← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 131

Sashe 71

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Nafi k'arfin taimakon ku daku da dangin ku baki daya, abinda nake so Ladidi ta fad'a muku baku ji me tace bane?." Yaya Ummi tace, "To tunda kinfi k'arfin taimakon mu dana dangin mu kiji wajan wanda basu fi k'arfi ba mana kin sa sai su taimaka miki, kinga da baki sha wahalar zuwa nan ba. Kije ki nemi wanda baki fi k'arfi ba sai mu gani."

Mama tayi shiru ta rasa me ya kamata tayi dan tasan ita ta kawo kanta, a ka'ida rashin mutunci ya kamata tayi musu ta bar gidan amma kuma tana buk'atar ganin Baba malam kodan bakin da yayi yawa a kansa hakan ya tilasta mata yin shiru badan taso ba zuciyar ta nayi mata mugun suya sabida b'acin rai.

  Suhaima da take gefe a tusashe tace, "Mamana tana so zata ga Baba Malam ne tana so ayi mata hanyar ganin sa dan Allah." Umma tace, "Abinda za'a ce kenan fa tun d'azu ake jan maganar. Rauda shiga ciki ki kira shi a waya ki sanar dashi abinda yace sai kizo ki fad'a mana." Rauda kallon Umma take alamun mamaki kafin tace, "Wai Umma me kike cewa ne? Kina nufin alfarmar zaki yi musu?." Umma ta zare mata ido tace, "baki ji me nace bane kike kallona?."

Tashi tayi ta shiga d'akin falon ya zauna shiru babu motsin kowa duk sunyi shiru Jim kad'an Rauda ta fito ta kalle Umma tace, "Yanzu bashi da lokaci yace amma zuwa dare bayan sallar i'sha zai jira ta. Bayan sallar i'sha ki dawo sai a had'a ki da wanda zai raka ki in hakan ta samu, in bata samu ba kuma abi wani sarkin" ta fad'a tana kallon Mama da kanta yake a sama amma tana jin me take cewa.

Mama ta juyo ta kalli Rauda suka had'a ido ta jijjiga kai ta had'd'iye yawu mai d'acin gaske kalaman Rauda na sukar ta a zuciyar ta amma duk da hakan babu abinda zata iya sabida halin da take ciki taimakon take so dole.

Umma tace, "Anjima in Allah ya kaimu zaku iya dawowa kamar yadda yace sai Rauda ta raka ku." Jakadiya tace, "Mun gode Allah ya bar zumunci." Umma tayi murmushi tace, "kar ki damu, ai mu zuciyar mu a wanke take tas da ruwan zamzam muna rama alkhairi ga sharri komai munin sa. Haka zalika muna rama alkhairi ga cuta komai yawan ta, haka zalika muna rama alkhairi ga cin zarafi komai d'acin sa. Mutane ne mu mun kuma san me muke yi muna taimakon kowa musamnan ma wanda ya kawo kansa" ta fad'a tana wani murmushi wanda kana kallon sa kasan akwai manufa a cikin sa.

Mama ta kalle ta har lokacin da murmushin akan fuskar ta sai ta sauke k'aramin numfashi ta tashi ta fita jakadiya ta rufa mata baya Suhaima ta matso cikin falon tace, "Mun gode sosai Mama, Allah ya saka da alkhairi. Amma kamar na sanki" ta fad'a tana juya kallon ta ga Rauda da take tsaye.

Rauda tayi murmushi tace, "Wataƙila mai kama dani kika sani bamu tab'a had'uwa ba." Suhaima ta tab'e baki ta d'aga kafad'a tace, "Maybe, sai anjima" tana fad'a ta juya ta fita.

     Rauda kamar tayi kuka ta kallo Umma tace, "Yanzu Umma wannan matar kika yiwa alfarmar ganin Baba malam? Kin manta abubuwan da suka faru ne a baya? Kin manta zagi da cin fuskar da tazo gidan nan tayi mana?, har sakawa tayi a kashe ni har cikin gidan nan amma shine zata zo da guntuwar izzar ta wai da niyar neman taimako kuma ayi mata?. Kina gani fa ko neman alfarmar ta kasa sabida a ganin ta fad'uwa ne kuma mu kamar masu jin tsoron ta sai mu taimaka mata?."

Umma ta kalli Rauda zatayi Magana Yaya Ummi tace, "Nima wallahi banji dad'in hakan ba, naso koda zamu taimake ta sai ta sauke izzar da take ji da ita ta rok'i alfarma da bakin ta in mun ga dama sai mu taimake ta. Kamar masu ji tsoron ta bata fad'i abu ba sai muyi mata." Umma ta kalle su tace, "to ku dake ni akwai ku wuce haushin ku." Jin hakan sai Rauda ta zauna tace, "ba batun duka Umma kawai dai bamu ji dad'i bane ba wallahi."

Umma tace, "meye danrangamin ki da ita Rauda? Ni in nice ke wallahi bazan nuna na santa bama balle na d'aga ido na kalle ta, in ma na nuna mata b'acin raina kenan na damu da d'anta ma. Ina izzar take? Ina mulkin yake? Ina sarautar take? Ina k'asaitar take? Ina ji da kan yake?. Har cikin falon nan tazo fa neman alfarma koda batayi magana ba ai munyi nasara a kanta tunda yadda muka ce sai ta tako tazo sai da tazo d'in rashin maganar ta ba wani abun bane ba. Kuma dan ka rama alkhairi ga sharri ai babban aiki kayi ko yanzu tasan muna da amfani gashi tazo neman alfarmar da ta rasa wanda zaiyi mata sai mu d'in dai da take ganin mu k'ask'antattu."

