Sashe 38
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da Suhaima ta fad'a d'akin da take tunanin na Rauda d'in ne ta had'a kayan da ta da ta gansu a wajan wanda zasu shiga wanda baza su shiga jakar ba ta barsu a wajan taga wayar ta a kan gado ta d'auko ta cusa magani a aljihun jakar ta jawo da sauri tana addu'ar Allah yasa Mama sun bar wajan. Tana fitowa babu Mama da Asad a wajan ta sauke numfashi ta hango Rauda a zaune a gefen wani d'aki ta had'a kai da guiwa sai passport d'in ta a kusa da ita ta k'arasa inda take tace, "Ga wayar ki ga kayan ki na bar wasu a ciki baza su shiga ba. Kiyi haƙuri da abinda Mama tayi miki na tabbata Yaya Asad yana sonki zai kuma dawo gare ki" abinda tace kenan ta ajjiye mata tabi bayan su da sauri ta shiga elevator ta sauka.
Da kallo ta bi bayan ta ta kuma fashewa da kuka mai tsuma zuciya ta kwanta a wajan ba tare da tasan abinda zatayi ba. K'arar bud'e elevator taji bata d'ago ba taji anzo kanta an tsaya idanun ta sunyi nauyi bazata iya kallon ko waye ba hakan ya saka bata motsa ba sai ajiyar zuciya da take yi.
Cikin harshen turanci taji ance, "Hotel d'in mu baya buk'atar zaman ki ki tashi ki fita ko mu kira miki y'an sanda su kama ki." Gabanta ya fad'i ta daure ta d'ago ta kalli wanda yake magana taga security ne ta tashi zaune ta dafe kanta da hannayen ta duka biyun zatayi magana akazo wajan bata iya kallon wanda yazo wajan ba taji ance, "A'a chocolatly lafiya kike a nan?" Dr Khalifa ya fad'a yana k'arasowa inda take kwance.
Kallon security d'in yayi cikin harshen larabci yake tambayar sa lafiya, security d'in yace, "an sanar damu babbar mai aikata laifi ce daga Nigeria,.ta fita daga hotel din nan ko mu kaita wajan y'an sanda bama som zaman ta a nan." Da mamaki Dr Khalifa ya kalle shi ya kalle ta yace, "Chocolaty me yake faruwa haka? Ina prince yake?." Ta kasa magana sai rawar jiki da jikin ta yake yi hakan ya saka shi tab'a wuyan ta yaji zafi rau yace, "Subahanallah" ya kalli security d'in yace, "waye ya baku wannan masaniyar? Ina wanda suke tare da ita yake?."
Security d'in yace, "bai dame mu ta tashi ko mu fitar da ita ta k'arfi." Dr Khalifa yace, "basai anje nan ba" ya kalli Rauda yace, "tashi mu tafi kafin su saka a kama ki kin san nan ba Nigeria bace tunda aka fad'a musu baza su amince dake ba." K'okarin tashi take yaga ta kasa ya kama hannun ta duka biyun ta tashi tayi baya zata fad'i tana dafe kanta yayi saurin rik'e ta yana fad'in, "Sannu." Jakarta yake jaya d'auki wayar ta da passport d'in ta suka shiga elevator suka sauka.
Suna barin wajan Asad ya dawo yaga bata wajan ya bud'e d'akin duk yasan bazai ganta ba ya duba ya sake kullewa yana kallon wajan yana tunanin ina taje zuciyar sa na bugawa sosai fiye da d'azu. Komawa k'asa yayi ya koma reception wajan ma'aikatan wajan da harshen larabci yace, "Ina son ganin camera na wajan k'ofar d'akin 012 special room." Dannawa wanda yayiwa maganar yayi nan take akazo inda security suka je kanta da inda Dr Khalifa yaje kusa da ita har yadda ya rik'e ta suka tashi suka shiga elevator.
Mummunan sarawa kansa yayi ganin yadda Khalifa ya rik'e k'ugun ta ga hannun sa a cikin nasa ya dafe zuciyar sa yana jan numfashi dak'yar yayi baya zai fad'i sukayi saurin tare shi ta baya suna jera masa sannu, zaunar dashi sukayi aka kawo mai ruwa mai sanyi amma bai iya sha ba abinda yake gani kawai a idanun sa shine yake sake tayar masa da hankali sai numfashi yake ja dak'yar kamar wanda zai bar jikin sa.
"Asad!." Mama ta fad'a daga bayan sa ganin an zagaye shi ta k'araso wajan tana kallon ma'aikatan wajan tace, "me kake jira ne basu key d'in kenan?." Kai ya dafe ya zaro key d'in motar hotel d'in da yake amfani da ita ya basu ya tashi tsaye dak'yar yana jin jiri na d'aukar sa ma'aikacin da yake kula da computer yace, "akwai ragowar kud'i da bai k'are ba na d'aki da kuma na motar." Da hannu Asad yayi musu alama ya wuce Mama tabi bayan sa zuciyar ta a cushe tunanin ta kawai kenan baiyi niyar dawowa ba yana nan yana kashewa y'ar talakawa kud'i.
