← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 131

Sashe 6

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rauda ta wara idanu tace, "Baba auren sa daidai yake da rasa rayuwa ta."
"Nasan daman tsoron da kike ji kenan ai shiyasa kika ce bakya son sa, ki kwantar da hankalin ki a ko ina Allah yana tare da mai gaskiya, Allah bazai bari ya cutar dake ba tunda baki hakkin komai." Rauda tace, "Duk da haka Baba ni bai min ba."
"Daman ai basai yayi miki ba tunda shi kinyi masa ai zance ya k'are. Zancen yayi miki ai bai tashi ba tunda shi har ya ganki yace yana so shikenan." Umma da take sauraren su ta kasa jurewa tace, "Auren dole kenan zakayi mata?."

Baba ya kalli jama'ar falon yaga har su Khalil suna wajan sai ya fasa fad'ar abinda yayi niya ya tashi yana kallon su yace, "Kowa ya tashi yaje yayi sallah" yana fad'a ya fita daga falon bai kuma cewa komai ba.

Babu wanda ya kuma magana aka tashi aka tafi sallah bayan sun idar da sallar i'sha a d'aki Rauda ta kalli Umma da take kan sallaya tace, "Umma kenan Baba auren dole zaiyi min?" Ta fad'a idanun ta na kawo ruwa zatayi kuka.
"Babu batun auren dole tunda kince bakya so auren nan baza'a yi sa ba, abu mai sauk'i ne naje har fada na nemi ganin martaban na fad'a masa halin da ake ciki ai ina da k'afar zuwa, dan san abin duniyan mahaifin ki tsaf zai aurar musu dake."

Rauda tayi shiru tana tunani tace, "Ina jin yawan fad'uwar gaba tsakanin kwanakin nan Umma." Umma tace, "Ai dole kiji fad'uwar gaba, har gida fa akazo za'a kashe ki in baki ji fad'uwar gaba ba ai baza kiji dad'i a zuciyar ki ba."

Shiru Raudan tayi ganin kamar ta shiga damuwa ya saka Umma tace, "Ki kwantar da hankalin ki kome kika ga ya faru Allah ya rubuta faruwar sa tun farko, ki nutsu ki ta addu'a Allah zai kawo miki mafita." Kai kawai ta d'aga jikin ta a sanyaye Umma ta fita daga d'akin ita kuma ta samu ta lallab'a tayi sallah raka'a biyu ta karanta addu'ar da manzon Allah S.A.W ya bayar ta istikhara kana ta tashi ta kwanta badan tana jin bacci ba.

Da safe jiki a sanyaye ta tashi sabida mafarkin da tayi wai ana bikin su da Asad shi da ita sai kuka suke amma da an gansu anga yanayin amarya da ango, gamsuwa take ji a zuciyar ta da gangar jikin ta na Asad shine mijin ta amma ta k'i barin hakan yayi tasiri a jikin ta sai kawar da tunanin take yi a dole baza ta bari yayi tasiri ba sai hakan ya haifar mata da sanyin jiki. Ko abinci bata iya ci ba tana zaune a d'akin tayi uban tagumi dana sanin ma yin istikhara take yi da tasan abinda zata gani kenan ko abinda zata ji a jikin ta kenan da bata yi ba.

Tana nan zaune Umma ta shigo ganin yanayin ta ya saka tace, "Ke kuma lafiya kike ko lek'owa bakiyi ba?." Numfashi ta sauke kana tace, "Umma mafarki nayi." Umma ta zauna kusa da ita tace, "Mafarki kikayi kin auri Asad ko?."

Rauda ta kalli Umma da mamaki kafin tace, "Umma ya akayi kika sani?." Umma ta dafa ta tace, "Nima nayi Rauda. A daren jiya ban kwanta ba sai da nayi ta addu'a akan nema miki zab'in Allah, na kuma rok'i Allah da ya nuna min zab'in da yayi miki ko a mafarki ne. cikin ikon Allah sai Allah y nuna min Asad shine mijin ki duk da mafarki ba gaskiya bane amma yana kasancewa wani lokacin Rauda. bazan ja da ikon Allah ba addu'ar kuma da nayi Annabin mune ya koyar damu ita sai nake ji a jikina yanzu na gamsu da auren ki dashi."
Rauda ta rausayar da kai kana tace, "Umma akwai tarin abubuwa a gaba wanda shekaru na sunyi kad'an na fuskance su, ki duba ikirarin mahaifiyar sa a kaina, bana son auren nan ko kad'an Umma."

"To Rauda nidai ban san me zance ba amma mu barwa Allah zab'i kawai, in ya zab'a miki shi ki saka a ranki shine alkhairin, in kuma akasin haka ya faru ki saka a ranki ba alkhairi bane ba. Ki tashi kizo ki karya" ta fad'a tana fita daga d'akin ta bar Rauda cikin zurfin tunani.

*☆☆*

A babbar fadar Katagum bayan sallar juma'a aka d'aura auren Asad da Rauda a kan sadaki naira dubu d'ari lakadan ba ajalan ba, babu mutane sosai daga mai martaba da Liman sai Wambai da abokan sa sai kuma Baba da k'annen Baba harda y'an uwan Umman Rauda sai kuma Hydar. Asad bai san me yake faruwa ba tunda yayi sallah ya fita daga gidan dan gabad'aya baya jin dad'in zaman gidan ko kad'an bai tsaya ba balle yasan abinda yake faruwa.