Rauda ta runtse idanun ta kafin tace, "Bata da kirki matar nan Umma. Ni ba ina magana akan saki ko wani abun ba; ki duba yadda tazo ta zauna kamar falon gidan su tana wani shan khamshi ita a lallai ga gimbiya maganar ma sai dai ayi mata."

Umma tayi murmushi tace, "Mun sani amma babu abinda zamu cewa d'anta, ya zama silar abubuwa da yawa cikin rayuwar mu baki d'aya, badan shi ba da yanzu muna neman gidan zama lokacin da aka zo rushe mana wannan gidan kodan shi mayi mata dan mu ba butulu bane ba."
Yaya Ummi tace, "Uhummm!." Alamun maganar bata wani ratsa taba kawai babu abinda suka isa su iya ne.

Umma tace, "An koya mana rama alkhairi ga wanda ya nufe ka da sharri tun a gidan mu, in badan haka ba shi kansa Baba malam din bazai saurare ta ba dan ke y'ar sace duk wanda ya tozarta ki shi ya tozarta. Ki shirya anjima suzo ki raka su." Rauda tayi wani irin juyi tace, "Umma wai da gaske ni zan rakata?" Ta fad'a tana zaro idanu waje. Umma tace, "Ke zaki rakata Rauda" ta fad'a tana shiga d'aki.
Rauda ma d'akin ta wuce tana ji a ranta ko za'a yi tashin hankali bazata raka Mama wajan Baba Malam ba sai dai duk abinda zai faru ya faru kawai.

        Yadda Rauda take jin zafi a ranta haka Mama ma a haka suka koma gida ji take inama tana da bindiga ta harbe kanta kawai ta huta da wulaƙancin da ta jawowa kanta, tunda suka koma take a zaune fad'i take, "Sadiya kin cuce ni, kin cuce ni Sadiya, kin yaudare ni kinyi amfani da yarda ta a gare ki kin ci amanata. Jira nake nayi setling komai zan dawo gare ki, sai kin yabawa aya zak'inta keda y'arki. Ta dalilin ki naje neman alfarma wajan k'ananu mutane, kaiiii!" Ta fad'a tana sake dafe kanta ji take kamar zai fashe sabida abinda take ji a cikin sa.

In badan neman taimako ba me zai kaita wajan su? Har su nemi fad'a mata magana sannan kuma suce wai ta dawo da daddare dan kawai sun raina mata hankali. Dogon tsaki taja ta tashi da sauri ta d'auki ruwan sanyi tana sha tana zubawa jikin ta dan ji take tiririn zuciyar ta na tab'a fatar ta.

D'akin da Hydar yake ta shiga ta same shi a yadda yake a kwance kamar gawa ta cize bakin ta tace, "Aliyu shine babba baya nan ko samun sa waya bana yi yanzu, Asad da nake da buri a kansa ya watsar dani an raba mu dashi dani da babu duka d'aya a wajan sa" ta matsa kusa da Hydar ta dafa kansa tace, "Hydar da yake taimaka min a ko wanne lokaci yake k'aunar ganin ya bani farin ciki shima gashi a kwance dashi da gawa duka d'aya.  Gaskiyar Hajiya ne da tace ina amfanin maza ukun da nake tak'ama dasu...? Tabbas babu amfani. Har gwara su masu mata da yawa dan da ace nice da matan dana tura su wani abun nayi wani abun, ko basuyi wani abun ba zasuyi shawara" ta fad'a hawaye na zubo mata daga idanun ta.

"Allah na roƙe ka ka bawa Hydar lafiya, ka dawo min da Aliyu gida ya bar banzayen dabi'un sa yayi hankali, ka karkato da hankali Asad kaina duk abinda aka yi masa ka karya shi ya Allah ka bashi ikon dawowa gare ni. Mijina ka bashi lafiya ka tashi k'afadunsa; tabbas da yana da lafiya abubuwa baza suyi min yawa haka ba, Allah ka dube ni badan halayya ta ba" ta fad'a tana kuka sosai mai tsuma zuciya nan take zazzaɓi ya rufar mata ta lallab'a ta fita ta koma d'aki tayi lamo akan gado bata da abokin shawara a kusa balle ta fad'a masa abinda yake zuciyar ta ko zata ji dad'i.

Idanun ta ta d'aga nan tayi k'aro da k'aton hoton su su uku ranar da Asad yayi shagalin nad'in sarautar sa yana tsakiya Hydar yana dama Aliyu yana haggu dukkan su sunyi murmushi ba sunyi bala'in kyau. Murmushin itama take tana hawaye zuciyar ta na azalzalzalar ta akan dole ma ta bazama nemawa y'ay'an ta magani koda zata rasa ranta.

    Ana idar da sallar i'sha Mama ta saka Suhaima a gaba sai wajan mota suka shiga aka tayar da motar zuwa gidan su Rauda. Motar na fita daga gate d'in farko kafin yaje na biyun wani dogari da yake tsaye ya d'auki waya ya shiga wani k'aramin d'aki da yake wajan ya danna wayar ya saka a kunne ya d'an yi jimm kafin yace, "Ranki ya dad'e an gama komai, nan da wasu mintina motar bazata sarrafu a hannun ta ba, zata kwace ni ta daki wani abun zasu mutu dukkan su."

Murmushi wacce ake yin wayar da ita tayi tace, "Godiya nake, zaka ga kud'in ka kamar yadda nace maka." Yayi murmushi yace, "Nima godiya nake ranki ya dad'e." Ya yanke wayar yana dariya yace, "Kodan wulaƙancin matar nan ai nayi abinda zata mutu, bata d'auki kowa da daraja ba gwara ta mutu ma huta da k'yara da hantara."
Chapter 71 · 0% Book details