Sashe 87
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Baba yace, "Umarni ne ba alfarma ba, duk abinda mai martaba yace an gama." Asad yayi shiru ya d'auki waya yana dannawa jim kad'an sai ga nurses guda biyu mata sun shigo falon suka zube a gaban sa suka ce, "Mun amsa kira ranka ya dad'e." Da hannu ya nuna musu Rauda jiki na rawa suka k'arasa inda take suka duk'a sukace, "Ranki ya dad'e sannu" tare suka kama Rauda suka fita da ita zuwa waje, suka sake dawowa aka rik'e Umma suka sake fita Yaya Ummi da Yaya Fariha suka bisu dan sunji dad'in zuwan da kodan Rauda ta samu kulawa.
Asad yaja numfashi ya lumshe ido ya buɗe zuciyar sa na dukan tara tara yace, "Nasan zakuyi mamakin ganina a nan, a fara samar mata lafiya komai zai biyo baya. Alfarma a gare ku gabad'aya dan Allah a bar maganar a nan." Kowa mamaki ya bayyana akan zuciyar sa sai kallon kallo suke yi kowa tunanin sa ta yaya yasan maganar? Kenan daman ita ta kawo shi kome?.
Baba ya gyara zama yace, "Ranka ya dad'e abinda ya faru fa ita Raudan cikin....." da hanzari ya katse Baba yace, "Baba dan Allah wannan kalaman su daina fitowa daga bakin ka." Baba da mamaki yace, "Ranka ya dad'e bikin ta ya kasance saura sati biyu kawai, da wanne ido zan kalli shi wanda zata aura nace masa tayi cikin shege...?."
"Hasbunallahu wani'imal wakil!" ya furta yana dafe kansa ji yake kamar ya toshewa Baba baya son abinda yake furtawa ko kad'an akan cikin da ya kasance na halak wanda aka same shi da aure, ga kuma zancen wani banza da yake masa wanda bazai tab'a mallakar abinda ya mallaka ba har abada shine ya saka shi yin salati ba tare da ya shirya ba.
Jin hakan sai Baba yace, "Tuba nake ranka ya dad'e, Allah ya wuci zuciyar ka, na bar maganar sai ta samu lafiyar kamar yadda aka umarce ni." Kai Asad ya girgiza kai kafin ya kalli sauran ragowar matan yaga biyu sun ragu alamun sun bi su Umma sai ya dawo da kallon sa ga Baba yace, "Zan koma, amma zan dawo" ya fad'a yana mik'ewa tsaye duk sai suka mik'e shima har waje suka raka shi ana godiya ya shiga bayan mota ya sauke glass bayan ya shiga yace, "Baba duka ya k'are dan Allah" ya fad'a a tausahe yana kallon Baba.
"An gama ranka ya dad'e, Allah ya kiyaye hanya." Glass d'in ya d'aga aka ja motar suka bar wajan kowa yabi motar da kallo da mamaki a zuciyar dukkan su. Ciki suka koma Baba ya zauna Kawu Badamasi yace, "Adamu mai martaba da kansa yazo gidan nan ya ceci Rauda daga dukan da kake mata, ya akayi yasan abinda yake faruwa har yazo ya cece ta? Abubuwan da suka faru a baya tsakanin shi da gidan nan ban d'auka zai sake waiwayo ahlin mu gabad'aya. Meyasa yake jin haushi dan kana kiran cikin jikin Rauda na shege? Anya kuwa ba......" Sai kuma kawu Badamasi yayi shiru yana jijjiga kai jin girman abinda zai fad'a da kamar wuya ya kasance.
Yayar Mu tace, "Abinda ya daure min kai kenan Kawu ya akayi yasan abinda yake faruwa? Bibiyar lamarin gidan nan yake ko me? In bibiya yake akan me to muda ba wata alaqa ce a tsakaninmu dashi ba?. Aure ne ya had'a kuma ya raba meyasa yazo a wannan lokacin har yake neman alfarma a haka duk da tarin matsayin da yake dashi?."
Kawu Mansur yace, "Gashi mun tabbatar da saki a tsakanin su har takardar tana hannun Yaya Adamu dukkan mu munga takardar sakin a lokacin me hakan yake nufi?." Baba ya sauke numfashi yace, "ni nama rasa bakin magana wallahi, amma mu jira ta samu lafiya itace zata warware mana komai. Babban tashin hankalina shine Anas."
"Mu bari zuwa gobe ai komai zai daidaita in yaso sai ayi maganar Anas daga baya." Baba ya kalli Yaya Shamsiyya yace, "Kira Ummi muji a wanne asibitin suke."
"Na kira su bayan fitar ka wai asibitin da Rauda ta kwanta lokacin da akayi mata aikin k'afa suka nufa."
Baba ya sauke numfashi yayi shiru na wani lokacin kafin yace, "ku tashi ku wuce gida kuma anyi i'sha" ya fad'a suna tashi suka fita domin yin sallah.
Karb'ar gaggawa aka yiwa Rauda aka kwantar da ita nan da nan aka fara bata kulawa ta musamman wacce zatayi gaggawar taimakawa jikinta wajan dawowa daidai. Umma jinin tane ya hau itama aka saka mata ruwan da bp zaiyi k'asa nan da nan bacci ya kwashe su duka. Yaya fariha ta tafi gida Yaya Ummi ta yiwa mijin ta waya ta sanar dashi zata kwana ya kai y'ay'an ta gidan su wajan Inna.
