← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 131

Sashe 36

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hydar yace, "haka ne. Baza'a rasa ba dan akwai wanda da dama hukuncin da ya yanke bai musu dad'i ba, to amma Allah yaja da ranka waye ko wace? Me suka aikata lokaci d'aya yayi tasiri haka?."

Mai martaba yayi shiru yana tunanin Hydar ya katse masa tunani yace, "Ko akwai wanda mai martaba yake zargi?."
"Tabbas akwai wad'anda zuciyata take zargi, bana so zargin nawa yayi nisa a kansu ne amma zan fad'ad'a bincike."

Hydar yace, "Allah ya bada iko ya bayyana mana koma su waye suke da hannu a wannan ciwon nasa na farar d'aya."
"Amin Hydar. Ka cigaba da kula dashi zan zo in sha Allah." Daga nan sukayi sallama da Hydar ya kashe wayar.

         K'arfe shida na safe motar su Mama ta sauka a Tafawa b'alewa international Airport driver da ya kawo su ya juya ita da Suhaima suka shiga cikin Airport suna jiran jirgi domin k'arfe bakwai jirgin su zai d'aga zuwa Cairo. Suna nan zaune aka sanar da zuwan jirgi suka fita suka hau motar da zata kai su bakin jirgi, hankalin Mama bai kwanta ba sai da taji jirgi ya tashi ya lula sama ya d'auki hanyar k'asar Egypt sannan ta sauke ajiyar zuciya mai k'arfi.

Awa biyar da y'an kaine suka kai Mama da Suhaima Cairo suka sauka daga jirgin a lokacin k'arfe d'aya na rana ta take sosai suka shiga mota direct suka nufi Four Seasons hotel ko hotel d'in su basu wuce ba kai tsaye inda Asad yake ta nufa.

       A cikin hotel d'in Rauda na zaune a d'aki kamar ko yaushe tana waya da y'an gidan su tana ware kayan da suka siyo a daren jiya tana zubawa a jaka, katse wayar tayi bayan sun gama wayar ta kalli jakar tace, "kai tama yi kad'an ashe." Wata jar doguwar riga ce ta d'auki hankalin ta ta d'auka tana d'agawa sama tace, "rigar nan fa tayi kyau sosai, bara na gwada na gani" ta fad'a tana zame ta jikin ta ta saka jar ta d'aura d'ankwalin irin d'aurin nan mai v ta ta gaba gashin gaban kanta ya fito ta waje.

"Kai amma tayi min kyau sosai" ta fad'a tana sake kallon kanta tana murmushi. Sai kuma ta tsaya cak tana kallon kanta har lokacin tace, "ko ina yake?." Bata da amsa ta jiyo motsi a falon ta bar kayan ta fito daga d'akin tana kallon fallon yana nan yadda yake jiya decoration d'in wajan kamar an sake sabunta shi.

Wajan taga ya kuma burgeta tana nan tsaye taji sautin Camera alamun ana d'aukar ta hoto, juyawa tayi ta kalle shi yana zaune akan kujera da cup d'in lemo a hannun sa yana sha fuskar sa babu walwala amma kuma yana d'aukar ta hoto. Murmushi tayi ta sunkuyar da kai k'asa ya ajjiye kofin ya taso ya k'araso zuwa gare ta ya rik'e hannun ta duka biyun yana jin bugun zuciyar sa a bayyane yace, "you look so beautiful." Murmushi ta kuma yi fuskar sa tana nan yadda take bata canja ba ya d'ago da kanta yana kallon idanun ta kafin ta sake sauke kanta k'asa.

Yana so ya fad'a mata abinda ya same shi amma bai san ta inda zai fara ba domin shi ya gama amince mata bashi da abinda zai b'oye mata a duniya kuma ya kamata ace ta sani amma ya rasa ta inda zai fara cewa ga abinda ya same shi, yayi shiru na wani yana kallonta yana kuma rike da hannunta zoben da ya bata ya sake haska hannun sosai.

Kallon sa tayi tace, "kayi min alƙawarin baza ka barni ba ko?." Ta d'ago ta kalle shi nan take taji gaban ta ya fad'i ya d'aga kai alamun eh tace, "dan Allah ka sake maimaitawa ina so na sake tabbatarwa." Numfashi ya sauke yayi shiru na wani lokaci kamar bazai magana ba har lokacin bai cika hannun ta ba sai daga baya yace, "ni Asad bin Nasir bin Sa'ad na yiwa matata Rauda alƙawarin bazan tab'a rabuwa da ita ba, duk wahala duk dad'i duk tsanani ina tare da ita" ya fad'a yana lumshe idanun sa a kan fuskar ta.

Rauda ta sunkuyar da kai tana murmushi ta d'ago idanun ta suka ciko da hawaye tace, "Na amince. Amma meyasa nake jin zuciyata tana rawa akan hakan? Sai naji kamar akwai abinda zai faru wanda zai raba ni dakai" ta fad'a k'irjin sa tana kuka tace, "Ina jin tsoro sosai, bana so a raba mu na saba dakai na fara sonka bana so son ya zamar min cuta nan gaba."

Hannu ya saka ya zagayo dashi a jikinta ya rik'e ta sosai yana jin kukanta a k'irjin sa yana bubbuga bayanta a hankali amma baiyi magana ba, sun shima a haka kafin yace, "Ki daina kuka, Asad bazai barki ba kin zama shi ya zama ke babu abinda zai raba ki dashi dan yana sonki. Ki daina kuka bana son jin kina kuka" ya fad'a muryar sa na rawa kansa na ciwo sosai.

