Sashe 8
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mai martaba yace, "ya naga baka murna ko baka sonta ne?, Hydar naga ya had'e fuska" ya fad'a yana kallon Hydar cikin zolayar Asad d'in. Murmushi Hydar yayi yace, "Takawa ai a zuciya yake farin cikin ni na sani." Murmushi yayi yana kallon Asad da har lokacin kansa yake a k'asa bai d'ago ba. Mik'ewa mai martaba yayi suka mik'e suma yana kallon Asad yace, "Tunda baza ka nuna min kana farin ciki da abinda nayi maka ba ai shikenan ni zan tafi." Sai a lokacin yayi murmushi shi kansa ya kasa gane halin da yake ciki a wannan lokacin shiyasa ya kasa dariya ya kuma kasa kuka.
Tare suka fito suka raka mai martaba ya shiga mota sannan suka dawo masaukin su. D'akin da Asad ya sauka ya shiga ya tarar da Aliyu yana niyar fitowa ya bishi da kallo shima kuma shi yake kallo alamun rashin gaskiya a tare dashi, ganin kallon da Asad d'in yake masa sai ya waske yace, "Oga deaf nazo duba ring d'ina ko a nan na bari ashe baya nan" ya fad'a yana ficewa ya bishi da kallo haka kawai yaji zuciyar sa bata amince dashi ba gabad'aya.
Zama yayi a kan kujera ya jingina da kujerar yana kallon sama kamar mai son hango wani abun a saman, jin sa yake wani iri in ya tuna abinda mai martaba yace masa sai yaji wani iri tsigar jikin sa har tashi take, abinda ya tsaya masa a zuciya bai wuce Rauda na son sa ko bata son sa ba dan shi dai yasan baiga alamun tana son sa a tare dashi ba, cize bakin sa yayi a bayyane yace, "that's mean ta amince?" Shiru yayi yana tuna abubuwan da suka faru sai kuma yace, "No bana tunanin ta amince, but ta yaya akayi auren?" Ya fad'a yana dafe kansa da yaji yana sara masa.
'In bata sona fa aka aura mata ni? Ya zanyi da ita ya zanyi da Mama?, na riga na yiwa Mama alqawari zan barta yanzu kuma gashi na canja anya zata yafe min?.' Abinda yake fad'a a zuciyar sa kenan yana jin komai yana fita daga kansa ga k'irjin sa yayi masa nauyi sosai kafin ya shafa kansa yana jin sa kamar ba shi ba. Motsi yaji a bayan sa hakan ya saka ya kalli wajan yaga Hydar ne ya shigo yana amsa waya kafin ya kashe wayar ya zauna kusa dashi yana kallon sa yace, "Oga deaf as groom" ya fad'a da murmushi yana kallon sa.
Asad da ya zuba masa idanu bai ce komai ba Hydar yayi dariya yace, "ka daina kallona idannun ka na rikita ni." Asad yace, "kai ka shirya komai?."
"Yeah na san komai na kuma shirya komai Deaf. A karo na babu adadi bazan bari ka rasa abinda kake so ba musamman wannan da ta kasance abokiyar rayuwar ka."
Ya sauke numfashi yace, "But ita bata sona."
"Mahaifin ta da kansa yace ta amince kaga kenan tana sonka."
"Bana tunanin da gaske ne."
"Mahaifin ta ai bazai mata k'arya ba, ka ajjiye abinda kake jin tsoro babu abinda zai faru sai alkhairi."
Ya sauke numfashi ya kulle idanun sa kana ya bud'e yace, "Rayuwar ta tana cikin hatsari a lamarin auren nan, u forgot abinda ya faru right?."
"Ban manta ba Asad amma a wannan karon babu abinda zai faru, lokaci kad'an ma da zaku wuce Cairo Mama bata san anyi ba." Kai yake girgizawa cikin sanyin jiki alamun bazai iya aikata hakan babu sanin Maman sa ba, nan take yaji auren ya sake fita a ransa komai baya yi masa dad'i dan sai Mama nasan abu shima yake ji yana so.
"Kar ka damu dan Mama bata sani bafa tunda Abba ya sani kuma shine ya yanke hukunci ai komai ya k'are." Asad ya sauke numfashi ya d'aga kai sama kamar mai son gano wani abun a saman.
Hydar ya kalle shi yace, "Ka kira ta for the first tym as your lovely wife." Kai ya sake girgizawa alamun a'a Hydar yayi murmushi kawai ya daki kafad'ar sa yace, "kurma nawa, ina ji da kai sosai, zan iya yin komai dan samuwar farin cikin ka, zan iya barin komai da farin cikin ka" yana fad'ar hakan ya tashi ya bashi waje yana dariya zuciyar sa fess karon farko Asad ya mallaki abinda yake so ba tare da takurar Mama ba.
Bayan kwana biyu.
Ranar da akayi addu'ar ukun mai martaba sarkin Kano su Asad suka d'auki hanyar Bauchi suka bar Mama ita kad'ai a gida sai anyi addu'ar bakwai zata dawo ita, bata san me ya faru ba har lokacin tana cikin alhinin rashin mahaifinta ba ta kan komai take bi hakan ya saka bata cika d'aukar waya bama balle a samu wanda zai sanar da ita bak'in labari a wajan ta.
Bayan sun huta da daddare Asad na zaune a d'akin sa yanaa karatu Hydar ya kira shi a waya, bai d'auka ba sai da ya kira sau uku sannan ya d'auka baiyi magana ba ya kashe ya fito zuwa falo. A tsaye ya tarar da Hydar d'in ya kalle shi alamun lafiya yake neman sa?.
