Sashe 4
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da sauri tayi hugging d'in sa cikin jin dad'i tace, "Na amince Asad, na amince, Allah ya maka albarka." Numfashi ya sauke ya kalli Hydar da yake gefen sa yace, "Amin Mamana, zan iya hak'ura da komai akan farin cikin mahaifiyata." Ta bar jikin sa tana murmushi tana kallon sa sai ya murmusa kad'an yace, "Lokacin Hutum mama ne ko zata iya hutawa?" ya fad'a yana kallon ta fuska a sake.
Kai ta girgiza ta juya tana tafiya kafin ta juyo ta kalle shi tace, "Kar ka canja abinda kace Asad, nasan ka baka sab'a alqawari ka tabbatar da maganar ka." Kai ya girgiza mata alamun to kafin ta shiga ciki shi kuma ya mik'e ya wuce ya bar Hydar a tsaye kafin ya biyo bayan sa.
Gidan tsitt sai sautin tsuntsaye da yake tashi a gidan da motsin dokuna da kukan dawisu suka wuce zuwa apartment d'in su, a bud'e suka same shi hakan ya tabbatar musu da Aliyu yana nan basu bi ta kansa ba Asad ya shiga d'aki Hydar yabi bayan sa yace, "Me ka aikata?." Ya juyo ya kalle shi amma bai tanka masa ba Hydar yace, "meyasa kace ka barta Asad? Ka manta itace wacce kake so kake burin aure meyasa zaka ce ka fasa?. Indai zaka biyewa Mama baza ka tab'a samun abinda kake so ba a duniya."
"Hydar ban tab'a ce maka ina so na aure ta ba, then zan iya barin kome nake so akan Mama u know dis."
Hydar zaiyi magana yace, "Hydar zan barta kodan ta tsira da rayuwar ta akan ina sonta bazan bari ta rasa rayuwarta sabida ni ba,kana jin mai Mama tace a kanta why zan saka rayuwar ta cikin hatsari sabida ni?, indai da gaske ina sonta Hydar barin ta shine abinda yafi min alkhairi" ya fad'a yana jawo drawer ya d'auko passports d'insu Rauda yace, "Please a siyo min ticket ina so ayi mata aikin nan immediately" yana fad'a ya shiga toilet bai kuma kallon Hydar ba.
Hydar ya fita jikin sa a sanyaye yana girgiza kai domin yasan daman Mama zata iya galaaba akan Asad amma ya kuma ci alwashin matuk'ar yana raye Asad bazai rasa Rauda ba sai ya mallake ta tunda yana sonta.
Asad kuwa bayan ya kwanta duk sai yaji ya kasa nutsuwa maganar Umman Rauda da maganar Mama nayi masa yawo a cikin kansa sun hana shi sukuni gabad'aya, bai tabbatar haka yake son Rauda ba sai a lokacin da ya furta zai barta nan yake jin wani abu na tasowa daga zuciyar sa yana taruwa a idanun sa da tsakiyar kansa ya cure waje d'aya.
Bai san haka yake k'aunar ta ba sai yanzu da ya barta, bai san haka ta mamaye ko ina na jikin sa cikin lokaci kad'an ba sai yanzu da ya furta ya barta bai san soyayyar ta tayi masa mugun kamu ba sai yanzu da ya barta. Ya zama dole ya hak'ura kodan mugun nufin Mama a kanta tsaf zata iya sakawa a kashe ta tunda bata sonta, hak'ura da ita shine yafi masa alkhairi tunda bazai iya jurar ta rasa ranta ba.
Numfashi ya fesar ya juya ya kwanta yana jin zuciyar sa na bugawa ya runtse idanun sa yana jin zafi tun daga cikin kansa har cikin idanun sa yake jin yaji da rad'ad'i na shiga cikin su zuciyar sa kuwa kamar zata fashe a wannan lokacin.
[17/12, 10:39 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*028.*
Har safiya Rauda bata dawo daidai ba idanun ta har lokacin akwai ja sosai a idon ta har lokacin wuyan ta ciwo yake mata ga shatar igiya nan a ciki kuma ji take kamar an rik'e mata mak'ogwaro, firgici da tsoro da fargabar jiya bata sake ta ba sukuku take ko magana ta kasa sai binsu da ido kawai da take yi kamar wacce aljanu suka shafa, bata tab'a tunanin tsintar kanta a cikin makamancin wannan yanayi ba shiyasa take yin komai a sanyaye. Dukkun su suna d'akin da take har su Inna an kawo mata shayi mai madara da biredi mai yanka-yanka tana ci a hankali.
Yaya Ummi ce ta shigo da Yaya Shamsiyya da babbar Yayar su wacce suke kira Yayar mu suka shigo a tare kamar gida d'aya suke, Umma ta amsa sallamar ta kalle su tace, "Kamar a gida d'aya kuke?." Dariya Yaya Ummi tayi tace, "a tare duka muka sauka daga mota kamar had'in baki. Ina kwana Inna, Umma ina kwana" ta fad'a a tare tana kallon su. A tare suka amsa suma suka gaishe su kafin Yaya Shamsiyya tace, "ita kuma me ya same ta haka?." Rahma tace, "Bari Yaya Shamsiyya jiya shigowa akayi da daddare za'a kashe ta."
Yayar mu tace, "Kamar ya za'a kashe ta kamar a film?." Rahma tace, "wallahi da gaske muke badan Allah ya tak'aita ba da yanzu sai dai kuzo jana'iza domin har sun shak'e ta; kalli wuyan ta ma zaki ga shatar igiya."
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" suka fad'a a tare suna yo inda Rauda take zaune tana shan tea a hankali.
