Sashe 40
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya girgiza kai yace, "A'a Asad bazai tawo da budurwa wata k'asa ba nasan halin sa."
"To kaga kenan indai har ba k'anwar ba bace ba to matar sace, yanayin yadda take magana kamar sun samu matsala ita dashi ne." Ya girgiza kai cikin gamsuwa yace, "na dai fi tunanin k'anwar tasa ce, abinda ya d'aure min kai ina yaje ya barta?. In ya kasancewa matar sace babu ta yadda za'ayi ya tafi ya barta ita kad'ai domin kishin sa bazai barshi ya iya barin ta ba. Shine fa wanda nake fad'a miki in ya nuna takalmi yace yana so tofa duk yadda kuke dashi kar ka saka wannan takalmin yadda yace yana so nasa ne shi kad'ai, in kuma ta faru ya bar maka shi baya so kiyi tunani ace matar sace ya abin zai kasnace?."
Ta girgiza kai tace, "akwai dai wani abun a biye Dear amma ni ban yadda k'anwar sa bace ba kallon matar sa nake mata, matsala suka samu har hakan ta kasance amma bazai bar k'anwar sa inda ka ganta ba. Tunda ya kasance mai kishi dole yayi kishin k'anwar sa. Kuma k'anwar sace zai tawo da ita k'asar nan su biyu kawai har ayi mata aikin k'afa ba tare da mace ba? Ka tuna suna da kud'in da za'a tawo da masu jinyar ta bama guda d'aya ba amma aka had'o su su biyu kawai, in ba matar sa ba babu wacce zai zauna da ita daga shi sai ita."
Khalifa girgiza kai yace, "to Allah ne dai masani, zan jira naga zai kira ni daga yau zuwa gobe in bai kira ba kawai sai na mayar da ita Nigeria d'in mayi magana dashi daga baya." Daga haka suka cigaba da hira kafin Khalifa ya fita.
[17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*045.*
B'angaren Asad yayi baccin sosai mai cike da sabbin mafarkai kafin ya farka dan sai da aka amsa allurar bacci sannan baccin ya d'auke shi. A gadon asibiti ya ganshi ya kalli hannun sa yaga ruwa yana shiga ya dafe kansa yana sauke numfashi a sannan Mama da Suhima suka shigo.
Mama ta kalle shi tace, "Sannu Asad, kaji dad'in jikin ka?." Kai ya d'aga alamun eh sai ga likita ya shigo ya k'araso inda yake ya zare masa ruwan jikin sa ya sake auna bp sa ya kalli Mama cikin turanci yace, "bp nasa ya sauka saura kad'an, daman ya firgita ne dalilin da ya saka jinin ya hau kenan but yanzu in ya samu nutsuwa zai dawo daidai."
Mama ta girgiza kai kawai bata ce komai ba tana binsa da kallo jin wai harda hawan jini akan kucakar yarinyar da bata wuce mai goge masa takalmi ba. A sannan suka koma cikin d'akin su ya shiga d'aki yayi alwala yayi sallah dan sosai yaji dad'in kansa ya rage ciwo sosai.
Bayan ya idar da sallah Suhaima ta shigo ta zauna kusa dashi tace, "Kayi haƙuri Yaya Asad na bata passport d'in ta da wayarta da kuma kayanta in sha Allah zata koma Nigeria. Sai dai kuma babu kud'in ticket" Suhaima ta daki kanta tace, "na manta ban bata ba Yaya, yanzu da wanne kud'i zatayi amfani ta siya?." Asad sai murmusa ya cize bakin sa ya lumshe ido ba tare da yace komai ba. Suhaima tace, "kazo falo inji Mama" tana fad'a ta Mike ta fita jikin ta a sanyaye.
Bai jima ba ya fito tunda ya fito daga d'akin take kallon sa har ya k'araso ya zauna a kusa da k'afafun ta bata daina kallon sa ba tace, "Asad kaga yadda ka rame lokaci guda kuwa?." Shiru yayi baice komai ba kafin ta share zancen itama tace, "gobe zamu koma Nigeria akwai abinda kake so ka siya ne? In akwai ka siya yanzu dan jirgin safe zamu bi." Dak'yar ya fizgo maganar yace, "Babu."
"To yayi kyau, in muka tafi da safe nasan zuwa azahar zamu je bauchi mu shiga katagum zuwa jibi dai nake so sarautar ka ta dawo hannun ka a had'a shagalin da bikin auren ka da Jidda a huta." Baice komai ba ko d'agowa ma baiyi ba balle yayi magana. Kamar ya tuna wani abu sai ya kalli mahaifiyar tasa yace, "Ya jikin takawa?." Mama tace, "Bamu samu Hydar a waya ba har yanzu." Ya kalli Suhaima yace, "Wayana."
Tashi tayi ta shiga d'akin ta kawo masa ya karb'a yana dannawa yaga message d'in Dr Khalifa a notification hannun sa na rawa ya danna ya bud'e yaga abinda yace kamar haka, _Prince ina kaje ne ina ta kiran baka picking call d'in?, sister ka tana gidana nazo hotel wajan ka na tarar da ita security suna neman arresting d'in ta. Ka kira ni in kaga message d'ina bata da lafiya ma._
_Tana gidana._ abinda ya sake dawo masa kansa kenan ya runtse idanun sa yayi saurin fita daga message d'in ya shiga wajan kira yana nemo Hydar zuciyar sa na zillo ya danna kiran wayar Hydar. Bai d'auka ba ya sake kira nan ma bai d'auka ba sai ya k'yale shi Mama tace, "Bai d'auka ba ko?." Kai ya d'aga alamun eh tace, "muma baya d'auka in mun kira, Allah yasa ba jikin nasa bane babu dad'i."
