← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 131

Sashe 82

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Na amince ranka ya dad'e, na amince wallahi zanyi." Ya girgiza yace, "Nawa ta biya ki?." Jikin ta rawa yake da hannu yyi mata alama da tayi magana tace, "dubu dari."
Ya d'aure fuska tamau yace, "Akan dubu d'ari kika so kashe mana uwa?." Kuka take yi sosai tace, "Ban san na kisa bane, ban san kashe ta za'ayi ba wallahi."

"K'arya kike Ladidi zan k'yale ki ne kawai. Zan ninka miki abinda ta baki sau goma matuk'ar kika yi abinda nace."
"Ko baka bani komai bama zanyi ranka ya dad'e." Ya kwanta a jikin kujerar yace, "Kiyi abinda nace in naga yanayin aikin naki sai muga abinda zai faru" da hannu yayi mata alama da ta tashi ta bashi waje ta mik'e tana godiya sosai.

       Bayan fitar ta ya tashi ya nufi d'akin sa har zai shiga sai ya fasa ya nufi k'ofar d'akin Asad ya murd'a handle d'in ya jishi a buɗe, "A'a bro yau kuma d'akin deaf zaka shiga?" Hydar ya fad'a daga bayan sa ya juyo ya kalle shi ya d'aga kai yana tura k'ofar d'akin yana kallon d'akin yace, "nasa zan dawo tunda ya wuce matsayin wannan yanzu."

Hydar yayi murmushi yace,  "Yadda kake so, but akwai kayan sa da littafan sa a ciki" yana fad'a ya shiga nasa d'akin Aliyu ya shiga d'akin ya turo k'ofar yana kallon d'akin yana tab'e bakin sa kamar yaga kashi.

Yana nan a gyare sai y'ar k'ura da yayi kad'an gadon a d'ame da alama babu wanda yake zama a cikin d'akin. Kamar an bashi umarni ya d'aga katifar gadon nan yayi karo da k'atuwar laya wacce bai tab'a ganin irin ta ba da wani bak'in gashi a nannad'e a jikinta ya saki katifar yana kallon layar.

A gefe ya ajjiye ya koma ya buɗe kayan Asad yana kallon su a shirye sama da kala hamsin har sunyi k'ura sabida ba'a tab'a su. Murmushi yayi ya girgiza kai yace, "Allah sarki Deaf, dole abubuwa su canja" ya fad'a yana zura hannun sa can k'arshen wardrobe d'in ya zaro wata layar ya had'a da waccan ya jefa a drawer ya shiga band'aki domin bazai zauna da layoyi a d'akin ba dan shi yasan inda suke.

A nan yayi wankan sa ya shirya tsaf da kayan Asad ya tsaya yana kallon sa a madubi yayi murmushi ya shafa gemu yace, "Like deaf." Murmushi ya sake yi domin shi kad'ai yasan abinda yake shiryawa a zuciyar sa, bayan Allah da ya halicce shi babu wanda ya isa ya gano shirin sa sai shi kawai ya fita daga d'akin.

*☆☆☆*

          "Ke Rauda tashi mana, wannan wanne irin bacci ne haka har azahar tayi baki tashi ba ko jikin ne?" Umma ta fad'a tana tashin ta daga bacci Rauda ta mik'e tana rausayar da kai Umma ta tab'a wuyan ta tace, "jikin ki babu zafi, tashi kiyi wanka kici abinci kiyi sallah bacci ciwo zai k'ara miki." Kai ta d'aga ta ziro k'afafun ta k'asa ta sakko daga kan gadon tana niyar mik'ewa sai tace, "Washh bayana."

Umma ta kalle ta tace, "meya samu bayan naki? Naga tun asuba kina rik'e bayan ki." Rauda tace, "Haka nan ya rik'e min" ta fad'a tana shiga band'aki sai kuma ta fito tace, "Bara na d'ora ruwan wanka babu mai zafi." Umma tace, "Zauna a kawo miki." Ba musu ta zauna tayi tagumi Umma ta fita ba jimawa da kanta ta shigo mata da ruwa a bokiti bata k'arasa band'akin ba ta ajjiye mata bata ce komai ba ta juya.

Tashi Rauda tayi ta d'auki ruwan ta shiga band'akin tayi wanka tare da alwala tazo ta tayar da sallar azahar, bayan ta idar tayi tagumi abinda ya faru da ita jiya yana yi mata yawo ba kamar irin kalaman da taji yana fad'a mata a lokacin da suke tsaka da sab'on Allah nan take tsigar jikinta ta tashi sai hawaye tayi saurin gogewa ta kwantar da kanta a guiwar ta.

       Gudun kar Umma ta sake yi mata magana ta gano wani abun sai ta mik'e ta fito ta samu tasha tea kawai bata iya cin komai ba Rahma tazo suna hira da Umma ita kam bata saka musu baki tayi shiru tana kallon waje daya. Yaya Ummi ce ta shigo tana fad'in, "mara lafiya kin tashi ashe?." Ta daga kai tace, "Yaushe kika shigo?."
"Kina bacci, ya jikin?."
"Da sauk'i, Ina wuni."
"Lafiya lau, Allah ya k'ara lafiya."
"Amin Yaya."

Umma ta kalli Yaya Ummi tace, "Jiya wanne turare kika bata ta shafa mai d'aukar hankali haka?." Gaban Rauda ya fad'i ta kalli Yaya Ummi suka had'a ido ganin yadda ta rud'e lokaci guda sai Yaya Ummi ta d'auki haske tace, "Sabo ne,  Abban su Islam ya kawo min shine ta d'auka ta saka."

