Sashe 73
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk da yanayin da Mama take ciki tana shiga b'angaren ta wajan Hydar ta shiga ta same shi yadda ta barshi ta d'auko ruwan rubutun da malam yace a gidan shafa masa a fuska da tafin k'afa dana hannu ta shafa tana yi tana cize bakin ta sabida ciwon da jikin ta yake mata. Sai da ta tabbatar tayi komai yadda akace sannan ta shiga d'akin ta tayi wanka da ruwan zafi bayan ta shirya tana zaune a d'aki Suhaima ta shigo da sallama ta amsa ta k'araso ta zauna a k'asan ta tace, "Mama nifa tunani nake kwance min burkin mota akayi, na tura mechanic yaje a d'auke ta ya duba ta a yanzu ya tabbatar da kwance Birkin aka aka juyar da sitiyarin yadda bazai sarrafu ba."
Mama tayi cak ta kalli Suhaima tace, "Kenan so akayi a kashe mu?." Suhaima ta d'aga kai mama ta sauke numfashi ta dafe fuska da duka hannayen ta biyu ita gabad'aya abubuwan nan sun fara fin k'arfin tunanin ta gab kwakwalwar ta take da daina aiki indai aka cigaba da tafiya a haka zuciyar ta ma zata iya bugawa ta mutu kowa ma ya huta Suhaima tace, "Waye zai turo a kashe ki? Su waye meye kuma dalilin su?." Shiru Mama bata amsa ba Suhaima ta kuma cewa, "Badan waccen yarinyar ba da yanzu bak'in labari ya gama karad'e masarautar nan, dole mu sake taka tsan-tsan da kowa Mama, yanzu kinga mu kad'ai ne daga ni sai ke bamu da mai taimaka mana" ta fad'a a sanyaye tana kallon Maman nata.
Da hannu Mama tayi mata alama da ta bata waje ta tashi ta fita Mama ta bud'e fuskar ta tana so ta tuna waye zai bada wannan d'anyen aikin a aikata mata amma kanta ya cushe gabad'aya tama rasa wanda zaizo ranta. _Duk musulmi na gari ceton rai shine aikin sa ba d'aukar rai ba._ kalaman Rauda suka dawo mata zuciyar ta ta daki goshin ta a bayyane tace, "Kaiiii! Meyasa haka yake faruwa dani..?" Ta fad'a tana yin baya ta kwanta a kan gadon tana ji kamar tayi hauka.
Kamar wacce aka yiwa allura sai kuma ta mik'e ta ta d'auki ledar da ta shigo da ita ta fita zuwa b'angaren mai martaba, yana kwance shi kad'ai idanun sa a bud'e da alama ba bacci yake ba ta d'auko maganin da aka bayar nasa tana shafawa masa tana kuka tana fad'in, "Mijina suna so su kashe ni, mijina haukata ni suke so suyi ban san me nayi musu ba. Dan Allah ka tashi ka taimaka min abubuwa sun yi min yawa suna neman fin k'arfin tunani na, kaine garkuwa ta a koda yaushe ka tashi ka taimaki matar ka mai rauni" ta fad'a tana hawaye tana zuba masa ruwan rubutun a bakin sa.
Haka ta dinga soki burutsu a wajan sa kamar kanta ya kwance kafin ta koma b'angaren ta tana ji kamar ta kashe kanta ma kowa ya huta.
*☆* B'angaren Rauda lokacin da ta shiga gida dukkan su zaman jiran dawowar ta suke yi yadda ta shigo tana d'ingishi hankalin kowa sai ya tashi Umma tayo wajan ta tana fad'in, "Rauda lafiya? Meya same ki?." Rauda ta fara kuka tace, "Umma ba kun amince da ita kun barni mun fita tare ba...? Da yadda kuke zaunen nan sai dai kuji labarin mutuwa ta."
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, wani abun ta kuma yi miki? Ba'a son raina kika bita ba bazan ja da umarnin mahaifin ki ba Rauda ba yadda zan iya. Meya same ki?." Baba da ya shigo yace, "meya faru?." Rauda tace, "Hatsari mukayi."
"Hasbunallahu wani'imal wakil!, hatsari..? A ina?" Umma ta fad'a a gigice tana kallon ta.
"A kan hanyar mu ta dawowa, motar ce tak'i tsayawa sai bud'ewa mukayi tana tafiya muka fita shine na buge da dutse a bayana" ta fad'a tana yamutsa fuska kamar zatayi kuka.
Umma tace, "Wannan mata dai zuwan ta bai tab'a zamar mana alkhairi ba, tunda iyalan ta da ita kanta suka shigo rayuwar mu shikenan komai yake canjawa. Shine kuma suka barki kika tawo ko a kaiki asibiti a duba ki?. Su suna ina?." Rauda tace, "ban sani ba a wajan na barsu kawai nayi tawowa ta. Umma bayana" ta fad'a tana cize bakin ta domin ciwo yake yi mata ba kad'an ba.
Rik'e ta Umma tayi tace, "Malam ya kamata muje asibiti a duba mana ita tunda su da suka fita da ita bata da matsayin da zasu kaita asibiti." Baba yayi shiru kawai baice komai ba dan yasan laifin sane da baice taje ba da hakan bata faru ba. Baba ya fita jim kad'an sai gashi ya dawo yace, "Kuzo muje."
Tare suka fito wanda yake jan napep d'in Baba suka gani suka shiga zuwa asibiti na kusa, kasancewar private ne ba jama'a nan da nan aka dubata aka bata magani nasha dana shafawa dan itama buguwa ce kawai ba wani abun ba, Baba zai biya kuɗi kenan sai ga Anas a wajan ya kalli Baba yace, "Baba." Baba ya kalle shi yace, "A'a Anas." Ya duk'a ya gaishe shi kafin yace, "Waye babu lafiya a daren nan?." Baba yace, "Rauda ce ta samu k'aramin hatsari, amma Alhamdulillah komai yazo da sauk'i buguwa tayi a bayan ta kawai."
