← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 131

Sashe 114

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaba kawai Rauda tayi ta biyo bayan ta suka fito harabar b'angaren Rauda ta nan suka shiga wata k'ofa sai gasu sun bayyana a harabar b'angaren Asad d'in sai da ta rakata har bakin falon sannan ta zube a k'asa tace, "A fito lafiya ranki ya dad'e." Da amin Rauda ta amsa duk tana jinta wani iri domin bata saba wad'annan abubuwan ba mace ta haife ta ta dinga zube mata a k'asa.

Kai tsaye falon ta shiga babu kowa ta tsaya tana k'are masa kallo in akace had'uwa to falon ya had'u carpet d'in kamar jikin mage, numfashi ta sauke tace, "Ko ina zan bi kuma oho." Tayi k'aramin tsaki ranta sai taji ya sake b'aci haka kawai komai ya dagule mata ta rasa ma abinda zatayi.

Ciki ta sake shiga ta sake ganin wani falon amma bai kai wancan girma ba amma shima babba ne akwai kyau duka hotunan Asad d'in a manne a jikin sa dana mahaifin sa, stair d'in ta gani kai tsaye ta nufe su ta fara takawa zuwa saman ba tare da tsoron komai ba. Wani falon ta sake shiga mara kayan da yawa amma ya tsaru shima a nan hoton  mahaifin sa da dukkan su har Mama yake a manne baza ka gane shi a jikin hoton ba domin kaya iri d'aya ne a jikin su.

Kai ta d'auke daga kan hoton ta kalli hanyar d'akunan kamar bazata shiga ba sai kuma kai tsaye ta nufi d'akin farko ta buɗe, girman d'akin ya bata tsoro domin gadon kamar ba'a saka ba gashi tafkeke a tsakiyar d'akin amma kamar babu sabida girman d'akin, har zata kulle sai ta hango hoton ta a kan bedside drawer wanda aka d'auka lokacin da suna Cairo.

Fita tayi daga d'akin ta dawo falon ta zauna tayi shiru domin ta tabbatar baya nan sai ranta ya sake b'aci haushin sa ya ninku a zuciyar ta tayi shiru ta rasa abinda zatayi.

          A b'angare Asad sun fita shida mahaifin sa da Suhail da kuma Uncle kai tsaye wajan Mama suka wuce suka same ta tana nan dai yadda take sai Suhaima da taji sauk'i sosai jikin ta ya warware. Tun shigowar su Suhaima ta mik'e tsaye security d'in da take kula dasu ta fita mai martaba ya kalli Suhaima yace, "Autar Mama ya jikin naki?."

Sai kawai ta fashe da kuka tana fad'in, "Abba jikin Mama baya sauk'i ko kad'an."
"Waye yace miki baya sauk'i? Kira mana likitan muji." Ba musu ta fita sai gata da likita sun dawo ya gaishe su gaisuwar girmamawa kafin ya mai martaba yace, "Wanne cigaba aka samu akan ciwon nata?."

Dr yace, "an samu cigaba a da bp ta baya sauka amma yanzu ya sauka ya dawo normal jiran farkawar ta kawai yake yi." Asad yace, "bugun zuciyar fa?." Dr yace, "Shima ya ragu amma bai dawo daidai ba har yanzu, amma in sha Allah daga yau zuwa gobe zata iya farkawa."

Asad ya k'arasa kusa da ita yana yi mata addu'a har lokacin da oxygen a hancin ta, a wannan lokacin k'annen ta suka shigo mata su biyu ganin su mai martaba suka gaishe shi yace, "Ya mai jikin?." Ta kalli Mama kafin tace, "Alhamdulillah gata nan a kwance."

Ta kalli Suhaima tace, "Suhaima ki tafi tare da Antyn ki kije gidan ta ki huta zan zauna da Maman a nan in yaso gobe sai ki dawo kema baki da lafiya." Fuska ta kwab'e zata musa Asad yace, "Ki tafi." Dole tayi shiru bata ce komai ba a nan su Asad suka bar su suka fita kai tsaye mai martaba yace su wuce asibitin da Waziri yake.

Shima yana kwance har lokacin bai farfad'o ba suka yiwa iyalan sa ya mai jiki da addu'ar samun lafiya, har zasu juya su fita matar sa tace, "Allah yaja zamanin mai martaba daman ina so zan kawo k'ara." Abba yace, "To k'ara wacce iri?." Tace, "Akan sane ina so a bi min hakkina dana y'ay'ana sakamakon kashe su d'in da yayi, bazan bar maganar nan ba shiyasa nace zan sanar dakai ko na kai k'ara human right."

Kai Mai martaba ya girgiza kafin yace, "Ya kashe miki y'ay'a kamar ya kenan?." Tace, "Ta son zuciyar sa da neman duniyar sa mana, ya karb'o abu dan ya ksshe wani ya k'are a kan y'ay'ana ni kuma wallahi bazan yarda ba."
"Shikenan ki jira ya samu lafiya sai ayi maganar gabad'aya, banda batun kai k'ara zamuyi maganin matsalar da kan mu."
"Na gode Allah ya k'ara girma ya k'ara lafiya" suka amsa da amin kafin su sake fitowa suka shiga mota amma babu wanda yake cewa kanzil.

         A can gidan lokaci d'aya wutar gidan ta d'auke duhu ya mamaye ko ina aka rasa daga inda matsalar take, Rauda na zaune taga haske ya d'auke duhu sosai ya mamaye inda take sai tsoro ya shige ta hannu na rawa ta kunna hasken wayar ta amma kamar bata kunna ba iya inda take kawai take ganin hasken.