"Wanne County suka tafi?" Ya tambaya muryar sa na shaking.
"Germany" Suhaima ta bashi amsa da tausayi.
"Zan iya siyan ticket naje Mama?." Ta kalle shi ya sunkuyar da kai tace, "A'a daga nan babu inda zaka je sai Nigeria, ka daina wani tunani in ba wannan ba." Ya girgiza kai kana yace, "Allah ya wuci zuciyar ki." Shiru ya ratsa tsakanin su kafin yace, "in an min izini ina so na sha iska." Mama ta kalle shi kamar baza tayi magana ba sai kuma tace, "jeka, amma in kayi abinda na haramta maka kasan sauran."
"Godiya nake" ya furta a hankali ya tashi ya fita daga falon ya sauka zuwa reception ya fita ya tsaya a kan titi kawai yana kallon mototoci hannun sa hard'e a k'irjin sa. Wayar sa tayi k'ara ya d'auko yaga sunan Hydar ya d'auka ya saka a kunne daga can b'angaren yace, "Sorry Deaf ka kira ni muna tare da Takawa ana bashi magani."
"Meyasa ba'a sanar dani bashi da lafiya ba?."
"Shi ya hana a fad'a maka shiyasa ban fad'a ba. Ya kake naji maganar ka wani iri kamar baka da lafiya."
Asad baice komai ba ya juya ya shiga hotel d'in ya zauna a reception kana datse kiran ya kira shi video call dan yana so yaga mahaifin sa, d'auka Hydar yayi fuskar sa ta bayyana a screen d'in wayar shima haka tasa fuskar tajewa Hydar daga can b'angaren Hydar yace, "Subahanallah! Deaf meya same haka? Naga ka rame sosai." Asad yace, "nuna min Abbana."
Ba musu ya juya Camarar ta baya ya haska mai martaba da yake kwance cikin wata na'ura kamar mai bacci, har kusa dashi Hydar yaje yana sake haska masa shi yana cewa, "tunda muka zo yake a haka sunce nan da kwana uku zai farfad'o in sha Allah kuma za'ayi nasara."
"Anya kunje asibiti mai kyau?" Ya furta a hankali cikin tashin hankalin ganin yanayin da mahaifin nasa yake ciki. Hydar yace, "kasan dai duk abinda zanyi dan ganin ya samu lafiya zanyi Deaf, likita har daga India munyo booking gobe zaizo, mun gayyato na nan Egypt ma shima zai zo a had'u su a duba ko za'a gano matsalar dan nan har yanzu basu gano komai ba.
Asad yayi shiru baice komai ba Hydar ya kuma cewa, "ka sanar dani dalilin wannan ramar taka Asad, ina ita Raudan take?."
Shiru Asad ya kuma yi ya sauke ajiyar zuciya kana yace, "Komai ya k'are Hydar." Hydar ya kalle shi bayan ya dawo da camera front yace, "ya k'are akan me? Kar kace min Mama tayi nasarar raba ku?" Ya fad'a yana kallon sa da alamun tashin hankali. Asad yayi shiru baice komai ba yana kallon Hydar kafin ya janye idanun sa yace, "ka kula da Abba dan Allah, zanzo nan kusa in sha Allah" yana fad'a ya datse kiran ba tare da ya bashi amsa ba.
Shiru yayi na wani lokaci yana kallon wani wajan daban kafin yaja siririn tsaki ya tashi ya koma ciki.
Kamar yadda Mama ta tsara da safe suka dira a airport k'arfe bakwai da rabi na agogon Cairo jirgin su ya lula sama suka nufo Nigeria. K'arfe d'aya saura suka sauka tun kafin su taso an sanar da driver da zai d'auko su a airport d'in suka same su suna ganin fitowar su a guje suka k'araso aka karb'i kayan hannun su aka take musu baya, mota personal Asad ya shiga shi kad'ai Mama da Suhaima suka shiga aka d'auki hanyar katagum.
Gudu suke sosai nan da nan suka shiga katagum aka isa gidan sarki aka bud'e gate motar su ta shiga cikin gidan, da sauri aka fito aka bud'ewa Mama k'ofa shi kam Asad kafin a bud'e masa ma ya bud'e ya fito yana kallon gidan sai yake ji ya zamar masa bak'o kamar ba'a nan aka haife shi ba. Ciki suka nufa Asad yayi hanyar da zata kai shi apartment d'in su ta kalle shi ta cigaba da tafiya, yasan ma'anar kallon ko bata ce ba yabi bayan ta a gajiye.
Tana shiga apartment d'in ta aka fara kawo gaisuwa amma babu wanda take kulawa har taje k'aramin falon ta wanda ba kowa yake zuwa ba ta zauna a kan kujera ya zauna a k'asa Suhaima ta wuce d'akin ta, kallon sa tayi tace, "Ban amince da d'akin ka na da ba dan haka zaka zauna a nan kafin a kammala komai ka koma b'angaren ka, aiki yayi nisa ko nace an gama ma." Shiru yayi baiyi magana ba tace, "ko baka ji bane?."
"Naji. Ina neman izini zanje can d'in na d'auko abinda zanyi amfani dashi."
"Ban amince ba ka fara hutawa kaje anjima, tashi ka shiga d'akin da Hydar ya kwanta." Bai musa ba ya tashi ya shiga tare da kullo k'ofa.