Taxi suka shiga Asad tunda suka shiga motar baice komai ba titi yake kallo yana jan numfashi dak'yar amma kuma a idanun sa Khalifa yake gani rik'e da k'ugun Rauda sai yaji kamar an soka masa mashi a zuciyar sa, _ina zai kaita? A ina zai ajjiye ta? Me zai mata da ya suka bar hotel d'in tare? Meyasa ya rik'e ta?._ Babu wanda zai bashi amsa ya sake kallon titi zuciyar sa ta kuma cewa, _meyasa ta bari ya rik'e ta? Meyasa ta bishi bayan tasan bazai iya tafiya bai nema mana mafita ba?, yanzu ina zasu je? Gidan sa zai kaita?, to su zauna ita dashi kenan?._
Tunanin hakan ya saka shi dafe kai tare da furta, "Hasbunallah!." Mama ta kalle shi batayi magana ba suka tsaya a hotel d'in da sukayi booking suka fita bashi da zab'in da ya wuce ya fita shimq duk da jirin da yake ji suka shiga ciki. Upstairs hotel ne dole suka shiga elevator zuwa d'akin da suka kama suka shiga ciki.
Babban falo ne k'ofa biyu a cikin sa da alama shima dak'una biyu ne Mama ta bud'e d'aki na farko tace, "Shiga kayi sallah." Bai musa ba ya shiga ta kulle k'ofar ta kalli Suhaima da take kallon ta tace, "meye kike bina da kallo?."
Ta langwabar da kai tace, "Mama bashi da lafiya fa kamata yayi mu wuce asibiti ba nan ba, jiri yake yi fa kamar zai fad'i." Ta tab'e baki tace, "Asirin ne yake sakin sa sai a hankali."
D'aya d'akin Mama ta shiga zuciyar ta fesss tayi wanka ta da alwala ta canja kaya tayi sallah ta d'auki wayar ta tana neman number Mum amma bata same ta ba. Suhaima ma a d'akin ta shirya tayi sallah ta fita zuwa restaurant d'in hotel d'in ta debo musu abinci ta dawo d'akin ta kawowa Mama ta kalli abincin tace, "bara na duba sji" ta fad'a tana tashi ta nufi d'akin da Asad yake.
A zaune ta same shi da alama ko alwalar ma baiyi ba hannun sa a kansa yayi shiru ko motsin kirki bayayi, k'arasowa tayi kusa dashi zuciyarta na sake jin haushin Rauda da tsanar ta tace, "Taya bazan tsani yarinyar nan ba tayi maka abinda ko sallah ka kasa tashi kayi bayan ba haka kake ba?" ta fad'a tana isowa inda yake ya kalle ta da jajayen idanun sa kafin ya saukar da idanun sa k'asa.
"Daurewa zakayi ka tashi kayi wanka then kayi sallah sai kasha magani ko muje asibiti." Baya son mata musu ko kad'an hakan ya saka shi ya tashi ta rik'e shi tace, "Sannu Zaki, sai a hankali asirin zai bar jikin ka."
_Asiri_ ya maimaita a zuciyar sa cikin wani irin yanayi na tunani da mamakin kalmar ya shiga band'aki, fita tayi ta barshi. Lokacin da ya fito yaga jakar sa ta kaya ya ya bud'e ya saka doguwar riga kamar kullum ya tayar da sallah bayan ya idar ya zauna yayi shiru yana jin kewa a zuciyar sa kamar marayan da ya rasa iyayen sa a lokaci d'aya. Hawaye yaji suna taruwa a idanun sa zuciyar sa na bugawa sosai amma yak'i barin kukan ya sakko.
Kamar ya tuna wani abu sai ya d'auki waya da sauri da niyar kiran ta yaji Mama tace, "In ka sake ka neme inda take zaka had'u da fushina Asad, bana so ka sake waiwayar ta daga nan har a tashi duniya indai na kasance uwa a gare ka." Ajjiye wayar yayi a gefen jikin sa a sanyaye ba tare da yayi kiran ba ya daure zuciyar sa da ta karaya yana ji idanun sa na kawo ruwa kamar zaiyi hawaye amma ya mayar dasu ya hana faruwar hakan dan farin cikin Maman sa.
Abinci ta ajjiye tace, "d'auki kaci." Kai ya girgiza alamun bazai iya ba yana runtse idanun sa, waya ta d'auka yana dannawa kafin ta saka a kunne tace, "Suhaima kawo masa tea." Ba jimawa ta shigo dashi a kofi ta Mama ta karb'a ta bashi ya karb'a yasha kad'an ya ajjiye kofin Mama ta bashi maganin hannun ta tace, "sha zaka ji dad'in jikin ka." Ya karb'a yasha ta sake fita jim kad'an ta dawo ta bashi wani a kofi tace, "karb'i wannan ma."
Shima baice komai ba ya karb'a yasha ta kuma kallon sa tace, "ka kwanta ka huta yanzu anjima in ka tashi zaka ji dad'in jikin ka." Kai ya d'aga ya tashi tsaye kamar yadda tace ya zauna a gefen gadon tayi murmushi kana tace, "Allah yayi maka albarka Asad, Yadda kake son abinda nake so Allah ya baka abinda kake so kaima." Sai ya kalle ta sai kuma ya sunkuyar da kansa a zuciyar sa yace, _Abinda nake so kin raba ni dashi Mama._
"Suhaima kin kira Hydar d'in ya jikin mahaifin naku?" Ta fad'a tana niyar fita sai kuma ta dawo tace, "Nasan baka san bashi da lafiya ba ko?, suna Germany da Hydar jikin sa ya rikice lokaci d'aya." Idanu ya lumshe sai yanzu ya fahimci yadda akayi Mama ta sub'uto ta tawo Cairo ashe mahaifin nasa bashi da lafiya.