← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 131

Sashe 89

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin hakan ya saka ya saki fuskar ta ya rik'e hannun ta yace, "Na koyi doguwar magana tunda aka shiga wannan situation d'in Rauda." Hannun ta kwace tace, "ka daina rik'e ni, ka fad'a min abinda zaka ce ina so na koma gida."
"Rauda ban sake ki ba."
"Ka sake ni." Ya sauke numfashi ya dafe kansa da dukkan hannayen sa zuwa wani lokaci.

Shiru sukayi dukkan su hannun sa na rik'e da kansa kusan mintina goma haka kafin yace, "A Cairo dana sake ki na mayar dake ko a'a?." Ido ta goge a fusace tace, "ka mayar dani. Amma ka kuma zuwa har gida ka sake ni kai da kanka kaga takardar da ka rubuta meyasa kake son yin wasa da hankalin mu ne dan kaga kai wani abu ne a duniya?."
Kamar zaiyi kuka yace, "Rauda bani bane, ki yarda dani banzo gidan ku ba. Aliyu ne!" Ya fad'a muryar sa raunane yana kallon ta.

Damm gaban ta ya buga jin abinda yace ta kalle shi da sauri sai kuma ta d'auke kai ta tsaya cak kwakwalwar ta tana tuno mata abinda ya faru a ranar da yazo da kamannin sa da maganar sa da komai nasa na Asad ne bana Aliyu ba.

Murmushi tana girgiza kai tace, "Kai ka nuna min zanen hannun ka kace min dashi kad'ai ake banbance ku da Aliyu koshi bai san da wannan zanen ba a ranar da kazo naga wannan zanen a hannun ka. Kana so kayi wasa da hankalina ne kawai amma ta ya akayi Aliyu yasan da abubuwan da suka faru a Cairo?. Ya akayi yasan ka sake ni har yazo ya sake sakina?, ya akayi yasan saki d'aya kayi min yazk ya k'arashe biyun?. Ya akayi ya samu rubutun ka?, Ya akayi maganar Aliyu ta koma maganar ka sak har yadda kake magana shima yayi?, Ya akayi Aliyu yasan ma akwai iddar ka a kaina har yazo ya sake sakina?. Yace min Muwaddaty ya akayi yasan sunan nan? Baka tab'a fad'a a gaban sa ba balle ace ji yayi ya akayi ya san dashi?. Indai har ba kai bane ya akayi yasan da wad'annan abubuwan?" Ta fad'a tana kallon sa yayi shiru shi kuma baya kallon ta.

Gabad'aya ta daure shi da jijiyoyin jikin sa tabbas duk abinda ta fad'a gaskiya ne shi kansa bashi da amsoshin tambayar tata hakan ya saka shi yayi shiru kawai baice komai ba yana sauraron abinda take cewa har ta kai k'arshe. Tayi murmushi tace, "Baza ka tab'a wasa da hankalina ba, a baya duk da abinda ya faru ina ganin mutuncin ka sosai kasancewar kaine shugaba a garin nan ina girmama hakan amma a yanzu ka zubar da wannan mutuncin in za'a ce min ga wuk'a na kashe wanda bana so tabbas kai zan fara kashewa. Ka daina k'ok'arin yawo da hankalina ko kace zakayi min wayo in iyayena sun amince dakai kai kasan ni bazan tab'a amincewa da kai ba, iya zaman da mukayi na fahimce ka daidai iyawata."

Kallon ta yayi akayi sa'a tana kallon sa murya a raunane yace, "Bana k'arya Rauda a kanki bazan fara ba, bazan miki k'arya dan cikar burina ba bayan nasan haramcin da yake cikin abinda nake son aikatawa..." yayi shiru na wani lokacin kafin ya kuma cewa, "A kan gaskiyar ki kike banga laifin ki ba nima a kan tawa nake Muwadda, amma ina so ki sani bazan ce akwai aurena a kanki sabida wata manufa tawa; in kin fahimta dakyau cikin halin Asad babu son kai babu kuma k'arya...." ya sake yin shiru ya dafe kansa kana ya kuma cewa, "A matsayin da nake dashi bazan ce bazan yi k'arya ba amma tunda har na rantse yana dakyau ki amince. Tun bayan rabuwar mu ban sake ganin kia zahiri ba sai da rabon abinda yake cikin ki yazo bance lallai sai kin amince ba ki zauna akan ra'ayin ki shima daidai ne."

Ya mik'e tsaye yana kallon wani wajan daban kana yace, "Amma ki sani bazan amince da sauraren wani namiji daban ba, bazan amince da maganar auren ki da wani ba, in kuma hakan ta cigaba da faruwa bake zan yiwa hukunci ba shi zan yiwa sai ya gwammace bai sanki ba.Maganar abortion da kike yi kiyi duk abinda zuciyar ki ta baki umarni daidai ne."

Mik'ewa tayi zata gifta shi ta wuce ya jawota jikin sa sosai yana kallon fuskar ta itama haka,babu wanda yayi magana a cikin su kallon ta yake tana kallon sa har minti d'aya suna a haka kafin ya motsa bakin sa zaiyi magana ta riga shi tace, "Ya akayi Aliyu yasan da irin wannan rik'on da kai kad'ai kake min irin sa? Ko camera ya saka can Cairo d'in yadda zai dinga ganin duk abinda yake faruwa?. Ina jin dai camera ya saka shiyasa yasan da kayi min alqawarin baza ka rabu dani ba."

Runtse ido yayi tashin hankalin sa ya ninka na baya ya matse ta sosai har sai dai kashin k'ugun ta ya amsa sabida matsar da yayi mata bata wsa bace har lokacin kuma bai bud'e ido ba fuskar sa a yamutse tana tattaro ja tana had'ewa waje d'aya.

