← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 131

Sashe 57

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shigowar Baba shine ya hana Yaya Ummi magana ya kalli Ummi yace, "Ki taya y'ar uwar ki da addu'a shine yafi ba wannan d'aga muryar ba dan ba amfani zatayi miki na. Rauda baki da lafiya ne?" Ya fad'a a tausahe yana kallonta. Kallon sa tayi cike da mamakin yadda yayi mata magana tace, "Kaina ne yake ciwo Baba."
"Dole kanki yayi ciwo kin kwana kina kuka, Kisha magani zai daina in sha Allah. Ki kwantar da hankalin ki kuma komai ya faru Allah ya k'addara faruwar sa tun kina ciki kafin kizo duniya, komai zai wuce tamkar bai faru ba.

Kai ta d'aga zuciyar ta cike da jin dad'in yadda Baban yake mata magana cikin taushin murya da kalamai masu kwantar da hankali ba kamar jiya ba sai taji hankalin ta ya sake kwanciya ko babu komai tasan yanzu Baba bazai ga laifin ta akan sakin ba. Baba yaa kalli Umma yaga fuskar nan tata a d'aure ta kawar da kanta gefe yace, "Binta kawo min ruwan sha sama." Kafin tace wani abun ya fita Umma da tasan babu wani ruwa da za'a kai masa badan taso ba ta mik'e bata d'auki ruwan ba ta fita.

Rauda tace, "Allah yasa su shirya, Yaya Ummi jiya naga tashin hankalin da ban tab'a gani ba Baba kamar zai daki Umma." Yaya Ummi tace, "da alama, a yanayin sa ai zaki ga ya gano bai kyauta ba shiyasa kika ga ya sauko har yana rarrashin ki. Daman banda abin Baba meye na fad'a?." Rauda bata ce komai ba tayi tagumi kawai tana kallon wani wajan daban.

        Lokacin da Umma ta hau saman a zaune ta same shi ta shiga ta zauna itama batayi magana ba yace, "Binta nasan ban kwanta ba jiya ni kaina sai yanzu na gano kuskure na tun farkon maganar sa da Rauda nine na bayar da goyan bayan ko meye ya faru nine na bada k'ofar faruwar sa. Kiyi hak'uri ki d'auka k'addara ce abinda ya faru jiya ma kiyi hak'uri."

Umma ta sauke numfashi tace, "Ya wuce." Baba yace, "itama Rauda ki bata hak'uri nasan ban kyauta mata ba tun farko, bata so akayi auren tayi biyayya ta amincewa abinda na zab'a mata ga kuma abinda ya faru na kuma d'ora mata alhakin hakan."
"Ai babu komai kamar yadda kace k'addara ce babu wanda yake kauce mata duk inda kake sai ta bika ta same ka, mun karb'e ta hannu biyu in sha Allah nan gaba zamu ga alkhairin hakan. Ni sai nake ganin ko na tura ta gidan Yaya Bilki tayi iddar ta a can?."
"Da idda a kanta ne?" Baba ya fad'a yana kallon ta da mamaki.

Umma ta d'aga kai tace, "Akwai idda tun dawowar ta na fahimci hakan a tare da ita, ni burina ma Allah yasa ba ciki dan bana so wata alaqa ta sake had'a mu kar nan gaba suzo suce abinda ta haifa ba nasa bane, shiyasa na k'agu naga ta gama iddar hankalina zai fi kwanciya."

Murmushi Baba kawai yayi kafin yace, "basai taje ko ina ba ki barta tayi iddar a nan babu wanda k'addara ta wuce fad'awa kansa." Umma tace, "haka ne. Allah yasa mu dace." Baba ya amsa da amin bata jima sosai ta sakko k'asa.

*☆☆☆*

          Washe gari su Asad suka tafi Madina aka kai Abba asibiti nan da nan aka karb'e shi aka fara k'ok'arin gano kan matsalar a sannan Asad ya bar Hydar da Uncle a wajan sa shi ya tafi hotel ya shirya cikin farar jallabiya ya saka huta fara k'arama a ciki ya d'ora hirami fari ya saka bak'ar alkyabba kamar yadda labarawan suke yi. Sak ya fito a balaraben Saudia ba b'ata lokaci mota tazo ta d'auke zuwa taron da aka gayyace shi.

Bai dawo da wuri ba dan an tattauna abubuwa da dama ciki harda son da suke ya dawo Madina da zaka amma ya nuna hakan bazai yu ba, maimakon ya koma hotel sai ya nufi asibitin wajan su Abba. Kamar can a ranar dai ba'a ce ga abinda yake damun Abba ba Asad yace bazai koma ba ya zauna nan suka wuce ziyarar Rauda.

Kwanan su biyu a madina amma shiru ba'a samu wani cigaba ba anyi iyakacin binciken da ya kamata amma ba'a ga wani ciwo ba dukkan su hankalin su ya tashi sosai. Asad yana zaune bayan an gama yi musu bayani ya dafe kansa ya kalli Hydar yace, "Hydar bazan bar Abba a nan ba zamu koma Nigeria dashi." Hydar yace, "Amma ranka ya dad'e da ka barshi a nan zai fi samu kula a akan can."

Uncle ma yace, "Nima a gani na ranka ya dad'e gwara zaman nan d'in zai fi samu kulawa akan can, amma hukuncin daka yanke shine daidai."
Asad ya shafa fuska sa kana yace, "muje dashi can" yana fad'a ya mik'e dukkan su babu wanda ya isa ya musa washe gashi jirgi ya d'auko su zuwa Nigeria.

