Sashe 118
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Asad yace, "Abba dan Allah ka yafewa Mama, wallahil azim tayi nadamar dukkan abinda ta aikata yanzu har Rauda ta saka aka kira ta bata haƙuri. Dan Allah ka yafe mata Abba." Abba yayi murmushi yace, "Dole tayi nadama ai koda bata so na dan in ma batayi ta tsakani da Allah na duniya ta koya mata hankali, taga ishara akan Sa'adatu da Yahuza da kuma Aliyu, ta tabbatar itama ta cigaba da tafiya a haka irin wannan k'arshen zatayi. Kaf ma'aikatan gidan nan basa son ta sabida halin ta na wulaƙanta na k'asa da ita a ganin ta Allah ya fifita ta akan su, y'ay'an ta har biyu dukkan su y'an ta'adda masu bak'ar zuciya da bak'ar aniya da mugun nufi ai dole tayi nadama. Duk taqamar ta akan y'ay'an da take yi sai gashi dukan su samun su ba alkhairi bane in aka cire ka, Rauda kuma da take magana badan ita ba da yanzu har yanzu ina kwance har yanzu ana cigaba da yi min allurar karya garkuwar jiki, silar kawun ta komai yazo k'arshe ba dole ta bata haƙuri?."
"Ka manta har kisa ta aika aje ayi a gidan su? Duk tunanin ta wannan ranar bazata zo ba sai gashi tazo tana kuka da idanunta. Ta gode Allah ma tana da bakin rok'on bata mutu tun farko abin ba da sai a lahira Allah ya tsayar dasu yayi musu hisabi. Taje ta raba ku da yarinyar nan duk a tunanin ta taci riba bata san Allah ya riga ya kulla alaqar ku ba."
Asad yayi shiru baice komai ba har sai da mai martaba ya gana fadn sa sannan yace, "Yafiya nake nema mata Abba, nasan duka ta aikata amma sabida Allah sabida ni Mai martaba ya yafewa Mamana iya abinda take ji a zuciyar ta ma ya ishe ta." Mai martaba ya sauke ajiuar zuciya yace, "ni na yafe mata ai; na yafewa Sa'adatu ma balle ita? Na yafewa Yahuza ma balle ita? Na yafewa dukka ire-iren su balle ita?. Taci darajar ka na yafe mata."
Asad yace, "Na gode mai martaba, Allah ya k'ara lafiya da nisan kwana." Ya amsa da amin kafin ya kalle shi yace, "Akwai gajiya a tare dakai yana dakyau kaje ka huta." Asad yace, "zan duba jikin Aliyu ne."
"Ana samun cigaba sosai a rashin lafiyar tasa, basai ka shiga ba tafi kaje ka huta. Shi kuma Hydar da yak'i saduda Allah zai mana maganin sa." Asad baice komai ba ya fito aka rufa maaa baya aka raka shi b'angaren sa kafin kowa ya watse.
Zai hau saman Rauda zata sakko idanun ta yayi ja alamun kuka tayi ta dawo da baya ta bashi hanya ya wuce bata ce komai ba ta sauka ta fita ya bita da kallo kafin ya wuce ciki shima.
Da daddare ta kawo masa abincin dinner har sama ta same shi zaune da k'ananun kaya masu laushi kalar milk yana aiki da laptop yayi shiru baka jin sautin komai sai na keyboard. Ajjiye masa abincin tayi ba tare da zatayi magana ba ta juya ya kashe laptop din yace, "Tsaya." Ba musu ta tsaya ta juyo tana kallon sa ya mik'e tsaye yazo kusa da ita yace, "Me kike ji dashi ne? Me kike d'aukar kanki?."
Rauda ta kalle shi itama fuskar ta kamar tasa fuskar a d'aure tace, "Abinda kake ji dashi nima shi nake ji dashi. In taqamar kai sarki ne ni matar sarki ce, in taqamar ka kai dan sarki ne nima sirikar sarki ce, in taqamar ka kai jikan sarki ne nima sirikar jikan sarki ce. Duk abinda kake ji dashi nima shi nake ji dashi" ta fad'a tana kallon sa shima ita yake kallo.
Kai yake girgizawa yana kallon ta kafin yace, "ba kece sarkin ba ashe matar sace?."
"Eh daidai nake da sarkin tunda nice matar sarkin!. Dan an kawo maka ni gidan nan sai ka dinga wulaƙanta ni kana yi min abinda kaga dama dan kaga kawai ina sharewa? In haushina kake ji nima ka sani haushi ka nake ji wallahi domin ta silar ka abubuwa da ya suka faru dani a rayuwata wanda bazan manta dasu ba har abada."
"Ta silar ka Ummana tayi min Allah ya isa" sai muryar ta ta soma rawa ta fara kuka tana fad'in, "Dukkan k'addara ta a kan kane duk abinda ya faru dani ta silar kane kaine ka jawo komai da baka shiga rayuwata ba da hakan bata faru ba. Ni banji haushin ka ba sai kai zaka dinga jin haushina kana share ni dan kawai kana taqama da wani abun kana ganin kamar power da kake dashi ne ya saka ni dawowa ko auren ka. To ba haka bane baza kayi min abu kuma ka fara fushi ba sannan ni na sauka k'asa ba bazai yu ba, a baya an dake ni an hana ni kuma amma a yanzu bazan lamunta ba wallahi, ina k'okarin sauke hakkin ka da yake kaina matsayin ka na mijina Allah yana gani in ka kula kanka in ma baka kula ba kanka" tana fad'a ta juya ta sauka ta barshi a wajan a tsaye yana kallon hanyar da tabi zuciyar sa na rawa sosai.
