← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 115 OF 131

Sashe 115

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaunar da ita yayi a kan kujera yana kallon fuskar ta yayi mata alama da kansa meya faru, muryar ta har lokacin rawa take tace, "Yazo nan bayan an kashe hasken gidan" ta tsaya tana jan numfashi a hankali ya furta, "Nutsu ina tare dake" ya fad'a yana goge mata hawayen fuskar ta ta rik'e hannun sa k'am tana kallon hanya tace, "Yazo nan! Yazo wallahi na ganshi."

Ganin a rud'e take har lokacin akwai tsoro a tare da ita sai ya d'auki wayar sa da hannu d'aya ya rubutawa Suhail message ya sanar dashi Hydar yana gidan a tabbatar an nemo shi kafin safiya, ajjiye wayar yayi ya sake rik'e hannunta yana kallon ta sai hawaye take yi.

"Ya bani wancan maganin yace in ban sha ba sai ya kashe ka!" Ta fad'a tana sake fashewa da kuka. Dumm k'irjin Asad ya buya ya d'auki kwalin maganin  yaga sunan sa nan take ya d'auki wayar sa ya shiga Google yana duba maganin na meye abinda ya gani ya saka shi firgita yace, "Kin sha?."

Kai ta d'aga masa alamun eh tana kuka, ya sauke numfashi mai tsaho ya furta, "Why!." Muryar ta na rawa tace, "Yace dole na zab'i d'aya ko na sha ko ya kashe ka ko yayi min fyad'e, dak'yar na gudu yana so ya tab'a niiii" ta fad'a tana sake fashewa da kuka ya rungume ta sosai a jikin sa zuciya sa na wani irin bugu mai k'arfin gaske.

"I'm sorry naje wajan Mama ne" ya fad'a yana shafa bayan ta gagarumin tashin hankali yana sake mamaye masa zuciya musamman da ta ambaci fyad'e ji yake kamar ana soka masa mashi a zuciyar sa sabida bala'in kishi da zafin da yake ji a ciki.

Tashi yayi zai fita tayi saurin rik'e shi ya dawo ya zauna tace, "Kar ka barni ni kad'ai zai dawo, tsoro nake ji dan Allah kar ka fita." Komawa yayi ya zauna ya sake rik'e ta a jikin sa hankalin sa yakai mak'ura wajan tashi haka zalika ransa yakai k'ololuwar b'aci so yake yaje ya samu masu tsaron wajan su fad'a masa aikin me sukayi har da za'a shigo b'angaren sa har saman sa matsayin sa na shugaba babu wanda ya sani.

Hannun sa ya d'ora a kan cikin ta ya runtse ido har lokacin kuka take yi tana jikin sa yace, "Meyasa kika sha? Meyasa baki amince an kashe ni d'in ba?. Tashi mu tafi asibiti." Kai take girgizawa amma batayi magana ba sai daga baya tace, "Bazan iya ba, bazan iya bashi kaina ba, bazan iya gani an kashe ka ba, gwara cikin ya zube" ta sake fad'a tana kuka sosai.

Bayan ta yake bubbugawa alamun rarrashi duk da har lokacin haushin ta yake ji amma bazai barta cikin wannan hali bai rarrashe ta ba babban tashin hankalin sa Hydar dan yasan zai dawo kuma wajan ta zaizo ba wajan shi ba. Tablet d'in ta buɗe a hannunta tace, "Ban sha ba, ya d'auka nasha a lokacin hankalin sa ya tashi yaji ana buɗe gate alamun kun dawo sai na neme shi na rasa."

Tablet d'in ya d'auke daga hannun ta ya mik'ar da ita tsaye tak'i barin jikin sa har lokacin ya kaita d'akin sa ya zare hijjabin jikinta ya ajjiye a gefe ya kwantar da ita yace, "Ki huta." Zai fita ta sake rik'e shi tana girgiza masa kai ya sauke numfashi dole ya zauna a gefen ta tana rik'e da hannun sa tana sauke numfashi alamun taci kuka ta k'oshi.

Wayar sace tayi k'ara ganin sunan mahaifinsa ya saka shi ya d'auka ya saka a kunne daga can b'angaren yace, "Asad da gaske Hydar yana gidan nan?." Asad ya girgiza kai kawai kamar yana gaban sa dan bazai iya magana ba b'acin ran da yake ji a zuciyar ba bazai barshi magana ba.

Jin yayi shiru Abba ya sake cewa, "Kayi magana Suhail ya sanar dani kace a bincika yana nan, kenan shine ya saka aka kashe wutar gidan?." Asad ya sauke numfashi yace, "Abba yazo har wajan ta." Jin yadda maganar Asad d'in ta fita yasan akwai tarin b'acin rai a tare dashi alamun wani abun ya faru Abba yace, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Amma dai lafiya ko?."

Asad yayi shiru yana runtse idanun sa ya kalle ta yaga itama shi take kallo ya d'auke kansa yana girgiza kai kana kallon sa kasan ransa b'ace yake. Jin bai amsa ba ya saka Abba yace, "In zaka iya sauko kasa Uncle ka zai zo kuyi maganar sabida a san abinda za'ayi kar abun yayi nisa."
Datse kiran Asad yayi ya mik'e zai fita ta kwab'e fuska tana kallon sa tare da girgiza kanta ya zauna ya dafa goshin ta yana kallon ta amma baice komai ba kafin ya zame hannun sa ya tashi ya fita.