D'agowa tayi ta kalle shi ta goge idanunta ya rik'e fuskar ta yana kallon idanunta yace, "Smile." Murmushin tayi duk da akwai hawaye a idanunta shima yayi murmushin yana girgiza mata. "Ya jikin ka?." Ya juya idanu ya kalle ta sai kuma ya kalli gefe ya sake kallon ta sai ya fasa maganar da zai fada ya rik'e hannunta suka je suka zauna.

"Wacce country kike son kije?" Ya fad'a yana kallonta. Ta sake yin dariya tace, "Suna da yawa." Da hannu mata alamun yana ji tace, "Saudia, America, England kai nifa ko ina ma ina so naje, especially Dubai ma kodan na shiga national world Quran competition." Kai ya girgiza jin dad'in abinda take so ta shiga d'in amma baice komai ba.

Kallon kanta yayi yace, "Zaki je saloon anjima kar kanki yayi ciwo" ya fad'a yana kallon gashin kanta da yake a tsefe. Murmushi tayi tana kallon zoben hannunta tace, "tohm." Hannun sa ta kalla babu agogo taga wannan zanen yana nan ta shafa zanen tace, "Ga shaida ta." Murmushi yayi ya kalli zanen ya kalle ta yace, "As my wife bazaki iya gane ni ba sai da sign?." Ta turo baki gaba tace, "Kuna da rikitarwa ne, kace fa Mama ma bata gane ku wani lokacin." Murmushi kawai yayi baice komai ba ya mayar da hankalin sa kan t.v.

Zata kuma magana kenan aka danna door bell hakan ya dakatar da ita daga maganar kafin ya mike ya k'arasa kusa da k'ofar ya cire lock yaja handle d'in k'ofar ya bud'e. Wara idanu waje yayi ganin wanda suke tsaye ido cikin ido yake kallon su zuciyar sa na bugawa fat, fat, fat ya kasa furta komai sai kallo ya kasa furta komai.

"Matsa min na wuce" Mama ta fad'a tana rab'a shi ta shiga ciki Suhaima ta biyo bayan ta. Had'a ido sukayi da Rauda gaban Rauda yayi mugun fad'uwa ta tsorata sosai har tsoron ya bayyana a fuskar ta taja baya tana cigaba da kallon Mama. Mama k'arewa falon kallo take tana girgiza kai gabanta na fad'uwa matuk'a ganin irin adon da yasha irin na gidan larabawa da India ne musamman lokacin da suke cikin nishad'in son kasancewa da iyalan su.

"Mamana!" Asad ya furta with full love emotion yana k'araso da sauri yayi hugging d'in ta very tight. Hugging nasa back tayi tana jin sanyi da kwanciyar hankali na ratsa ta zuciyar ta na dawowa bugu daidai domin tunda Asad ya bar k'asar bata kuma jin zuciyar ta na bugawa daidai ba sai yanzu.

Sakin ta yayi ta kalli face d'in sa tace, "Kar ka damu nazo gare ka tunda kai an hana ka zuwa inda nake" ta fad'a tana kallon Rauda da take wajan a tsaye kamar an dasa ta kanta a sunkuye. Dawo da kallon ta tayi gare shi tace, "Nasan raba mu akayi dakai shiyasa baka nema na bayin kanka bane aikin wannan bak'ar ashanar ne" ta fad'a tana nuna Rauda.

Suhaima da take ta kallon falon tace, "Wow wajan nan ya had'u ya kuma tsaru sosai, Oga Deaf waye yayi planing wajan nan haka?." Kallon Suhaima yayi sai kuma ya kalli Mama gaban sa na fad'uwa matuk'a yaga Mama ta isa kusa da Rauda babu b'ata lokaci ta tsinke ta da mari.

Da hanzari Asad ya k'arasa wajan yana kallon Maman ya kalli Rauda da hannun ta yake kuncin ta hawaye yana sakko mata idanunta a kulle tace, "Y'ar talakawa, mayya mai zubin mayu dangin mayu. Duk irin kashedin da nayi miki akan Asad baki ji ba sai da kika san yadda kikayi kika asirce min shi aka cuce shi aka aura masa ke kuka tawo nan. Gashi nan naga har canjawa kinyi anzo k'asar waje ana cin abinda ake so ke ga mai wayo ko?. Nafi k'arfin dangin ki ma gabad'aya balle ke y'ar k'aramar alhaki." Motsi Rauda batayi ba balle ta amsa hawaye ne yake zuba a idanun ta jikin ta yayi sanyi sosai tana ji a jikinta akwai abinda zai faru a wannan lokacin.

"Kin raba ni dashi baya nema na baya min waya duk a tunanin ki kinyi nasara a kaina har abadah kamar yadda kika ce, to baki isa ba yarinya wanda ya riga ka kwana sai ya riga ka tashi baki isa kiyi nasara a kaina ba daidai da rana d'aya. In ma rik'e masa kurwa kikayi yau zaki sake shi domin banga abin so a jikin ba har da zai maqale miki, kin samu riba ai tunda gashi har kina taka k'afar ki tafiya tayi miki kyau. Anyi aure ban sani ba yanzu kuma na sani za kuma a warware shi."

Asad ta kalla gaban sa ya fad'i ya saukar da ido k'asa zuciyar sa na rawa burin sa kar ta furta abinda zuciyar sa take aiyanawa domin bai san ya zaiyi ba, "Asad!." Jin yadda ta kira shi ya saka ya kalle ta da girmamawa yace, "Mama."
"Wacece ni a wajan ka?." Kansa na k'asa yace, "mahaifiyata."
"Na isa da kai ko a'a?."
"Mamana itace isa da kanta."
Chapter 36 · 0% Book details