Sashe 78
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kuyi hak'uri hanya ce ta bi dani sai na shiga" ta furta tana goge idanunta. Baba ya sauke numfashi yace, "to jeki ciki Allah ya jiqan rai, amma ko dan gaba kar ki sake aikata abinda kika yi kinji ko?." Ta d'aga kai alamun to ta mik'e tana jan k'afar ta ta shiga ciki ta kulle kanta a d'aki ta cillar da mayafin jikinta ta cillar da wayar ta cire doguwar rigar ta watsar tayi zaman dirshan a k'asa ta fashe da sabon kuka mai tsuma zuciya.
Had'a kai tayi fa guiwa ta cure waje d'aya tana furta, "Ka cuce ni, ka gama da rayuwata, ban tab'a aikata sabon Allah ba sai yau, me nayi maka kayi min wannan hukuncin? Me na aikata maka ka zab'i ka lalata min rayuwa...?" Ta sake fashewa da kuka tana jin yadda zazzaɓi ya rufe jikinta gabad'aya.
Tunawa da tayi bata da tsarki sannan kuma batayi sallah ba sai ta mik'e dak'yar dan gabad'aya jikinta ciwo yake mata sosai ta shiga band'aki, ruwan band'akin yayi sanyi da yawa amma bazata iya fitowa tace zata dafa ba kar su zargi wani abun haka tayi amfani dana sanyin duk da zazzaɓin da da yake jikinta.
Doguwar rigar da skin tried d'in da komai da ta cire ta cure su ta saka a leda bayan ta fito ta cusa can k'arshen wardrobe dan har abada bazata sake amfani dasu ba ta tsane su, _Meye na tsanar kaya Rauda bayan fatar jikin ki da ita aka aikata zinar?._ kalaman da suka zo ranta kenan ta buga kanta a jikin kwabar tana jin zafi a zuciyar ta sanyi yana ratsa jikinta.
A haka ta daure ta saka kaya ta kalli gabas da niyar tayar da sallah sai take jin kunyar mahaliccin ta zuciyar ta na rawa a haka tayi sallar magriba tayi i'sha ta tayar da shafa'i da wutri ta kwanta a kan sallayar ta cure a cikin hijjabi tana jan numfashi. Buga k'ofar ake yi ta d'ago ta kalli k'ofar ta mik'e dakyar ta k'arasa ta buɗe k'ofar Ummulkhairi tace, "Anty Umma tace kizo kici abinci." Rauda tace, "na k'oshi, ki karb'o min maganin ciwon kai" ta fad'a tana komawa ta zauna a gefen gado.
Ba jimawa Ummulkhairi ta dawo da p.c.m ta bata had'e da ruwan pure water ta bata tasha ta koma kan gadon tayi lamooo hawaye na sauka ta gefen idanun ta. "Rauda!." Jin muryar Umma a kanta sai ta firgita abinka da mara gaskiya ta kalle ta tace, "Na'am." Umma tace, "meya same ki?." Rauda murya na rawa tace, "Zazzaɓi ne Umma shima kuma kukan da nayi a gidan su Farida ne." Umma ta k'arewa fuskar ta kallo sannan tace, "Kin tabbata?." Rauda ta d'aga kai alamun eh.
Hannu Umma takai ta tab'a wuyan ta taji zafi sosai tace, "Jikin ki akwai zafi sosai kin sha maganin?." Ta d'aga kai alamun eh Umma tace, "dukkan mai rai mamaci ne ai nima wata rana haka za'a fitar da gawata dole kuma kiyi hak'uri." Rauda ta sunkuyar da kanta k'asa tana jan numfashi.
Umma ta sake kallon ta tace, "Amma d'azu da kika gifta ni naji sabon khamshin turare a jikin ki wanda ban sanki dashi ba, yana da khamshi luma yana da k'arfi har yanzu ina jin tashin sa a jikin ki a ina kika same shi? Ko duk a gidan mutuwar kika shafa?."
Rauda ta rud'e ta gigice ta ta mik'e zaune tana waige-waige bakin ta yana rawa gashi Umman ta zuba mata ido alamun tuhuma ita kuma alamum rashin gaskiya ya bayyana a tare da ita, Umma tace, "Ya naga kin rud'e kamar mara gaskiya ne?, ko wani ne ya baki turaren?." Sai Umma ta kai fuskar ta wuyan Rauda ta d'ago tace, "Akwai khamshin sa sosai a wuyan ki, waye ya baki kika saka bayan fitar ki?."
Rauda ta sosa kanta idanu na zubar da kwallah murya na rawa tace, "gidan....Yaya Ummi."
"Ita ya baki ki shafa?." Rauda ta d'aga kai alamun eh, Umma tace, "To yayi kyau, kwanta Allah ya k'ara lafiya. Amma ki daina kukan in kina so kanki ya daina ciwo" tana fad'a ta fice Rauda ta koma da baya ta kwanta ta sake fashewa da kuka.
Bata tab'a yiwa iyayen ta k'arya gashi a akan Asad ta fara, taya baza ta tsane shi tsana ta har abada ba? Ai ya gama cutar ta sai dai Allah yayi mata sakayya ranar alqiyama. Da wannan tunanin ta kwanta lamoo tana share hawaye ciwon kan yana raguwa a hankali, smun sassaucin ciwon kan sai bacci ya kwashe ta.
*☆☆☆.*
Jidda ce zaune cikin d'akin ta waya rik'e a hannun ta fuskar ta da gwada alamun damuwa k'arara a kai tace, "Mum wallahi yau gabad'aya fa tsoro ya bani, ya canja daga daren jiya zuwa yau d'in nan, zancen da nake miki ko tun d'azu ya fita har yanzu bai dawo ba gashi dare yayi, kuma shi kad'ai ya fita dan baza ma ka gane shi ba in ka ganshi." Mum tace, "Uwar sa ta dage ai lallai sai ta dawo dashi yadda yake a baya, amma kin san me za'ayi?."