K'asa ya sakko tun daga nesa da Uncle da Suhail suka hango shi suka san ran maza ya b'aci domin kuwa fuskar sa har ja tayi sabida b'acin rai annuri kona sisi babu akan fuskar sa yana k'arasowa ya kalli Suhail yace, "An same shi?." Suhail ya tsorata da yanayin Asad yaja baya yace, "ranka ya dad'e an duba ko ina amma ba'a samu Hydar a gidan nan."

"Meye amfanin ma'aikatan gidan nan har da Hydar zai shigo har nan har sama babu wanda zai ganshi? Meye aikin su?" Ya fad'a cikin fad'a sosai yana kallon Suhail har sai da ya tsorata dan bai tab'a jin muryar sa da amo haka ba.

Suhail yace, "Allah ya wuci zuciyar ka ranka ya dad'e tuba nake, dukkan su hankalin su ya tafi tunanin abinda ya d'auke wutar gidan a yadda akayi bincike an tabbatar shine ya kashe wutar gidan."

Uncle da yake kallon Asad yanayin b'acin ransa ya tabbatar da an yiwa matar sa wani abun ya kalli Suhail yace, "Meya amfanin cameras gidan din gidan nan da aka saka? Meyasa basu mayar d ahankali wajan kula da duk wanda zai shigo gidan ba?."

Asad ya murza yatsun sa na tsakiya da babba suka bada sauti ya kalli Suhail yace, "Aje a duba a tabbatar an gano ta hanyar da ya shigo nan" yana fad'a ya juya ya koma Suhail ya fita ya kalli Uncle yace, "Gaskiya akwai abinda ya faru da ya b'ata ran mai martaba haka, dole a nemo inda Hydar yake nan gaba ba'a san me zaiyi ba."
Uncle yace, "Ya kamata."

Asad lokacin da ya ya same ta a tsaye a falon ta kasa nutsuwa ganin sa ya saka hankalin ta ya kwanta ya rik'e hannun ta suka koma ta kwanta ya kalle ta kamar zai magana sai ya fasa ya cize bakin sa. Ya jima a haka kafin ya dawo nutsuwar sa yace, "Ki nutsu babu abinda zai faru." Kai ta girgiza yana zaune a gefen ta har bacci ya d'auke ta ya d'auki waya ya fita yana neman Suhail.

A daren sai da aka tabbatar da ta inda Hydar ya shiga b'angaren sa da ta inda ya fita sannan hankalin sa ya kwanta aka tara meeting na ma'aikatan duk a dare aka yiwa kowa warning akan kula da aikin sa duk suka amsa da zasu dage Suhail ya sanar dashi sai a lokacin yake jin nutsuwa a zuciyar sa.

Yana zaune bayan sun gama waya da Suhail kawai yaga kiran Hydar yana shigowa ba tare da tunanin komai ba ya d'auka ya saka a speaker kafin yayi magana Hydar yace, "To dan ka saka an nemo ta inda na shiga apartment d'inka ai ba wani abu bane mai wahala, ka sani masu tsaron ka ina da yaran da in nazo zan shiga zasu bar wajan suyi kamar wani aikin ne ya taso musu. Ina da mutane da yawa a gidan nan ko me naso yi zanyi lafiya lau babu damuwa."

Asad baiyi magana ba hakan ya saka ya kuma cewa, "Na samu matar taka ai a zab'in da na bata na d'auka zata ce a kashe kane sai naji gwara ta bar babyn ta ya salwanta da dai kai ka bar duniya, amma fa naso ta amince dani mun kasance yau d'in nan kasan ance mace mai k'aramin ciki sirri gare ta" sai ya kyalkyale da dariya yace, "Kwantar da hankalin ka ko hannunta ban rik'e ba tunda dai tasha maganin shine burina, zan juyo kanka daga baya."

Asad ya runtse ido ya buɗe murya a kausashe yace, "Ka kiyayi had'uwar mu Hydar!" yana fad'a ya yanke wayar ya cillar akan kujera ya dafe kai da duka hannayen sa.
Bai jima a haka ba ya tashi ya shiga d'akin yayi wanka ya saka kaya ya kwanta a gefen ta amma ko kad'an bacci yak'i zuwa idanun sa sabida b'acin rai, tsaki yayi ya d'aura alwala ya tayar da sallah.

Washe gari da wuri Rauda ta bar b'angaren ta koma nata dan ita take son dinga yi masa abinci ba ma'aikata ba, duk da akwai kitchen a saman nasa amma bata tsaya yi a can ba ta sauko k'asa. Da kanta tayi duk abinda ya kamata sannan ta saka aka d'auka suka tafi tare aka kai har lokacin bai fito ba kasancewar asabar ce babu zaman fada.

Hadimar ce ta koma ita kuma ta tuna wayar ta na saman sai ta hau saman da sallama ta shiga falon ya amsa ta ganshi a zaune amma bai kalle ta ba, k'arasowa tayi ta zauna tace, "Barka da rana." Kai kawai ya d'aga mata ta tab'e baki ta duba wajan da wayar ta fad'i ta hango ta a can k'arshen kujera har chajin ya k'are saboda fitila da take a kunne tama manta ita.

Kallon sa tayi taga ya wani d'aure fuska yana zaune da manyan kaya kansa babu hula yana ta aikin kad'a k'afa ya d'ora d'aya kan d'aya, "Breakfast yana k'asa" ta fad'a tana niyar mik'ewa kallon da yayi mata ya saka ta fasa tashin ta koma ta zauna ta kawar da kanta gefe itama ta d'aure fuska ta fara kad'a tata k'afar.
Chapter 115 · 0% Book details