← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 131

Sashe 97

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rauda tace, "Kiyi hak'uri Umma."
"Ba laifi kikayi min ba Rauda, nasan duk abinda ya faru k'addara ce daga Allah amma duk mahaifin ki shine sila." Rauda tayi shiru har Umma ta kai k'arshe sai ta rik'e hannun Umma ta d'ora a kan k'irjin ta tace, "Umma kullum ji nake zuciyata kamar zata fashe, Umma a kullum bana tunanin in na kwanta zan tashi da raina sabida a yanayin da nake kwanciya bana tunanin zan iya tashi. Umma in na tuna Allah ya isar ki a kaina sai nayi dama na mutu na huta" ta fad'a tana fashewa da kuka ta d'ora kanta a cinyar Umma.

Umma ta sauke numfashi tace, "Ki cigaba da hak'uri komai yana gab da zuwa k'arshe in sha Allah. Rayuwar ki tana cikin rud'ani na sani amma haka Allah yaso jarabawa ce Allah ya baki ikon cinyewa Rauda." Kuka take a cinyar Umma sosai sai da tayi mai isar ta sannan ta tashi Umma ta lalaba ta ta kwanta a akan gadon badan tana jin bacci ba.

*☆☆☆*

"Mum me za'a yi da akace ana kiran meeting? Nidai gaskiya bazan je ba sai daku kuje keda daddy" Jidda ta fad'a a rud'e tana kallon Mum. Mum tace, "Dole kuwa kije domin akan ki maganar take ba'a kaina ba, mahaifin ki baya nan dole nida ke d'in zamu je."

Jidda ta girgiza kai tace, "Nidai bazan je ba Mum, bazan iya zuwa ba tsoro nake ji kar muje an gano komai."
"Nima kaina tsoron nake ji Jidda amma ya zama dole muje in bamu je ba shima wata matsalar ce, zuciyata bugawa take yi sosai ban san me zan tarar a goben ba."

Jidda ta fashe da kuka tace, "Nidai Mum bazan je ba zan iya mutuwa in akace sai naje, bazani ba." Mum binta take da kallo ganin yadda ta tsorata sosai kamar ita tayi wani babban laifin tace, "Jidda ni ya kamata naji tsoro bake ba, amma sai naga kin fini ma jin tsoron. Wannan yanayin naki yana sakawa na sake jin tsoro domin ban san me kika aikata ba."

Jidda kawai ta tashi ta fita dan babu wanda zai saka ta tafiya gobe bazata je asirin ta ya tonu ta shiga uku ba gwara koma meye zai faru ya faru a bayan idanun ta ba a gaban idanun ta.

*☆☆*

        "Dole a san abinda za'ayi bana son Abba ya kai gobe da ransa ya zama dole na tabbatar ya koma rashin lafiya ko kuma ya mutu gabad'aya" ya fad'a yana hakki cikin tashin hankalin daya bayyana a tare dashi zuciyar sa har bugawa take yi sabida rud'ani da tashin hankalin zuciyar sa. Kamar an tsikare shi sai ta mik'e ya lek'a taga yaga dare ya fara mutanen gidan suna ta raguwa ya kalli d'akin Hydar ya tabbatar yana ciki ya sauke ajiyar zuciya yana sake girgiza kansa.

Komawa yayi ya zauna yana girgiza k'afa tare da cize baki yana ji kamar ya jawo dare yayi sosai yaje ya aiwatar da abinda yake so ya aiwatar. Yana nan zaune k'arfe d'aya na dare ta buga ya zabura ya mik'e ya fita daga falon kai tsaye b'angaren mai martaba ya nufa ba tsoro a tare dashi balle fargaba.

Masu tsaron k'ofar duk sunyi bacci ya shiga falon ya jishi shiru an kashe komai na falon baka ganni koda hannun ka sabida duhu, da yake ya haddace komai hatta hanyar da take falon ya haddace ta a haka ta k'arasa har k'ofar d'akin mahaifin nasa.

Tunanin bud'e k'ofar yake dan yasan tabbas in ya bud'e zai iya ji gashi shi kuma baya son b'ata lokaci. "Sai me ma dan ya ganni? Mtsww" ya fad'a a bayyane yana jan tsaki ya tura k'ofar d'akin cikin dakewar zuciya da son idda nufin sa akan mahaifin nasa kai tsaye.

Hasken a.c kawai ake gani a d'akin ya nufi kan gadon kai tsaye duk da baya gani sosai amma ya tabbatar da yana kwance a kan gadon a wannan lokacjn. Zagayawa yayi ta gefe ya d'auki pillow da yake gefe a ajjiye ya nufi inda yake hango tudun Abba daidai inda yasa kansa yaje ya danna pillow a kai da niyar toshe masa numfashi da k'arfin gaske.

Ba zato babu tsammani yaga haske ya gauraye d'akin ya firgita matuk'a ya d'ago kai a firgice yana kallon inda switch d'in fitilun yake don ganin wanda ya shigo a lokacin da bai shiryawa hakan ba.
[17/12, 10:42 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*077*

           A tsaye yaga mai martaba hannun sa hard'e a k'irji yana kallon sa fuskar sa da murmushi da alama baiyi mamaki ko al'ajabi da ganin abinda yake shirin faruwa ba yasan daman hakan zata kasance, bai san pillow hannun sa ya sub'uce ba yayi baya kamar zai fad'i idanun sa kyam akan na mahaifin sa tashin hankalin da ya bayyana a tare dashi ba d'an kad'an bane ba.

