Sashe 79
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiru basuyi mata magana ba ta kafa kai a kofin tasha ta sauke sai taji yayi mata dad'i yaji kayan khamshi hakan sai ya saka tasha da yawa ta ajjiye ragowar tayi tagumi, Hydar ya cire hannun ta yace, "Dan Allah Mama." Idanun ta ya ciko da kwalla tace, "Aliyu baya nan, Asad ya guje ni sai yaga dama yake zuwa inda nake, Sadiya tana so ta kashe ni, Jidda tana yi min wulaƙancin da take so, mutanen gidan nan gabad'aya sun raina nj ya kuke so nayi?. Bani da uwa bani da uba y'an uwana suna nesa dani me kuke so nayi in ban damu ba?."
Shiru sukayi ganin tana hawaye Suhaima tace, "Amma ranki ya dad'e damuwar ciwo take saka miki, likita yace damuwar da kike sakawa tayi yawa ya kamata ki rage kodan lafiyar ki." Ta sauke numfashi tace, "Nafi buk'atar mutuwa ta a yanzu." Shiru sukayi jin abinda tace ko wanne kansa a k'asa zuciyar su duka a raunane.
Cikin ta taji yana juyawa sai taji tana jin amai ta yamutsa fuska tace, "Hydar bani maganin ciwon ciki a cikin drawer." Ba musu ya juya yana neman maganin yaji ihun Suhaima tana cewa, "Yaya Hydar Mama!" Ta fad'a tana yin kanta suka ga tana shak'uwa idanun ta na juyewa suna komawa farare babu alamun bak'i a cikin farin abu na fita a bakin ta kafin Hydar ya k'araso tuni Mama ta zube akan gado babu numfashi.
*☆☆☆*
"Ashe zaku iya cin amanata ban sani ba?" Aliyu ya fad'a yana kallon Waziri da hajiya idanun su sunyi fik'i-fik'i alamun marasa gaskiya. Gyara tsayuwa yayi jin sun kasa magana yace, "baza kuce komai ba?." Waziri yace, "Aliyu ka saurare ni."
"Kace min me?."
"Abinda kake tunani sam ba haka bane ba, mu kan mu bamu san meyasa ka maqale a wata k'asar ba."
Ya harde hannayen sa a k'irji yana bin su da kallo yace, "Shine baku tab'a nema na ba?."
Fulani Hajiya tace, "Na kira ka bana samun ka." Yayi murmushi mai kyau ya taune lips d'in sa yana jin d'aci a zuciyar sa yana girgiza kai.
"Amma yanzu tunda ka dawo zamu d'ora daga inda muka tsaya ko Fulani?" Ya fad'a yana juyawa ya kalle ta ta d'aga kai tace, "Daman mun rasa wanda zai shafawa Asad maganin da zai bar karagar nan baki d'aya tunda ka dawo mu abin murnar mune ai."
"Da ban dawo bafa? In kuka yi nasarar shafa masa maganin waye zai hau karagar kenan?." Alamun rashin gaskiya ya bayyana a tare dasu suks kalli juna Hajiya tace, "Ai bai ma farun ba, ka daina tuna baya dan Allah muyi abinda yake gaban mu yafi mana alkhairi."
"Ai bazan kuma amincewa daku ba domin dukkan ku munafukai ne, kunce min matar Asad baza tayi ciki ba sai gata da ciki har ya bayyana ko bamuyi haka daku ba?." Waziri yace, "Sammatsi aka samu ne ranka ya dad'e amma yanzu zamuyi iya bakin k'ok'arin mu koda yaron yazo duniya zamu kashe shi dan baza mu bari y'ay'an sa su Shura ba."