Motsi ta dinga ji a bayanta gabanta yayi mugun fad'uwa ta kasa juyowa balle jira take kawai taji an shake ta ta baya. "Hiii Gambia Rauda!" Aka fad'a daga bayan ta ana dawowa ta gaban ta. Wayar hannun ta ta sub'uce ta fad'i k'asa jikinta ya soma rawa har lokacin bata kalli waye ba.

Dariya yayi sosai ya kunna tashi fitirar ya haske kansa yace, "K'anin mijin kine Hydar, kar kiji tsoro." Maimakon tsoron ya ragu sai ya sake k'aruwa jikinta ya cigaba da rawa tana kallon sa amma bata iya cewa komai. Yace, "Zauna ki nutsu magana nazo muyi dake ta fahimta, zauna" ya fad'a yana zama shima dole itama ta zauna tana kallon sa.

"Magana ce nazo muyi dake ta fahimta wacce zaki tsira mijin ki ma ya tsira. Ba zama nazo yi ba balle surutu magana nake so muyi guda biyu ko nace zab'i ne zan baki guda biyu ko guda uku wanda kika amince dashi zamuyi amfani. Na farko ga magani yanzu ki karb'a Kisha a gabana cikin jikin ki ya fita, na biyu ko ki amince dani a wannan daren mu kasance da juna nida ke, na uku ko na kashe mijin ki. D'auki d'aya a ciki da sauri ba b'ata lokaci nazo yi ba."

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!" Shine abinda Rauda take fad'a kenan jikinta yana rawa zuciyar ta na bugawa sosai ta zuba masa ido ta rasa abinda zata yi. Jin tayi shiru ya skaa shi daka mata tsawa yace, "Baki ji me nace bane?!." Ta sake firgita tace, "Naji" murya tana rawa sosai. Yace, "iskanci ne ya saka kika yi min banza kenan? Babu wanda zai kwace ki a yanzu domin dukkan su basa nan zan iya yin duk abinda nake so dake a yanzu kuma kisha maganin ta k'arfi kuma na kashe mijin naki babu abinda kika isa kiyi. Na baki zab'i ne dan kawai ina ganin mutuncin ki amma in kina ganin baza ki zab'a ba..." ya fad'a yana tasowa yayo kanta ta zabura ta mik'e tayi baya tace, "Zan zab'a! Wallahi zan zab'a ka tsaya."

Kuka take yi tana maganar ya tsaya yace, "Ina jinki." Tace, "bani maganin zan sha, amma kayi min alƙawarin in nasha zaka kyale mu." Hannu ya wara kafin yana kallon ta ta hasken fitilar wayar ya mik'a mata tablet d'in da ruwa a k'aramar jarka hannunta yana rawa ta b'alla amma ta kasa sha sai kuka da take yi.

Hannu taga ya mik'o zai jata jikin sa bata san lokacin da ta cilla maganin bakin ta ba ta kafa kai tana shan ruwan a haukace a daidai lokacin motar su Asad ta shigo cikin gidan.
[17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*087.*

         Kamar walqiya sai ta neme shi ta rasa nan take haske ya mamaye d'akin duk ta jiqe da gumi sai numfashi take saukewa k'irjin ta yana sama da k'asa ruwa duk ya zubar mata a jikinta. A kan carpet ta zauna ta cure waje d'aya tana sauke numfashi tsoro yaka sake mamaye mata zuciya.

Motar su Asad tana tsayawa haske ya mamaye gidan Uncle yace, "Da me ya samu wutar gidan haka?." Babu wanda ya amsa Mai martaba ya kalli Asad yace, "to sai da safe bance ka biyo ni duba Aliyu ba." Amsawa yayi cikin gamsuwa Suhail ya raka shi har b'angaren sa. Kallon Suhail yayi sai yaga yana ta murmushi ya kalle shi yace, "Murmushin na meye?."

Suhail ya sosa kai yace, "A'a ranka ya dad'e wani abun na tuna." Asad yayi k'aramar dariya ya kawar da kansa yana jinjina kai kafin yace, "Fad'a min as your friend." Suhail ya kalle shi sai ya sauke kai k'asa yace, "Ranka ya dad'e wannan labarin baya ne ni yanzu ko iya kallo fuskar mai martaba ma bana iyawa." Asad ya murmusa ya shiga ciki Suhail ya juya ya fita.

Kai tsaye saman ya hau dan shi yama manta an kawo Rauda gidan hankalin sa yana wajan Mama yana hawa ya hango mutum a cure a waje d'aya sai gaban sa ya fad'i ya tako ya k'araso wajan yaga robar ruwa a wajan a yar ga tablet na magani a kwali ya kalli inda take amma baiyi magana ba.

Jin motsi ya saka Rauda d'agowa ganin sa ya saka ta zabura ta mik'e ta k'araso inda yake ta rugume shi sosai tana kuka cikin tsoro har lokacin jikinta rawa yake yi. Hankalin sa ya tashi ganin yadda take hakan ya tabbatar masa akwai abinda ya faru ya d'ago ta daga jikin sa ya rik'e ta yana kallon fuskar ta da ta jiqe da hawaye yace, "Lafiya kike?."

Numfashin ta sama da k'asa yake yi bakinta yana rawa tace, "Hydar! Hydar ne yazo nan, tsoro nake ji" ta sake fad'a tana sake komawa jikinsa jin abinda ta fad'a sai ya rik'e ta sosai hankalin sa kai k'arshe wajan tashi burin sa yaji abinda ya faru.
Chapter 114 · 0% Book details