Murmushi mai martaba yayi ganin yadda ya firgice sai ya tako a hankali yazo inda yake yace, "Gani gaka zaka iya kashe ni in kana so." Baya yayi ya nisanta kansa daga kusa dashi jikin sa yayi bala'in yin sanyi duk ya dabarbace alamun rashin gaskiya amma babu alamun nadama ko kunya a tare dashi.
Murmushi yayi ya sake cewa, "Kana tunanin ban san waye kai ba? Ko ina tunanin duk abinda yake faruwa a gidan nan ban sani bane ba?. In hakan kake tunani ka d'auka kayi babban kuskure duk abinda kuke aikatawa a tafin hannuna yake kuma k'arshen ku yazo ka tabbatar da komai ya kusa zuwar muku k'arshe."

Zuciya ce take d'aukar sa akan kawai ya shak'e mai martaba ya huta in ba haka ba gobe zata zamar masa barazana ga rayuwar sa gabad'aya in ba kashe shi yayi ba hankalin sa bazai tab'a kwanciya ba, hannu biyu ya d'ago da niyar kaisu wuyan mai martaba sai kuma suka had'a ido ya fasa mai martaba ya sake yin murmushi yace, "Kashe ni mana ya zaka fasa?."

"Ba kai kad'ai kake son kashe ni ba a yau kuna da yawa wanda basa so gobe tayi, baku san me zan tattauna a  goben ba amma dukkan ku hankalin ku ya tashi kun manta da karin maganar da bahaushe yake cewa rana dubu ta b'arawo rana d'aya tak ta mai kaya. Dubun ku ta cika gobe lokacin girbar abinda aka shuka ne."

Kamar wanda aka yiwa allura ya zabura ya kama wuyan mai martaba da k'arfin gaske ya matse yana fad'in, "Bazan iya bari ka kai gobe ba koda nima bazan kai ba, gwara na kashe ka in yaso nima a kashe ni" ya fad'a yana sake matse masa wuya da k'arfi.

Shigowa d'akin akayi aka kwace mai martaba daga hannun sa Uncle ya tsinka masa mari ya sake marin sa ya bishi da kallon b'acin rai yana fad'in, "Ban tab'a d'auka rashin hankalin naka har ya kai haka ba sai yanzu, duk abinda ka aikata baya bai ishe ka ba sai ka had'a da kashe mahaifin ka."

Mai martaba ya zauna gefen gado yana tari kad'an yace, "Mubarak kaje dashi a killace shi a wani wajan bana so ya gudu daga gidan nan, kuje a tabbatar an saka masa matakan tsoro yadda ya kamata." Da k'arfi Uncle ya jashi yak'i tafiya ganin hakan Galadima shima jashi suka fita dashi dak'yar.

Mai martaba ya bisu da kallo bayan sun fita ya shafa wuyan sa hankalin sa ya tashi sosai zuciyar sa tayi rauni dan bai d'auka duk zafin kansa zai iya k'okarin kashe shi ba idon sa yana cikin nasa ba, ya d'auka zai tsaya yi a bayan idanun sa amma bai d'auka yana kallon sa shima yana kallon sa zai iya kashe shi ba. Ya sauke numfashi a bayyane yace, "Me ake da irin wannan haihuwar?."

      Ba jimawa Uncle ya dawo ya k'araso wajan Mai martaba yana fad'in, "Ranka ya dad'e babu abinda ya faru dai ko?." Mai martaba yace, "Babu abinda ya faru, ina kuka ajjiye shi?."
"Yana d'akin cikin b'angaren nan yanzu haka Galadima yana wajan sa an masa d'auri mai kyau. Mai martaba zufa yake a kunna a.c" ya fad'a yana d'aukar remote zai danna yayi saurin dakatar dashi ta hanyar fad'in,

"Kar ka kunna, yanzun nan na kashe ta akwai wanda suka zuba guba a cikin ta da zarar na shak'a zan mutu kamar yadda akayi a wancan lokacin." Uncle yace, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, mutane me suke nema a duniya suka mayar da kashe musulmi ba komai ba?. Jinin ka shine yake son ganin bayan ka a koda yaushe meyasa duniya ta koma mai amana kad'an ne?." Mai martaba yace, "Dukkan su basa so na kai gobe dalilin da ya saka hakan kenan, suna nan da yawa domin ba mutum d'aya bane dukka kuma na san su d'aya bayan d'aya."

Kai ya girgiza yace, "Ai gwara Allah ya tona asirin su kodan suji kunyar duniya su kuma jira jin ta lahira." Mai martaba yace, "Kaje ka huta Allah ya kaimu goben."
"Bazan iya tafiya na bar mai martaba a a wannan yanayin ba."
"Kar ka damu jeka" ba musu Uncle ya fita ya kulle masa k'ofa zuciyar sa babu dad'i.

Washe gari.

          "Rauda wai meye haka ne? Amma kin san dai na fad'a miki mai martaba shine yace yana neman mu ko?" Umma ta fad'a tana kallon Rauda da take a zaune a gefe. Rauda ta kalli Umma da jajayen idanun ta kamar ko yaushe tace, "To Umma me zanje nayi a can?."

"Tunda ya neme ki me zai hana baza muje ba kika san abinda ya faru?." Rauda tayi shiru tace, "Umma gabad'ayan iyalan gidan su bana son ganin su duka, sun yi min mugun tabo a rayuwata bana son sake had'a ido da ko wanne su."

Umma ta kalle ta tace, "Na sani Rauda duk abinda ya faru ai babu wanda ban sani ba, tun shigowar iyalan gidan su rayuwar ki komai yake lalacewa amma Allah ne ya rubuta hakan kuma shine zai gyara komai ai." Sunkuyawa tayi tana kuka Umma taga shatin dukan da tasha a hannu Baba a kwance a bayan ta sai jikinta yayi sanyi ta sauke numfashi tana kallon ta.
Chapter 97 · 0% Book details