*Duk mulkin namiji bawan mace ne.*🫡
[17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*089*
Da kallo ya bita har ta sauka ya furzar da iska ya juya ya hard'e hannayen sa a k'irji ya runtse idanun sa. _Sudai mata duka halin su d'aya basa damuwa da damuwar ka kansu suka sani kawai_. Ya fad'a a zuciyar sa yana sauke numfashi ya zauna akan kujera yana jin zuciyar sa na bugawa.
Baya so kalaman ta suyi tasiri a ransa dan zasu b'ata masa rai ne hakan ya saka bai ma kalli abincin ba ya tashi ya barshi a wajan ya shiga d'aki a zuciyar sa yana aiyana dole ma gobe ya bar garin tunda Mama ta samu lafiya dole ya basu waje ya huta tunda ba son ganin sa zai basu waje tunda babu tausayi a zuciyar ta bata ganin yanayin da yake ciki take sake k'ara masa damuwa.
B'angaren Rauda a fusace ta shiga b'angaren ta ranta duk a b'ace haka take jinta sai girgiza kai take yi ita kad'ai komai ya tsaya mata. "Bashi kad'ai yake ji da kansa ba nima ina ji da kaina, ni mutum ce kamar shi wallahi bazan d'auki wulaƙancin dana d'auka a baya ba" ta fad'a a bayyane tana dafe kanta tana zaune a gefen gado.
Sai kuma ta rasa me yake mata dad'i sai kawai ta mik'e ta nufi b'angaren Mama dan ta sake duba jikinta. A zaune ta same ta a falo sanye da hijjabi da carbi a hannunta tana ja ita da Suhaima tana b'are mata ayaba tana bata amma kafin ta cinye guda d'aya ma aiki ne.
Da sallama ta shiga Maman ta amsa ta saki murmushi tana kallon ta Rauda kuma ta sauke kanta k'asa ta zauna tace, "Barka da dare Mama."
"Barka dai Fulanin Asad, ina aka baro mai martaban kuma?." Jin yadda Mama tayi mata magana da barkwanci sai ta d'ago ta kalle ta sai taga tana ta murmushi ta sunkutar dakai k'asa tana murmushin itama.
"Nazo na sake duba jikin Mama ne kafin na kwanta." Mama taji dad'i har zuciyar ta tace, "Jiki Alhamdulillah, daman tarin hakki ne yayi min yawa yanzu kuma duk da kuka yafe sai nake jin ina ta samu lafiya." Rauda bata ce komai ba tayi shiru Suhaima ma batayi magana ba.
Mama tace, "Kije ki huta dare yanayi." Rauda ta mik'e tace, "A kwana lafiya." Daga haka ta juya ta fita tana ji a zuciyar ta badan Umma tace ba wallahi bazata zo ba ta yafe mata amma tana jin haushin ta.
Mama ta kalli Suhaima tace, "Raka ni b'angaren su Sa'adatu" ta fad'a tana mik'ewa Suhaima ma ta mik'e tace, "Mama bakya jin dad'in jikin ki fa." Mama tayi murmushi tace, "zan iya zuwa." Gaba Mama tayi Suhaima na binta a baya da jakadiyar ta har b'angaren Hajiya.
Mama ta manta rabon da ta shiga b'angaren ta hakan ya saka taga ya canja mata amma bata nuna ba hadiman Hajiya suka mik'e ana gaishe ta da Mama ta amsa kafin a sanar da Hajiya zuwan ta su shiga ciki. Tana ganin Mama ta mike tana fad'in, "Rabi'atu da kanki keda baki da lafiya?."
Mama ta zauna itama ta zauna tace, "Jiki Alhamdulillah na samu lafiya." Hajiya tace, "Haka muke fata." Mama ta kalle ta tace, "Nazo neman afuwa akan abubuwan da suka faru a baya wanda nasan na aikata a abubuwa da yawa wanda baau kamata ba, ayi haƙuri dani." Ba k'aramin Mamaki Hajiya tayi ba ta kalli Mama ta girgiza kai kana tace, "Haba babu komai mune mukayi laifi bake ba."
Mama tace, "Nima nayi."
"Amma ba kamar ni ba, nayi abubuwa da yawa a bayan idanun ku wanda baku sani ba, tuun ranar da aka haifi su Asad nake tsaye a kansu dan ganin dukkan su babu wanda za'a mora a cikin su har girman su. Adadin abubuwan da na aikata dan dakushe su bazasu irgu ba dole na nemi afuwar ki nima Rabi Asad ya yafe min saura ke." Mama tayi murmushi tace, "Duk abinda kuka aikata nice na jawo, halina ne ya jawo badan halina ba da duka baku aikata ba, da kun rik'e su tamkar y'ay'an ku amma nine na raba na nuna kuda su akwai banbanci."
Hajiya tace, "Duk da haka ai ke baki nufe mu da sharri ba mu kuwa fa?." Mama tayi murmushi tace, "haka ne, nidai na yafe ko meye ina fatan a yafe min nima." Hajiya tace, "Naji dad'in yafiyar ki nima kuma na yafe miki koma meye, Allah ya bawa Asad ikon cigaba da mulkin sa cikin aminci da lafiya, Allah ya bawa Aliyu lafiya" ta fad'a muryar ta rawa sosai sabida kuka da yake so ya kwace mata.