A wannan lokacin suka samu labarin rasuwar Sarkin Kano mahaifin Mama, Asad yana zaune a guest house ya kashe wayar sa gudun kar a dame shi bai ma san me yake faruwa ba. Tv da take a kunne ana haska labarai itace ta sanar dashi rasuwar kakan nasa ba shiri ya taso ya dawo gida ya tarar dasu Hydar suna niyar tafiya dole shima ya shiga cikin su akayi tafiyar dashi.

Da yake tafiyar mota ce basu isa ba sai bayan la'asar lokacin ana ta k'okarin tafiya kai shi makwancin sa an so a jira zuwa safiya sabida wanda basu iso ba amma ya'yan sa sunce suna so ya shiga a juma'ar kodan albarkar ta dole aka hanzarta komai aka tafi kai shi. Jana'izar ta had'a manyan mutane da mayan sarakuna da y'an siyasa kowa ka gani yana wane wannan, wannan yana na fika wannan ma yana nima na fika.

Basu samu ganin Mama ba sai bayan sallar i'sha suka shiga cikin gidan aka nemo musu ita idanu sunja sabida kuka. Mai martaba sarkin Katagum ya mata gaisuwa y'ay'an ta ma suka yi mata gaisuwar rashin mahaifin ta da addu'a kafin Mai martaba yace, "ina babu damuwa a turo sauran muyi musu gaisuwa." Kai kawai Mama ta d'aga kafin ta tashi ta fita jim kad'an sai gata da y'an uwan ta mata suka gaisa sukayi musu gaisuwa kafin su tafi masaukin su.

A Bristol hotel suka suka mai martaba yana zaune a personal room d'insa shi kad'ai su Asad da sauran makarraban sa kowa yana wajan da zai kwanta. Abinci aka kawo kamar ba'a so sabida yawa sa aka bawa kowa yaci ya k'oshi banda mai martaba dan su ba abincin kowa suke ci ba musmaman ma in yasan an san da zuwan sa kamar abincin dan shi akayi.

A b'angaren Baba lokacin da ya bar wajan d'aurin auren bai koma gida har yaji labarin rasuwar yasan bai da k'afar zuwa da babu abinda zai hana shi zuwa yiwa sirikar sa gaisuwa ba to yana gudun abinda zai je yazo. Lokacin da ya koma gida suna zaune gabad'ayan su har y'ay'an da suke gidan mijin su sunzo ya shigo da sallama yana cewa, "yawon ku yayi yawa fa yaushe kuka zo harda zaku kuma dawowa yau?." Dariya sukayi dukkan su kafin su gaishe shi ya amsa kana yace, "nama ji dad'i dana ganku gabad'ayan ku." Umma ya mik'awa ledar hannun sa ta karb'a yace, "kud'in hannun ki kud'i ne na kayan lefe, da kud'in na gani ina so na y'ar ki Rauda."

Gaban Umma ya fad'i ta kalli kud'in da tarin yawa ta kalle shi ta kalli Rauda da tayi sak tana kallon sa tace, "Malam ban gane ba." Baba yace, "Zaki gane yanzu ai" ya fad'a yana sake d'auko kud'i a aljihun sa ya mik'awa Rauda ganin tana kallon sa ya saka yace, "karb'i mana." Ba musu ta karb'a hannun ta na rawa yace, "Sadakin ki kenan jama'a sun shaida d'aurin auren ki da Asad ga goro da alewa" ya Fad'a yana fito dasu daga aljihun sa.

Dammmmm k'irjin su ya buga ta kalli Baba da sauri ta kalli kud'in ta kalli Umma da take kallon sa itama ta kalli y'an uwan ta kafin tace, "Aure kuma Baba!?." Baba yace, "Eh aure Rauda. D'azun nan aka d'aura auren ku a fada ba'a masallaci akayi ba shiyasa baizo kunnen ki ba." Rauda tayi sak ta kasa furta komai sai Umma ce tace, "Malam wai da gaske ko wasa?."
"Na tab'a yi muku irin wannan wasan ne?." Inna tace, "Yau dai ka fara Malam." Ya kalle ta yace, "ba wasa nake ba da gaske nake, da waliyan ta duka akayi d'aurin auren har da yayyen ki ma suma sun shaida" ya fad'a yana kallon Umma.

Ganin sun kasa magana ya saka ya kalle su yace, "kud'in hannun ki kuyi mata siyayyar kaya dan tafiyar su Misra baza ta wuce wannan satin ba, ayi siyayya yadda ya kamata duk abinda zata buk'ata a siya ragowar kud'in kuma suna hannuna za'a yi wani abun dasu. Ke Rauda bani na hannun ki" ya fad'a yana mik'a mata hannu jikin ta duk ya saki ta mik'a masa ya saka a aljihu yana murmushi yace, "to ai kin gani, ana so a bawa yarinya sadakin auren ta a hannun ta shiyasa na baki, yanzu kuma za'ayi wata hidimar dasu."

Yaya Ummi tace, "Baba dan Allah da gaske yanzu Rauda ta zama matar Asad halak malak?."
"Mtswww! Wai makaryaci kuka mayar dani ne ko me?."
"A'a Baba abin ne muka ji shi kamar a mafarki."
"To kuji shi kamar gaske domin Rauda matar Asad ce a yanzu, wacce take ganin k'arya nake ta kira kawun ta ta tambaya" yana fad'ar hakan ya tashi ya fita yana tsaki.
Chapter 6 · 0% Book details