Ya murmusa kana yace, "Ita mamana me tayi muku kuke son kashe ta?." A tare suka wara idanu suka ce, "Kisa? Mu din?." Banzan kallon da yayi musu ya saka waziri yace, "bamu tab'a k'okarin kashe Rabi'atu ba, to akan me ma zamu kasheta muda ba ita muke hari ba?." Aliyu yayi murmushi mai kyau ya d'an sosa goshin sabaice komai ba waziri yace, "Yanzu ina tare da maganin da za'a shafa masa ayi maganin matsalar mun tura Suhail amma ya kasa yin komai, kai kad'ai ne zaka kawo k'arshen matsalar nan."
Aliyu ya zuba hannu a aljihu yana kallon su d'aya bayan d'aya yayi shiru baice komai ba duk suka tsargu ganin irin kallon da yake musu yana murmushi wanda yake basu tsoro dan basu san shirin sa ba sun kuma san halin sa akwai dan bazan wayo, "well, ku kawo mu gani." Waziri ya washe bakin sa ya saka hannu a aljihu ya d'auko shi a kwalba ya mik'a masa ya kalla ya kalli wazirin sannan ya karb'a Waziri yace, "Kana shafa masa wannan an tabbatar mana da awa biyu bazata cika ba zai haukace kaga shikenan babu sarauta a hannun mahaukaci."
Aliyu ya jinjina kai yana girmama mugunta irin tasu amma yafi su kaifin tunani dukkan su buga su zai dinga yi kamar ball shi kad'ai yasan mai ya tsaya da kuma abinda zai aiwatar yace, "Da an shafa masa shikenan an gama ka tabbatar?." Waziri yace, "An gama na tabbatar da wannan." Aliyu ya juya ya bar wajan ya shiga mota yaja ya tafi ba tare da yace komai ba.
Hajiya ta kalle shi tace, "Ni nasan za'a yi haka sai da nace ka kashe Aliyun tun ba yanzu ba kak'i, wayon jaraba ne dashi zai iya lalata mana komai, dawowar sa barazana ce ga sarautar ka domin bazai bari kayi ba sai shi." Yayi murmushi yana kallon inda Aliyu yabi yace, "Barshi ya gama yi mana wannan aikin ya shafawa Asad d'in tukunna kiga yadda zanyi dashi, ai yadda ya shafawa Asad shima haka zan saka a shafa masa an fad'a miki k'aramin kaine dani?, duk wannan marairaicewar da kika ga ina yi ina sane tarko ne. Haka na tsara ko master planer da taji wannan sai da tace tsarin yayi ko ita iya abinda zata iya kenan."
Fulani tayi ajiyar zuciya tace, "Har naji dad'i domin na tsani Rabi'atu tsana maimunin gaske, haka na tsani y'ay'anta." Yayi murmushi yace, "Yanzu aka fara wasan fa, barni dashi kawai."
Aliyu da yake tafiya ya saka bt a kunnen sa yana sauraron duk abinda suke fad'a ta cikin bt d'in ya murmusa ya daki sitiyarin motar yace, "Naku wasa ne tunda na dawo komai yazo k'arshe" ya fad'a yana sake take speed d'in motar yana k'warara gudu akan titi.
*☆☆☆*
Yadda babu wanda yasan ya fita haka babu wanda yasan shine ya shigo sai masu gadin k'ofar sa yana hawa sama bai nemi Jidda ba ya shiga d'aki ya kulle kansa abubuwa sun cushe masa kansa yama rasa wanne kalar tunani zaiyi yaji fad'i. Zama yayi a gefen gado yayi tagumi yana kallon wani wajan daban yaji ana buga masa k'ofa.
Yasan Jidda ce domin shi bashi da lokacin ta a halin da yake ciki yana buk'atar kebe kansa amma yasan bazata gane ba, "My king pls ka buɗe magana zamuyi."
"Jidda please leave, I need rest" ya fad'a a sanyaye yana kallon k'ofar.
"Pls my king magana kawai zan maka fa." K'aramin tsaki yaja daman yasan bazata tafi ba ya kwanta a kan gadon ya lumshe ido kafin ya tashi ya shiga wanka.