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, yaushe Baba?" Ya tambaya a gigice yana kallon Baba. Baba yace, "kwantar da hankalin ka, d'azu ne kuma da sauk'i dan yanzu dana biya kud'in nan ma tare zamu koma." Anas ya karb'i takardar yace, "Baba ka koma ka zauna zan gama komai." Baba yaji sanyi a ransa dan Allah ya sani baya son fitar da kud'i dan babu yadda zaiyi ne yasan shine yaja yace, "Ayi haka Anas?." Yayi murmushi kawai ya k'arasa inda ake biyan kud'in Baba kuma ya koma da baya zuciyar sa fes.
Bayan ya biya kud'in aka siyi magani Umma suka fito da Rauda Anas ya gaida Umma ta amsa Raudan ta gaishe shi ya amsa yace, "Ya jikin naki?."
"Da sauk'i, maganin da suka bani nasha naji dad'in." Kallon da yake mata ya saka ta k'in had'a ido dashi murya a tausahe yace, "Sannu." A tare suka fito harabar asibitin Anas yace, "ku tsaya Umma bara na kawo motar nan."
Baba yace, "Ai da adaidaita sahu muke." Anas yace, "bara na sallame shi sai mu tafi tare." K'arasawa inda motar sa take yayi ya bawa mai adaidaita sahun kud'i yace ya tafi ya shiga mota ya kawo ta inda suke tsaye Baba ya shiga gaba suka shiga baya suka tafi gida. A k'ofar gidan suka tsaya suka fito Baba yace, "Allah yayi albarka Anas, mun gode." Murmushi yayi kawai suka shiga gida yabi Rauda da kallo har ta shige ya sauke ajiyar zuciya Allah ya sani yana son Rauda da wannan tunanin ya shiga mota ya tafi.
*Bayan wasu kwanaki.*
An shiga watan Ramadan an fita an shiga na sallah, tuni an saka ranar auren Rauda da Anas ya rage saura sati hud'u kacal ana ta shirye-shirye daman akwai kayan ta duk da aka siya lokacin auren ta da Asad k'arawa kawai akeyi tunda Allah ya rufa asiri yanzu. Amarya Rauda tana ta karb'ar gyara daga wajan yayyen ta kai da ka ganta kasan ta kusa zama amarya khamshin da yake fita a jikinta kad'ai zai tabbatar da hakan. A cikin satin za'a kawo lefe can gidan su angon ma shirye-shirye ake sosai bikin Babban d'a ba wasa bane.
A bangaren gidan sarauta babu abinda ya canja anyi shagalin sallah yadda ya kamata mai martaba sarki Asad yayi hawan sallah fiye da wanda akayi a baya, yasha ado ya kashe kud'i dan dawakin da aka hau ma daga Germany aka zo dasu.
Mama har lokacin bata kai matsayin da Asad zai zo inda take ba har gwara ma yanzu ya kan lek'a wajan ta ya gaishe ta amma bata san komai ba duk abinda zai faru sai dai ta gani kawai ya faru amma bata san anyi ba. Kullum Mama cikin shan maganin hawan jini take domin ya riga yayi mata illa dole sai da suka d'orata akan magani. Mama ta rame tayi bak'i abubuwa sun tarar mata iskanci kala-kala jidda take shinfid'a mata musamman yanzu da cikin Jidda ya tasa kana iya ganin sa a cikin riga sai iskanci yayi gaba dalilin samuwar ciwon ta kenan.
Hydar ya warke ya cigaba da kula da mai martaba wanda ake samun cigaba a rashin lafiyar sa dan a yanzu yana motsawa sosai sai dai baya magana har lokacin kuma baya tashi.
Aliyu kuwa har lokacin babu labarin sa tun ana samun a sa waya yanzu ta kai ta kawo an daina samun sa a waya har Maman ta gaji ma ta daina gwada kiran nasa, tayi addu'a a watan azumin da ya wuce taje umra zuciyar ta tana fad'a mata Allah ya masa dukkan abinda ta rok'a sai dai ta jira sakamako.
*☆☆*
"Nifa na kasa gane abubuwan nan da suke faruwa, tun kwanakin baya kace min zaka san yadda za'ayi da Asad za'a haukatar dashi ya dawo daga England lafiya lau ya cigaba da mulkin sa babu abinda ya canja har kawo yanzu saima cigaba da yake samu. Kace min bazai tab'a iya haihuwa ba yanzu ga matar sa da ciki har ya fito ana ganin sa. Abu biyu ka fad'a ka cika shine b'atar da Aliyu da kuma gurb'acewar raywuar Rabi'atu bayan wannan shiru har yanzu ni na gaji. Kaida mastar d'in kun kasa komai lokaci yana ta tafiya da zarar yarinyar nan ta haihu shikenan abu ya sake dawowa baya" Hajiya ta fad'a tana kallon waziri da yake zaune.
Yace, "kwantar da hankalin ki ni kaina nasan an d'auki lokaci amma me kika ce a maganar ki? Abubuwa biyu sun tabbata sauran ma zasu tabbata ne."
"Yaushe? Kusan shekara ana abu d'aya ace har yanzu an kasa cimma komai."
"Zamu cimma daman dole sai munyi hak'uri, in kuka tuna waye Asad ta b'angaren addini dole sai mun sha wahala. Suhail da muka tura shi jikin sa matar Asad bata yadda dashi ba tana k'okarin raba su ne kin san yanzu sai abinda tace shine nak'asun da muka fara samu tun farko."