Hydar yace, "Takawa ya bada umarnin kaje gidan su matar ka yanzun nan shiyasa na sanar da kai" yana fad'ar hakan ya wuce ya barshi tsaye yana tunanin abinda ya kamata yayi. Yasan shirin Hydar ne sarai amma tunda ya ambaci mahaifin sa dole yaje babu yadda zaiyi.
Shi bawai baya sonta bane yana sonta har lokacin kawai wasu abubuwa ne suke caja masa kai har yaji komai yana fice masa a rai shiyasa baya wani zumud'in hakan kwata-kwata. D'akin sa ya koma ya d'auki makullin mota a kan madubin d'akin har ya gota sa ya dawo yana kallon kansa a madubin, kayan jikin sa yake kalla riga da wando ne dogaye marasa nauyi a jikin sa sai yaji a zuciyar sa bai kamata yaje da kayan jikin sa ba.
Ajjiye key d'in yayi ya shiga band'aki ba jimawa ya fito ya shirya cikin yadi fari mara nauyi mai shara-shara ya saka hula bak'a kalar aikin jikin yadin ya fashe jikin sa da turare masu sanyi ya tsaya yana kallon kansa a madubin bayan ya gama shiryawa.
Shi kansa yasan yayi kyau sosai ya murmusa sai kuma ya cize baki ya d'auki key d'in motar ya fita a sanyaye. Da Aliyu suka had'u a falon har ya gifta Aliyu sai kuma ya dawo da baya ganin irin kallon da Aliyun yake masa ya wara idanun alamun kallon na meye?. Aliyu yayi dariyar shak'iyanci ya cize bakin sa kamar yadda Asad d'in yake yi yace, "na tsaya ina kallon angon talakan yarinya, wow u look very beautiful deaf" ya fad'a yana tasowa yazo kusa dashi yana kallon sa.
Asad baice komai ba ya fita shi kuma yayi dariya yana cize baki cike da mugunta sai da ya tabbatar Asad ya hau mota ya fita sannan ya shiga d'akin Asad d'in da yake a bud'e.
K'arewa d'akin kallo yake yana girgiza kansa ganin sa tsaf dashi khamshin turaren Asad d'in ya cika d'akin wanda indai kasan Asad ka sanshi da wannan turare, a jikin bango ya jingina yana bin d'akin da kallo kamar me neman wani abun kafin ya girgiza kansa ya fita.
Asad kuwa a sanyaye yake driving d'in motar gabad'aya jikin sa ya saki kansa take ji yana rasa masa sosai ga tunanin ta yadda zai tunkari gidan su Rauda as sirikin gidan duk sai yaji wani iri a jikin sa wallahi, Dak'yar ya iya kawo kansa k'ofar gidan ya faka motar yana kallon gidan amma ya rasa abinda zaiyi shiyasa ya zauna a motar kawai yana kallon gidan.
Kamar wasa ya ganta tana nufar gidan ita da wani saurayi suna ta murmushi ita dashi har tayi tuntub'e zata fad'i yayi saurin rik'o ta ya gyara mata zaman sandinan nata suka cigaba da takawa har suka shiga cikin gidan da alama wani nata ne ta san shi sosai.
Wani irin zafi Asad yaji yana taso masa daga zuciyar sa yana mamaye dukkan jikin sa har cikin idanun sa, cize bakin sa yake yana bin su da kallo har suka shiga gidan ya runtse ido ya kai hannun sa ya rik'e wuyan sa da duka hannayen sa biyun nan take yaji har fatar wuyan tayi zafi sabida zafin zuciyar sa har ya huda ya fito ya mamaye fatar sa. Ya sani yana da kishi Allah ya yishi cikin maza masu zafin kishi ko kad'an baya so yaga an rabi abinda yake so koda kuwa takalmi ne balle kuma matar sa.
Idanun sa har sun fara canja launi daga fari zuwa ja ciwon kansa ya k'aru fiye da wanda yazo dashi dana sanin zuwa wajan ya mamaye masa zuciyar sa da ruhin sa ji yake ina ma baizo ba da baiga abinda zai d'aga masa hankali haka ba. Knocking d'in glass d'in ake yi amma bai iya kalla ba sai akayi kusan sacan ashirin sannan ya kalli gefen tagar ganin mahaifin ta ya saka shi daurewa ya bud'e motar ya fito waje.
Baba ganin sa sai ya washe bakin sa yana jin farin ciki a zuciyar sa ganin kamar Asad ya kasance siriki a wajan sa me zaiyi in ba farin ciki ba?. Kafin Asad ya gaishe shi Baba ya riga shi furta, "Barka da Dare Asad." Sai Asad yaji wani iri ya dawo da nutsuwar sa jikin sa ya duk'a ya gaishe shi ya amsa baki a wangale kana yace, "ya karin hak'uri kuma?." Asad ya amsa da fad'in, "Alhamdulillah."
"Allah ya jikan sa ya gafarta masa ya duba abinda ya bari."
"Amin" Asad ya amsa a tak'aice domin baya jin dad'in yanayin sa gabad'aya.
Baba yace, "ka k'araso ciki mana Asad kamar wani bak'o ka tsaya a waje." Babu yadda ya iya dole yabi bayan sa zuwa ciki , a k'aramin falon dake wajen cikin gidan ya zauna yana kallon sa yace, "Bara na turo maka ita ku gaisa" Baba ya fad'a da nishad'i yana kallon sa. Murmushi yayi kawai baice komai ba Baba ya fita shi kuma ya d'auko waya yana dannawa ko zai rage masa abinda yake ji a zuciyar sa.