Asad tun bayan da ya koma guest house shi kad'ai ya zauna ya zuciyar sa cike da tunanin abinda ya faru gabad'aya ya rasa abinda yake damun sa farin ciki yake ji ko akasin sa bai sani ba, waya ya d'auka ya kira Dr Yasir babu b'ata lokaci ya d'auka yace, "Ranka ya dad'e, Allah yaja zamanin ka an gama komai an basu kulawar gaggawa dukkan su sun sami bacci." Shiru yayi bai amsa ba na wani lokaci. Dr Yasir ya fahimci karin bayani yake so hakan ya saka yace, "Allah yaja zamanin mai martaba komai lafiya a b'angaren k'aramar, hatta abinda yake jikinta yana nan lafiya babu abinda ya same shi."
Sai a sannan ya sauke numfashi ya sauke wayar daga kunne sa ya ajjiye a gefe ya jingina da kujera yayi shiru yana kallon sama. Inda yasan ciki ne zai bayyana a abinda ya faru da bai bar hakan ta kasance ba duk da daman ba'a son ransa ba amma da yayi k'ok'arin rik'e kansa, k'aramin tsaki yaja tunawa da bikinta wai saura kwana sha hud'u a bayyane yace, "Bata da hankali ne." Sai kuma yayi murmushi tunawa da cikin sane fa a jikinta kuma silar sa dole a fasa auren ta da wani duk da ko babu cikin ma sai an fasa tunda matar sace, d'an dukan kansa yayi yana tunanin ta wacce hanya kuma zai bi ya cewa su Baba cikin sane a jikinta?.
Numfashi ya sauke ya kalli wayar sa yaga tana haske ganin mai kiran sai ya d'auka ya saka a kunne, "Okay good" abinda ya furta kenan ya sauke wayar daga kunne ya mik'e tsam ya fita drivern sa yaja suka fita daga gidan gabad'aya.
*☆☆☆*
Jidda na zaune a b'angaren sa a falon sa na sama duk ranta a b'ace yake hankalin ta kuma a tashe, ganin zaman bazai kai labari ba sai ta mik'e tana ta zagaye har ta fara jiyo takun sa ta juya ta ganshi ya shigo yana waya yana shigowa falon ya sauke wayar daga kunnen sa. Jidda ta matso kusa dashi tace, "My king ina kake zuwa a cikin kwanakin nan kai kad'ai? Ko dogarai baka d'auka fitar sirri kake yi kuma sai dare na kasa fahimta."
Kallonta yayi ya sakko da idanun sa ga cikin ta sai yaji wani iri a zuciyar sa ya d'auke kai baice mata komai ba ya wuceta zuwa d'aki, ta d'aga kafa zata biyo shi ya d'aga mata hannu ya girgiza yatsa d'aya dole taja ta tsaya shi kuma ya wuce zuwa d'akin sa ba tare da ya sake kallon ta ba.
Juyowa tayi ta sakko daga saman a guje ta fita zuwa b'angaren ta aka rufa mata baya masu rik'e alkyabbar ta gudun kar taja k'asa sai gudu suke sabida sauri take yi sosai.
Tana shiga b'angaren ta ta dakatar dasu ta shiga falo na biyu ta tarar da hasken gabad'aya a kashe ta kunna idanun ta ya fad'a cikin na Aliyu da yake a kan kujera yana kad'a k'afar sa, tsoro ya mamaye mata zuciya ta firgita ya kalleta ta k'asan idanu sai yayi murmushi ya mik'e tsaye yace, "Meye shirin ku na gaba akan Mama?." Baya take ja tana girgiza kai tace, "bamu da wani shiri."
Baki ya tab'e ya girgiza kai zuciyar sa nayi masa mugun ciwo yana cize bakin sa ya lumshe idanu ya buɗe baice komai ba kawai ya fita ya bar mata falon ma gabad'aya. "Na shiga uku na ni Jidda me na jawowa kaina haka?" Ta fad'a zuciyar ta na bugawa domin ita kad'ai tasan hatsarin kasancewar Aliyu a cikin gidan nan ba k'aramin tashin hankali bane a gare ta.
"Mum!!" Ta furta da k'arfi tana zama jagwab akan kujera ta dafe kanta kawai sai ta fashe da kuka hankalin ta a matuk'ar tashe yake zuciyar ta karkarwa take yi sabida tsoro, kai take girgizawa tace, "dole nayi maganin sa da kaina, dole na kashe Aliyu bazan barshi ya zame min barazana a cikin gidan nan ba, dole naga bayan sa da kaina zan gudanar da wannan aikin" ta fad'a tana tashi ta shiga d'aki tana tunanin irin hanyar da zata bi dan ganin bayan Aliyu.
A b'angaren Mama tana zaune tana waya ita kad'ai a bedroom d'inta tana fad'in, "Ina kake zuwa ne Asad? Kwana biyu kana fita babu wanda ya sani ina kake zuwa kai kad'ai?." Shiru tayi alamun yana bata amsa kana tace, "yadai kamata ka cigaba da kulawa bana son wata matsalar ta sake faruwa koda nan gaba."
Shiru tayi kafin ta datse wayar ta sauke numfashi tana jin farin ciki a ranta komai yana tafiya daidai sai kuma tace, "Mai martaba." Shiru tayi tace, "ya zama dole a hana bakin sa buɗewa in hakan ta kasance I'm in trouble" ta fad'a tana tashi da gaggawa ta saka alkyabbar ta ta nufi b'angaren sa.
Tana shiga ta tarar da Dr da yake kula dashi ya kalle ta yace, "Good day madam." Da yake bature sai tace, "How was your work."
"Fine ma'am."
Kallon sa tayi suka had'a ido sai ta d'aga masa kai shima ya d'aga mata kawai sai ta juya ta fita shi kuma ya d'auko allura a aljihun sa ya balle kanta yaja a sirinji ya zuba Mai martaba a cikin ruwan da yake shiga jikin sa.
*☆☆☆*
Washe gari.