakon ku tun a duniya Allah sai ya lalata rayuwar ku" ta share hawayen ta tace, "Bani da kud'in da zanyi Shari'a dakai a duniya amma ina da k'arfin guiwar yi dakai a lahira, sai ka fad'awa wanda ya halicce mu dalilin keta min haddi da kayi, wallahi sai Allah yayi mana hisabi nida kai Asad!. Na tsane ka tsana mai muni!" Tana gama fad'a masa hakan ta fita jiri yana d'aukar ta.
A bud'e taga gate d'in ta fita cikin ikon Allah taga mai adaidaita sahu ta fad'a ciki jikin ta na rawa sabida zazzaɓin da yake jikinta suka tafi tana bin gidan da kallo tana hawaye tana ji a zuciyar ta har a tashi duniya bazata manta da gidan da ta aikata zina ba.
*Tofa wai Asad ne ko kuwa Aliyu ne?.*🤔
[17/12, 10:41 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*064.*
Kamar an dasa shi a wajan haka yake a tsaye k'am har ta fita bai motsa ba yana wajan jinin jikin sa yana tafasa kamar an kwashe shi an zuba a wuta ana dafa shi haka yake jin zafin na karad'e ilahirin jikin sa. Mazinaci! shi za'a kallah a kira da wannan sunan mai muni da rashin dad'in ji. Sai a sannan ya zauna ya hard'e hannayen sa yana kallon wani wajan daban zuciyar sa kamar ana gasa a tukubar tsire.
_Kayi gangancin bari ta raina ka, in ba raini ba ita har ta isa ta kalle ka ta fad'a maka wad'annan maganganun harda marin ka..? Mama ce kawai ta tab'a marin ka shima sau d'aya ne tak kuma a kan son tane sai ita. Wacece ita me take dashi da zatayi maka wannan cin fuskar? Dan kawai kana sonta ko me?._ Zuciyar sa tace take bashi wannan labarin ya furzar da iska ya jingina da kujera yana kallon fitilun da suke saman d'akin.
_Ba'a tab'a ci min fuska kamar yau ba, ban tab'a danasanin aikata abu kamar yau ba, ban tab'a jin haushin kaina kamar yau ba, ban tab'a jin haushin wata halitta kamar yadda nake jin haushin ta yau ba. Mari fa...ta kuma kira ni da mazinaci, zina abinda na tsana a rayuwata dashi zata danganta ni?. Duk matsayin da nake dashi a garin nan dama duniya baki d'aya na sauke shi na nemi yafiyar ta akan abinda ya faru duk da ba laifina bane ta sani amma shine zata yi min wannan rashin hankalin?. Allah ya sani banyi niyar mata komai ba magana kawai naso muyi but lokaci d'aya nayi losing control ya kamata ta fahimce ni tunda tasan ina sonta, Ni Asad wata mace ta mara ta kuma kirani da mazinaci....!_ A zuciyar sa yake wannan maganar yana girgiza kai alamun abun ya tab'a shi sosai ba d'an kad'an ba.
_Ni ba matar ka bace, har abada bazan zama matar ka ba, babu komai a tsakaninmu._ kalaman ta suka fad'o masa a zuciyar sa ya runste ido ya dafe kansa da duka hannayen sa yana mamakin dalilin ta na furta hakan bayan tasan lokacin da ya sake ta a Cairo ya mayar da ita.
Suya ransa yake masa sosai amma yasan shine ya jawo da bai d'auko tama da duk hakan bai faru ba gashi a banza a wofi tayi masa abinda har duniya ta tashi bazai manta ba, kai yake girgizawa kansa na sarawa yace, "Is okay!" Ya furta sai kuma ya kwab'e fuska kamar zaiyi kuka ya daki kujerar da yake kai yana cize baki alamun kalaman nayi masa ciwo sosai.
Bai san adadin lokacin da ya kwashe yana haka ba sai agogo ya kalla yaga dare yayi ya tashi ya shiga d'akin ba jimawa ya fito ya rufe ko ina na fuskar sa ko waye kai baza ka gane fuskar sa ba ya fita daga falon gidan ya hau mota ya bar gidan gabad'aya.
Rauda kuwa kuka take a cikin adaidaita sahun kamar wacce dangin ta kaf suka mutu a lokaci d'aya, mai napep din ma ya d'auka mutuwa akayi mata sai ta bashi tausayi yace, "Kiyi hak'uri baiwar Allah." Bata saurare ba kuka take yi suna tafiya taji yace, "Mun zo unguwar baiwar Allah." Kallon wajan tayi tace, "ga layin.....can" ta fad'a muryar ta na rawa sosai ya k'arasa da ita ta sauka yace, "ki bar kud'in, Allah ya jikan wanda ya mutu" ya fad'a yana jan napep d'in sa ya barta ita kuma ta nufi gida gaban ta yana mugun fad'uwa ko ta kan mai napep d'in ma bata bi ba.
Haka take takawa kamar wacce kwai ya fashewa a jikinta ta shiga cikin gidan ta same su a tsaye sun zubawa k'ofa idanu da alama ita suke jira, ganin hakan sai gabanta ya tsananta bugawa duk suka zubo mata ido harrrr sai taji ta sare ta tsaya cak a tunanin ta in ta k'arasa kusa dasu zasu ji wata alama da zata nuna ta aikata zina a wannan daren.
"Malam! Malam!! Gata ta dawo" Inna ta fad'a cikin d'aga murya sai ga Baba ya sakko daga sama, Umma binta kawai take da kallo kamar mai son gano wani abun a tare da ita sai sake ware idanunta take akan Raudan kafin tace, "Ina kika shiga Rauda? Tun bayan la'asar Ummi tace min kin tawo ina kika tsaya haka har takwas na dare?." Hawaye sharrr ta durk'usa a wajan kawai ta fashe da kuka, dukkan su sai hankalin su ya tashi Rahma tayo wajan ta a guje tana fad'in, "Anty Rauda meya same ki?."
Baba ya kalle ta yace, "Ana tambayar ki inda kika tsaya kina yiwa mutane kuka..? Ina kika je har dare yayi baki dawo ba sai yanzu?." Rauda bakin ta rawa yake yi ta rasa abinda zata ce dan Allah ya sani baza ta iya fad'a musu abinda ta aikata ba koda zata mutu. Kukan ya sake tsamari Umma taja tsaki tace, "ba magana ake miki bane zaki saka mu gaba kina yiwa mutane kuka? Gidan ubanwa kika je har dare yayi haka?."
"Naje...gidan.....Farida y'ar ajin mu ta islamiyya na duba Maman su, da naje sai na samu Mamanta ta rasu a lokacin da muke hira da faridan kuma mun gaisa da Maman, shine na tsaya akayi jana'iza dani sai na tawo. Umma mun gaisa fa da Maman nasu amma tana shiga d'aki sai gawar ta aka fito da ita......." ta sake rushewa da kuka kamar gaske duk sai jikin su yayi sanyi Baba ya tausasa harshe yace, "Amma meye amfanin wayar ki da bazaki kira ki sanar damu ba? Kafin nan yaushe kika fara zuwa gidan su k'awa baki fad'awa Umman ki ba?."