Umma tace, "Tunda ke ya bawa bai kamata ki bata ba, yana da dad'in khamshi sosai amma matsayin ta na wacce bata da aure bai cancanci ta shafa shi ta fita ba, yana da k'arfi d'azu ma naji khamshin sa a jikinta ya rik'e fatar ta sosai, ki kiyaye koda nan gaba kema kuma kar ki saka ki fita waje" Umma tana fad'a ta mik'e ta fita daga falon Yaya Ummi ta kalle ta tace,

"Tunda naga kina raba ido nasan baki da gaskiya, ke ina kika sami turaren?." Rauda tayi shiru ta rasa abinda zatace sai Yaya Ummi tace, "tambayar ki nake yi." Rauda tace, "a gidan su k'awata Farida ne na ganshi sai kawai yayi min dad'i na shafa, kin san in na cewa Umma haka fad'a zatayi min shiyasa nace a gidan ki na samu."

Yaya Ummi tace, "Munafuka" ta fad'a tana yar dariya tana ta janta da hira ita dai bata iya bata amsa da ta kulle idonta abinda ya faru take hangowa duk ta koma wani iri lokaci d'aya.

      Bayan la'asar Anas yazo bata so ma fita ba suka tilasta mata dole taje inda yake kamar ko yaushe yana zaune ta shiga ta zauna da sallama ya amsa ya kalle ta yace, "Amarya ta meya same ki haka kika rame a fuska?" Ya fad'a cikin kalar tausayi yana kallon ta.

Murmushin yak'e tayi tace, "Ina wuni." Jin muryar ta na rawa sai yace, "Taya zan wuni lafiya bayan kina kwance ke baki da lafiya? Ji yadda maganar ki take shaking fa."
"Zazzaɓi ne da ciwon kai shima naji sauk'i."
"Anje asibiti?."
"Basai anje bafa naji sauk'i."

Yayi shiru yana kallon ta sai yaga kawai tana kuka hankalin sa ya tashi sosai ya matso kusa da ita yana fad'in, "Haba Rauda ya kike so nayi ne? Kukan na meye kuma?."
"Kayi hak'uri!" ta fad'a murya na rawa sosai tana kuka. Hankalin sa ya tashi babban tashin hankalin sa bai wuce ace za'a raba su ba yace, "hak'urin na meye Rauda bayan ni ya kamata na baki hak'uri nayi miki laifi jiya? Hak'urin me zanyi? Ki sanar dani dan Allah kin saka min tsoro a zuciyata."

Kai take girgizawa tana kuka duk ya rud'e hankalin sa ya tashi yana ta bata baki amma bata daina zubar da hawaye ba, wani yana bin wani haka take kukan hawaye na zuba sosai sun k'i tsayawa, jin bazata iya jurewa ba sai kawai ta mik'e tayi cikin gida a guje ta barshi a tsaye yana binta da kallo gaban sa yana fad'uwa.
[17/12, 10:41 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*067.*

          A guje ta shige su a falo zuwa d'aki ta fad'a kan gado tana kuka har suna jiyo gunjin kukan ta daga d'akin. Umma tayi murmushi tace, "Wai ka haifi yaro yace zai maka yawo, tun jiyan nasan akwai wani abun da yake damunta a zuciyar ta tana b'oyewa dan bata so mu sani." Yaya Ummi ta tashi ta bita d'akin lokacin tana fad'in, "Na tsani rayuwata bana son rayuwata, Allah ka aiko da mala'ikan mutuwa ya d'auki raina na mutu na huta da wannan bala'in da nake ciki."

"Ban tab'a dauka ilimin ki ba bashi da amfani ba sai yau Rauda, da bakin ki kike wannan addu'ar bayan kin san yinta babu kyau?." Rauda jin muryar Yaya Ummi ya saka tace, "Yaya ya zanyi? Ji nake zuciyata kamar zata fashe na rasa wanne kalar tunani ma zanyi."  Yaya Ummi ta zauna a kusa da ita tace, "Fad'a min me yake damun ki? Wani abun Anas d'in yayi miki kike yiwa kanki wannan fatan?."

Rauda ta fara jan numfashi alamun wacce taci kuka ta k'oshi Yaya Ummi tace, "Fad'a min mana meya faru, in baza ki iya sanar da Umma ba ni zaki iya fad'a min." Kallon fuskar Yaya Ummi take yi tana hawaye amma ta kasa cewa komai, taya zata iya fad'a mata ta aikata zina da tsohon mijinta? Taya zata iya ce mata tarbiyyar ta ta shekara ashirin da biyar ta watse a daren jiya? Ta zata ce mata ta aikata babban laifi a cikin mayan laifukan da Allah subahanahu wata'ala yayi hani da kusantar su duniya da lahira?. Ina baza ta iya ba gwara ta cigaba da barin sa a ranta koda zata mutu.

Yaya Ummi ta tab'a ta tace, "Sanar dani ina jinki." Ta sunkuyar da kai tace, "ni tunda naga jiya babar su Farida ta rasu daga shiga d'aki bata sake fitowa ba sai gawar ta shikenan nake jin komai ya yatsa min cak Yaya, hatta auren sai naji bana so wallahi" ta fad'a tana sake fashewa da kuka.

Yaya Ummi tace, "Bayan shi akwai wani abun a ranki, me Anas yayi miki?." Rauda ta girgiza kai tace, "Wallahi bai min komai ba Yaya, abinda na fad'a miki shine a raina kawai."
"Shine kike yiwa kanki wannan fatan?."
"Yaya Ummi ji nake inda Ummana ce ta rasu haka jiya a ina zan saka Raina? Wanne irin hali zan shiga?, tuna hakan shine yake sakawa naji komai ya fita daga raina Yaya."
Chapter 82 · 0% Book details