Yaya Shamsiyya tace, "Su waye su d'in to? Me tayi musu? Ya akayi shigo gidan nan?." Umma tace, "turo su akayi su kashe ta tun kafin mu kulle gidan suka shigo aka kulle dasu, badan Allah ya kiyaye ba da yanzu wata k'ila an kaita kushewa."
Yayar mu tace, "To wa Rauda take dashi da zai turo a kashe ta?, bama y'an fashi bane ba kenan turo su akayi kawai dan suga bayan ta, waye ya turo ita da ba y'ar siyasa ba?. Amma dai an kama su ko?." Yaya Ummi tace, "Abinda yake raina kenan; wa Rauda take dashi mak'iyi da zai nemi kashe ta har haka? Me take dashi a duniya?." Umma ta tabe baki tace, "hmmm badai d'an sarkin Katagum ya furta zai aure ta ba; kar ku manta kuma shine mai jiran gado ko yanzu mahaifin sa zai iya murabus ya bashi sarauta shiyasa aka fara neman rayuwar ta sabida kawai ya furta ita yake so."
Yaya Shamsiyya tace, "ikon Allah sai kallo, daga cewa kana so sai a fara yunk'urin kisa? Sai kace wacce d'an sarki Saudia yace yana so. Banda abinda akaje har gida aka yi muku?." Umma tace, "to ina dalili auren sa da gafara zai saka ayi mana ba? Ko gafarar ubangiji zaka samu ta hanyar auren sai kayi addu'a Allah ya kawo maka wata hanyar a bar wannan, yaje ya nemi daidai shi amma banda Rauda baza mu zuba ido a kashe ta a banza ba."
Yayar mu tace, "wallahi fa, ina dalili daga zancen ana so sai a fara maganar kisa? Me yayi zafi shi ba wuta ba. Sannu Rauda Allah ya saka miki." Suka amsa da amin kafin Rahma tace, "Kuma abin haushi ma ko Yayar mu har yanzu babu wata maganar kirki da ta shiga tsakanin sa da ita, k'asaita da sarauta yake ji da ita ya kasa bata lokacin sa balle su fahimci juna." Umma ta sake cewa, "Wallahi shiyasa ban amince da soyayyar da yace yana yi mata ba ko kad'an, ni zuciyata fad'a min take akwai manufar da yasa yake sonta amma ba dan Allah ba."
Yaya Shamsiyya tace, "Babu lallai kuma Umma shi had'uwar jini haka yake wanda baka d'auka zai saurare ka ba in Allah ya had'a jinin ku babu wanda zai ji yana so sai kai. Ita duniya ai haka take daidan wani karkataccen wani." Umma ta kawar da kai tace, "Kayya dai Shamsiyya." Yaya Ummi tace, "To me Baba yace?."
"Me zai ce kuwa? Shi har yanzu bai saduda ba yana kan bakar sa ta aura masa Rauda sabida wani abun ya rufe masa ido baya ganin aibun hakan. Nidai na fad'a masa Rauda bazata aure shi ba." Shiru suka yi kowa yana juya abin a ransa daga baya aka cigaba da tattaunawa a kan maganar.
Da misalin k'arfe sha biyu na safe Walida da Habiba suka kawowa Rauda ziyara lokacin ta d'an ware ba laifi ana hira da ita, ita kad'ai ce a d'akin suka shiga Habiba tana yi mata jinjina irin na sarakai tace, "Allah ya ja zamanin uwar gida kuma amaryar yarima Asad." D'an k'aramin tsaki taja suka zauna kusa da ita Habiba tace, "Ai na rantse da Allah babu amana, ace wannan abin alkhairin ya same ki sai dai naji na gari amma ko a waya baki kira kin sanar damu ba?." Walida tace, "Ai wallahi Rauda baki kyauta mana ba duk yadda muke dake."
Rauda tace, "Sai abu ya dame ka ko yana maka dad'i sannan kake tunanin fad'awa wasu, ba auren sa zanyi ba kinga babu amfanin fad'ar" ta Fad'a a hankali tana kallon su. Habiba tace, "Akan me baza ki aure shi ba?, arzuk'i yazo miki har gida kisa k'afa ki ture shi."
"Ba irin wannan arzuk'i ake nema ba Habiba."
Walida tace, "irin wanne ake nema? Kamar a gaban ki aka fad'a mana halayyar wanda yace yana sonki d'in meye abin kin amincewa?."
Rauda tace, "gidan sarauta bai dace dani ba Walida. A tak'aice ma ya akayi kuka san da maganar nan?." Habiba tayi dariya tace, "Ke kina wasa da lamarin gidan sarauta kina kuma wasa da lamarin y'an unguwa, maganar babu inda bata zaga ba wallahi." Rauda ta girgiza kai cikin mamaki kafin Habiba tace, "meyasa bai dace dake ba? Ke ba mace bace ba?."
"Macece amma ba irin wacce ta dace taje can bace."
Habiba tace, "kawai dai bakya ra'ayi amma ni banga aibun hakan ba." Rauda tace, "Daga furta zai aure ni abubuwa marasa kyau sai faruwa suke dani da iyalan gidan nan, har gida suka je aka dake ni da Ummana har aka ji mata ciwo a hannun ta har yanzu bai warke ba; suka d'aye kwanikan gidan mu kawai dan a wulak'anta mu. Allah ya kawo shi Asad d'in da wanda ya buge ni aka kaimu asibiti daga nan suka kawo mu nan da sunan za'a gyara wancan ashe rushe su sukayi. Mahaifiyar sa tazo har gidan nan tana yi min gargad'i akan in na aure shi sai taga bayana, akan me zan kai kaina halaka?."