Yana ji tana dukan k'ofar yayi banza sai da ya gama shiryawa yayi sallah sannan ya buɗe ya same ta a tsaye yana bud'ewa ta fad'a jikin sa tace, "My king nayi maka laifi ne kake share ni?." Ji yayi tana bashi mugun haushi ya runtse ido gabad'aya baya son ganinta kwata-kwata ya dafe kai ya d'ago ta daga jikin sa ta sake komawa ya sake d'ago ta ta sake komawa ya fusata ya fincike ta yace, "I said leave....!" Ya fad'a cikin murya mai amo wacce ta saka ta gigicewa tana kallon sa idanu a waje cikin zallar mamaki da al'ajabi.
[17/12, 10:41 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*065.*
Kallon sa take da mamakin da ya cika mata zuciya ganin ita yake yiwa tsawa har cikin kanta kamar zai dake ta kuma yana kallon ta, sak tayi jiki yayi sanyi ta koma da baya shi kuma ya kulle k'ofar tabi k'ofar da kallo jikin ta a mace kawai ta sauka daga saman ta fita gabad'aya daga b'angaren.
Kamar zata kifa haka take tafiya bata lura ma da jakadiyar ta ba kawai tafiya take tana shiga d'aki ta kulle kanta hannu na rawa take neman layin Mum amma bata d'auka ba ta sake kira bata d'auka ba ta ajjiye wayar tana kallon mudubi gabanta yana fad'uwa.
Hankalin ta mugun tashi yayi ta rasa inda zata saka ranta zuciyar ta na bugawa ta dafe kai da hannun biyu tace, "Na shiga uku, me yake shirin faruwa ne? Yau My king shine ne yake min tsawa haka?" Ta fad'a tana zagaye a d'akin hankalin ta ya tashi sosai ji take kamar tayi tsuntsuwa ta tafi gidan su.
*☆☆☆*
"Dr ka saka mu a gaba baka ce mana komai ba, meya samu Mama wai?" Hydar ya fad'a yana kallon Dr Yasir shima yana kallon sa. Dr Yasir yace, "I'm sorry to say prince, guba Mama tasha."
A tare suka wara idanu waje Suhaima tace, "poison..!." Dr yace, "Eh, kuma poison din ma ba kad'an ba da an sha kashe mutum take kai tsaye dan kunyi gaggawar kawo ta nan ne da babu abinda zai hanata kashe ta." Hydar ya kalli Suhaima sannan yace, "Amma a me tasha gubar Dr?" Ya tambaya cikin tashin hankali yana kallon sa.
Dr yace, "Ba zallar ta tasha ba a wani abun aka zuba mata, inda zaku iya tuna abinda tasha na karshe ko zamu ga ragowar sa zamu iya duba shi wata k'ila a ciki gubar take."
"Tabbas tasha tea, tana gama sha take cemin cikin ta na ciwo na juya na d'auko magani sai na ganta a yanayin da muka kawo ta nan." Dr yace, "To tabbas a cikin tea d'in poison d'in yake, amma dan mu tabbatar zamu iya zuwa mu d'auko ragowa in akwai sai gwada mu gani."
Suhaima tace, "eh ta rage dan bata shanye ba ta ajjiye yana d'akin ta." Dr yace, "Zamu iya zuwa a d'auko mu gani." Hydar ya mik'e tsaye ya fita baice komai ba Suhaima tace, "Ina zuwa Dr" tabi bayan Hydar tana fad'in, "Yaya Hydar tare zaku je a d'auko?." Cak ya tsaya ya juyo yana binta da kallon tuhuma yace, "ta ya Mama tasha poison bayan kece kika kawo mata tea d'in?."
Suhaima ta buɗe baki tana kallon sa da mamaki kafin tace, "Yaya Hydar zargina kake?."
"Meyasa kika yi saurin kama kanki bayan bance ke kika zuba mata ba?." Suhaima ta rud'e tace, "Amma kasan dai babu yadda za'ayi na bawa Mamana poison ko?."
"Shiyasa na tambaye ki ya akayi tasha poison bayan kece kika kawo mata tea d'in?."