A katafaran b'angaren da aka gina mai kyau da tsari aka sauke Abba kafin la'asar an had'a duk abinda Abba zai buk'ata a cikin gidan an fara bashi kulawa a cikin gidan. Asad yana zaune a falo bayan an gama kula da mai martaba Mama da Hajiya da Ammi suka shigo da sallama. Mik'ewa yayi yana amsawa suka shiga inda mai martaba yake bai bi bayan su ba Jim kad'an suka fito Hajiya tace, "Amma sai nake gani zaman sa a can zaifi samun kula a akan nan."

Asad yayi shiru bai amsa ba Ammi tace, "Gwara nan d'in yafi samun addu'a." Nan ma dai baiyi ba suka fita aka bar shi da Mama ta kalle shi tace, "meyasa bakayi shawara dani ba ka tawo dashi nan?." Ya d'aga ido ya kalle ta sai ya sunkuyar da kai tace, "dakai nake magana  meyasa?."

Kansa ya dafe kad'an kafin yace, "Please Mama" yana fad'a ya hau sama ba tare da yace komai ba domin haushin su dukkan su yake ji ya barta a wajan a tsaye a tana kallon sa. Mamaki ya kusa saka Mama ta zube a k'asa a wajan ta bishi da kallo cikin tsantsar tashin hankali amma sanin babu abinda zatayi ya saka ta fita zuciyar ta cike da tashin hankalin da bata san dalilin sa ba.

Bayan wasu kwanaki.
[17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*054.*

         Waya ce a hannun Mama tana juya ta kana kallon yanayin ta kasan tana cikin tunani domin fuskar ta ta bayyana hakan kallo d'aya zakayi mata ka fahimci akwai damuwa mai tarin yawa a tare da ita duk da tana k'ok'arin b'oyewa. Sake kallon fuskar wayar tayi ta danna video call ta kira Aliyu, ba jimawa aka d'auka fuskar sa ta bayyana a kai ta kalle shi tace, "Aliyu kana wacce k'asa ne?." Aliyu da yake zaune ya kalle ta yace, "Bahrain."
"Yaushe zaka dawo ne? Wannan wanne irin zama kake yi a wata k'asar bayan kasan ina buk'atar ka nan." Yace, "Mama zan dawo akwai abinda nake yi a nan d'in ne amma dana gama zan dawo nima nafi so na dawo nan d'in akwai dalilin zaman nan d'in." Yana bata amsa ta yanke kiran ta cillar da wayar a kan kujera ta dafe kai da duka hannayen ta.

"Asslamu alaikum" Hydar ya fad'a a sanyaye yana shigowa falon ya zauna a kusa da ita. A ciki ta amsa ya kalle ta yace, "Akwai damuwa a tare da mahaifiyata, ko zan iya sanin dalilin zuwan ta?." Ta furzar da iska ta jima a haka bata bashi amsa ba kafin ta d'ago tace, "Hydar Asad! Ya canja yanzu gabad'aya kamar bashi ba." Hydar ya girgiza kai yace, "Allah yaja da ran Mamana akwai wani abu da ya aikata ne?."

       "Meye ma bai aikata ba Hydar? Asad yanzu baya shawara dani yake aiwatar da komai sai dai naji labari a bakin Sadiya ko Jidda, Sadiya da Jidda sai sun fara jin abu kafin ni naji meyasa yake neman canjawa lokaci d'aya?." Hydar ya girgiza kai yace, "Allah ya wuci zuciyar ki; kinfi kowa sanin halin Asad kece kika haife shi kika kuma raine shi kinfi kowa sanin halin sa a kan kowa a duniyar nan. Duk yadda akayi yana da dalilin aikata abinda yake yi."

"Dalilin sa na banza da wofi, duk yadda kake tunanin Asad a baya yanzu ba haka yake ba. Wacece Sadiya da zata riga ni sanin wani abu daya shafe shi?."
"Allah ya wuci zuciyar ki, zan same shi da kaina nayi masa magana a kai in ma akwai wani abun da yake damun sa zan ji."
"Jeka maza yanzu, yamma ce yana b'angaren sa."
"A tashi lafiya" ya fad'a cikin girmamawa yana tafi ya fita direct ya wuce b'angaren Asad.

        Asad yana zaune hannun sa rik'e da waya yana dannawa Jidda ta fito daga d'akin sa sanye cikin riga da siket y'an kanti kanta babu d'ankwali tayi kyau sosai tana zuwa ta yiwa kanta mazauni a cinyar sa ta kwace wayar a hannun sa ta ajjiye a gefe ta had'a goshin su waje d'aya tana kallon idanun sa. Shima kallon nata yake yi kamar yadda take kallon sa; shidai kawai yasan zuciyar sa tana sonta a wannan lokacin amma bai san yaushe hakan ya samo asali ba.

Murmushi tayi masa shima ya samu kansa da mayar mata da martani khamshin bakin sa ya daki hancin ta ba shiri ta kai bakin ta kusa da nasa ta d'ora a hankali ta fara kissing d'insa slowly, bai hanata ba sai ma taya ta da yake yi hannun ta akan sajen fuskar sa tana shafa gashin tana sake rik'e fuskar tasa sosai. Kusan minti biyu suna a haka kafin ta zame bakin ta a hankali tayi dariya ta kwanta a k'irjin sa tace, "i love you my king."

Idanun sa ya lumshe ya bud'e su a kanta muryar sa can k'asa yace, "Love you too." Wani irin dad'i take ji yana ratsa jijiyoyin jikinta tayi farrr da idanun tana jin kanta a sama in ta tuna Asad da yake fizge-fizgen yanzu shine a hannun ta sai abinda tace masa yake yi.
Chapter 57 · 0% Book details