Rauda zafin rok'on take ji sosai ta kulle idon ta ta buɗe suka had'a ido yace, "Aliyu har rik'e ki yayi? Meyasa kika amimce hakan ta kasance? Ina hankalin da na sanki dashi ina yaje har kika bari hakan ta faru?, Aliyu fa ya rik'e ki like yadda muke yanzu....Hasbunallahu wani'imal wakil!" ya furta yana sakin ta sai ya koma da baya ya zauna a kan kujera ya dafe kansa da duka hannayen sa yana jin d'aci na mamaye masa kan harshen sa sabida tsananin kishi.

        Wani irin abu taji a jikin ta ganin yadda ya koma lokaci d'aya ta bishi da kallo yana zaune a inda ya zauna har lokacin hannun sa yana dafe da kansa sai taji zuciyar ta na bugawa da sauri-sauri ba tare da tasan dalilin hakan ba.

D'ago kai yayi yana kallon ta suka had'a ido sai ya cize bakin sa ya had'd'iye abu mai d'aci ya sake kulle ido ya bud'e cikin rauniyace, "Za'a kai ki gida, kije" yana fad'a ya tashi ya ya shiga ciki ta bishi da kallo har ya b'ace bai sake kallon inda take ba. Duk sai taji jikin ta kuma yayi sanyi sosai ta fita itama bata kuma kallon sa ba tana fitowa taga an bud'e mata mota ta shiga driver yaja basu tsaya a ko ina ba sai a k'ofar gidan su.

Lokacin da ta shiga bata tarar da kowa a falo ba ta shiga falon Umma nan ta ga Umman a zaune ita da Khairi ta k'araso da sallama tana kallon Umma, a hankali ta taka inda Umma take kafin ta k'arasa ta fara kuka ga kanta da yake ciwo sosai, tsugunawa gaban Umma take niyar yi Umma tace, "Ummulkhairi rik'e ta ku shiga ciki kar ta fad'i." Ba musu ta tashi ta rik'e ta suka shiga ciki ta zaunar da ita a kan gado ganin yadda take rik'e kanta sosai sai Khairi ta d'auko mata maganin ta da ruwa tace, "Kisha Anty ko zai daina miki ciwo."

Kai kawai ta d'aga mata Khairi ta fita Rauda ta ture maganin ta kwanta tana sauke numfashi koya ta kulle ido shi take ganowa da kalaman sa da suke mata yawo a cikin kanta har lokacin ta kasa mantawa. Umma ce ta shigo d'akin ta kalle ta bata ce komai ba ta fita jim kad'an sai gata ta dawo da ruwan tea mai kauri ta dawo kuaa da ita tace, "Tashi kisha shayi."

Jin maganar Umma a tausashe a kanta kamar a mafarki sai ta zabura ta mik'e tsaye Umma ta ajjiye tea d'in ta zaunar da ita tace, "Meye na wannan zaburar kamar kinga dodo? Koma ki zauna? Ta fad'a tana zama kusa da ita. Kuka take k'ok'arin yi Umma tace, "Kar kiyi min kuka, ki mayar da wannan hawayen bana son ganin su."

Ba shiri ta mayar dasu tana kallon Umma ta mik'o mata tea d'in tace, "karb'i ki shanye yanzun nan kisha maganin ki." Ba musu ta karb'a ta kafa kai duk dan ta burge Umma tana yi tana kallon ta. Bata sauke ba sai da ta gama shanyewa tass ta ajjiye kofin Umma ta bata magani da kanta tasha amma bata ce mata komai ba. Kallon Umma Rauda take yi ta sunkuyar da kanta k'asa murya na rawa tace, "Umma wallahil azim duk abinda ya faru babu laifina dan Allah ki yafe min."

Umma ta sauke numfashi tace, "ki daina kuka ki kwantar da hankalin ki komai ya wuce yayi mana bayani kuma dukkan mu mun gamsu." Rauda ta kalli Umma tace, "Umma kema kin amince dashi kenan?."
Umma tace, "Na amince har zuciyata Rauda, yanayin yadda yayi mana bayani ya tabbatar mana da kalaman sa gaskiya ne d'an uwan sa shine ya sake ki tun farko kin san shine wanda kuke fad'an nan bazai zo yaga kin rab'i dan uwan saba shiyasa ya yanke wannan hukuncin. Amma shi mai martaba Asad bashi ya aikata wannan sakin ba."

Rauda tace, "Umma rubutun sane, kalaman sane, maganar sace, yanayin sane, hatta shaidar da ya nuna min yace da ita ake banbance su na ganta a hannun sa a ranar kuma ya sanar dani ba kowa yasan da wannan alamar ba ta yaya zai zama Aliyu ne bashi ba?." Umma ta sauke numfashi tayi shiru Rauda na k'ok'arin saka mata kokwanto a zuciyar ta amma har ga Allah ta amince da Asad dan yayi musu bayanin da dukkan su sai da suka firgita da lamarin masarauta.

Umma tace, "Duk na amince da hakan Rauda amma bazai yi rantsuwa a kan karya ba."
"Umma zai iya yi kodan ya samu abinda yake so. Yana k'ok'arin kare kansa ne daga fyad'en da yayi min amma babu aure tsakanina dashi Umma. Tabbas a Cairo ya mayar dani amma ya kuma sakina Ummaaaaa!" Ta fad'a tana can kalmar Umman cikin sanyi tana karyar da wuyan ta hawayen suka sakko mata.
Chapter 89 · 0% Book details