Jidda tace, "A'a Mum."
"Za'a sake sabunta aikin da akayi ne da alama ya fara lalacewa sai mun kuma yin sabo."
"Mum kika ce za'a kasheta, ai gwara a kashe d'in kawai a huta kinga da duk ba haka ba da bata raye."
"Na gwada hakan yafi sau biyar amma babu nasara, amma za'a sake gwadawa a karo na shida."
"Mum nidai ayi abinda za'ayi kar a raba ni dashi."
Mum tace, "karfa ki damu tunda ina raye ai zance ya k'are, zan turo Eman yanzu ta kawo miki wani magani ki tabbatar ya kwanta dake yau bayan kin sha wannan maganin zai mana amfani sosai." Jidda tace, "toh Mum zanyi." Tana fad'ar hakan ta yanke wayar Jidda ta sauke numfashi tana kallon wayar zuciyar ta a cushe, burin ta kar a raba ta da Asad gashi an d'auko hanya shiyasa duk sai ta tsorata a iya yau kawai.
Suhaima da take tsaye a k'ofar d'akin Jidda taji komai hannunta toshe da bakin ta take girgiza kai ta koma da baya a guje zuwa b'angaren Mama, da bak'i ta tarar da Mama hakan ya saka ta wuce d'aki tana ta zagaye burin ta bak'in su tafi duk minti biyu sai ta lekoo falon amma suna nan.
Bak'in suna tafiya Mama Jamila k'anwar Mama ta shigo Mama ta kalle ta tace, "Jamy kina son tafiyar dare ke kam." Tayi dariya ta zauna tana fad'in, "tun d'azu fa muka zo mun sauka a guest house ne mun huta sai yanzu na fito. Barka da dare Mama."
Mama tace, "Barkan ki, ya hanya?."
"Alhamdulillah."
"Ya kika baro mutanen Kano?."
"Suna lafiya Mama, ina Suhaima?." Suhaima da dama jira take ta fito a gigice tana fad'in, "Mama!." Mama ta kalle ta tace, "lafiya?."
Suhaima tace, "Naje apartment d'in Jidda naji tana waya tana cewa za'a sake sabunta aiki wanda aka yiwa Yaya Asad ya fara barin jikin sa, kuma wai gwara kawai a kashe ki in ba haka ba zaki sake lalata komai. Mama ina jin muryar Mum tana cewa ta saka a kashe ki har sau biyar babu nasara."
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!" Suka furta a tare suna mik'ewa tsaye Mama Jamila tace, "Suhaima kin tabbatar da abinda kike fad'a gaskiya ne?." Suhaima tace, "wallahi da gaske nake small Mama, abinda naji tana cewa kenan." Mama Jamila tace, "kinji ko? Na jima da sanin Sadiya da y'arta amanar ki suke ci gashi yunk'urin kashe ki ma suke yi. Yanzu mr gari ya waya Maman Suhaima?."
Mama kuwa tayi cak ta kasa cewa komai jikinta yayi sanyi ta sulale ta zauna akan kujera tayi tagumi da hannun ta duka biyun ta kulle idanun ta fuskar Mum tana gilma mata. Small Mama tace, "Bafa shiru zakiyi ba mataki za'a d'auka tunda Allah ya tona mata asiri dole tayi prison."
Mama dai bata iya cewa komai ba tayi shiru da alama ta rasa ma abinda zata ce small Mama ta durk'usa a kusa da ita tace, "Maman Suhaima kallona zakiyi wannan tagumin babu abinda zai haifar miki sai zallar damuwa, ki bari muje muci ubanta sannan mu saka a kulle ta bata fimu da komai ba."
"Jamy komai ya faru nice na jawo, nice na jawo komai Jamy, Da ban bata k'ofa ba da duk hakan bata kasance ba. Na fifita sama ta da kowa ko ku bana d'aukar shawarar ku kamar yadda nake d'aukar tata. Duk da karfafa zumuncin mu na had'a d'ana da y'arta na tsallake duka y'ay'an ku na raba shi da wacce yake so na bashi wacce nake so. Hasbunallahu wani'imal wakil" Mama ta furta tana tashi tsaye.
Small Mama tace, "Wacce yake so kika saka ya sake ta ita kuma wacce kike so yace bazai yi ba." Mama ta girgiza kai tace, "Jamy ku k'yale ta in sha Allah bazata ga fad'uwa ta ba" tana fad'a ta shiga d'aki Jamila ta bita rai a b'ace domin bata ga dalilin da zai saka a k'yale wacce take son kashe ta.
Tana shiga d'aki ta biyo bayan ta tace, "Akan me za'a k'yale ta? Kenan in ta kashe ki shikenan taci riba?." Mama tace, "bamu da hujja Jamy, dan Allah ku bani waje ina so na huta." Ba musu ta fita tana k'wafa ranta duk ya b'aci matuk'a.
Bayan kamar awa biyu Suhaima ta shiga wajan Mama ta ganta a zaune batayi magana ba sai ta fita zuwa kitchen ta had'o mata shayi mai zafi dan tasan bata ci komai ba ta tawo kawo mata.
Hydar ta samu a wajanta ta zauna tace, "Allah yaja da ran Mamana, baki ci komai ba tun safe ki daure kisha tea d'in nan ko zaki ji dad'i." Hydar ya karb'i cup d'in yace, "Mama dan Allah kisha." Ta yamutsa fuska tace, "Hydar bana so."
"Please Mahhh!" Ya furta a sanyaye yana kallon ta ta mik'a hannu ta karb'a ta rik'e a hannunta amma bata sha ba.