Sashe 72
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Su Mama kuwa k'ofar gidan su Rauda suka tsaya daidai lokacin Baba yana niyar shiga ganin mota babba kamar wannan ta tsaya ya saka shi ya tsaya shima dan Umma ta sanar dashi komai yana ganin motar abinda yazo ransa kenan, Suhaima ce ta bud'e gaban motar ta fito ta zaga ta bud'e maman ta baya ta kalle ta tace, "Mama mun zo." Shiru Mama tayi bata amsa ba Suhaima tace, "Sai da nace Mama ki zauna baki da lafiya amma kika ki."
Mama ta d'an yatsine fuska tace, "Dan Allah jeki kiyi magana dasu ta fito muje." Suhaima ta kulle motar ta kalli cikin gidan taga Baba a tsaye ta k'arasa inda yake tace, "sannu." Yace, "yauwa. Fulanin ce a mota?." Suhaima tace, "eh" ta bashi amsa a tak'aice yace, "to bara na turo Rauda" ya fad'a muryar sa har rawa take ya shiga ciki ita kuma ta tsaya tana jiran sa.
Kamar an cillo shi haka suka ganshi a falon Rauda na raka'ar k'arshe a sallah ya kalli Umma yace, "Ga Fulanin tazo tana waje tana jiran Rauda a mota taje su tafi." Umma ta kalle shi tace, "Shine kake rawar jiki haka Malam? Sallah take yi to." Ya kalli Rauda da take zaman tayya yace, "kiyi ki idar kar ki barsu suna jiran ki." A wannan lokacin Rauda tayi sallama yace, "Maza tashi kije ku tafi ki raka su ki dawo."
Rauda kamar zata yi kuka ta kalli Umma ta dawo da kallon ta ga Baba tace, "Baba yanzu kana goyan bayan na raka su?." Baba yace, "kamar ya ina goyan baya?, zaki tashi kije ko sai nayi ball dake?." Rauda hawaye ya sakko mata ta kalli Umma da take kallon ta itama tace, "Umma bakwa jin tsoro in na bisu su kaini wani wajan da zasu kashe ni? Kun manta matar nan bata sona meyasa zaku ce na bisu?."
Umma zatayi magana Baba yace, "Tashi ki wuce." Babu yadda ta iya tana hawaye ta fita da hijjabin da tayi sallah ta fita zuwa k'ofar gidan Suhaima na ganin ta sai tayi murmushi ta wuce gaban motar ta shiga ta lek'o ta taga tace, "Shigo nan." Rauda jikin ta a sanyaye ta share idanun ta ta isa gaban motar ta shiga suka d'auki hanya.
Tafiya sukayi mai d'an nisa kafin su iso unguwar kasancewar ta shiru babu kowa sai haske wani b'angaren wani b'angaren kuma babu, suna isa k'ofar gidan suka ga akasin haka domin akwai mutane har lokacin ga wajan a cike dam Suhaima ta faka Rauda ta kalle ta tace, "Ina zuwa" ta fad'a tana fita ta shiga cikin gidan.
Jim kad'an ta fito tana fitowa ta k'araso inda suke tace, "Kuzo muje" tana fad'a tayi gaba abinda Mama taji kamar ta jawota ta tsinka mata mari dole suka fito suka bi bayan ta baza kace Mama ta rab'i sarauta ba domin hijjabi ne a jikinta har k'asa.
A k'aramin d'aki suka zauna Rauda tayi shiru kamar babu ita a wajan fuskar ta cike da b'acin rai kana kallon hakan zaka fahimta dan fuskar a d'aure take matuk'a, gyaran muryar Baba ya saka ta kalli k'ofa ya shigo ya zauna a kan kujerar da yake zama yace, "Babata ana ta saka ki aiki ko?." Murmushi tayi mai kama da yake tace, "babu komai ai Baba, bara na shiga ciki" ta fad'a tana tashi ta basu waje domin su tattauna.
Sun jima sosai har Rauda ta gaji da zaman sai daga baya aka aiko kiran ta alamun sun gama ta shiga d'akin ta samu Baba yana fad'in, "Bazan karb'i komai daga wajan ku ba, banyi dan a biya ni ba kowa yasan dan Allah nake taimakon kowa da aljihuna nake siyan ko wanne magani na kuma bayar kyauta. Nayi miki ne kodan shi shugaban namu na garin nan baza mu so rayuwar da aka jefa shi a ciki ba dole muyi iya bakin k'okarin mu wajan ganin mun taimaka ya dawo hanya ma daidaiciya duk da muma a wajan Allah muke nema." Mama tace, "Mun gode Allah ya saka da alkhairi" karon farko kenan da ta yiwa wata halitta godiya da irin wannan addu'ar.
Baba yace, "babu komai ai yiwa kaine, in kika rik'e abubuwan dana baki da wanda shi za'a bashin nan da wasu kwanaki masu zuwa ko wanne irin tsafi ne zai bar jikin sa in sha Allah amma sai kin dage da addu'a sosai muma kuma zamu taya ki." Mama tace, "Amma dan Allah malam bana so mutane su san da maganar nan, amincewa dakai ya saka na kawo kuka na wajan ka in mutane suka san abinda yake faruwa ban san ya zanyi ba."
Baba yayi murmushi irin na tsoffi yace, "Duk wanda yasan Baba malam yasan baya fidda sirrin wani ga wani, manyan mutane da suka fiki sunzo wajena kuma sun koma lafiya har yanzu babu wanda yasan me ya kawo su. Inda ina fitar da sirrin wani zuwa ga wani da ban kawo yanzu ba, kema da ba'ayi miki kwatance na ba." Mama tayi shiru ya kalli Rauda yace, "Babata kin kyauta abinda kikayi kar kiji a zuciyar ba'a kyauta miki ba abinda kikayi shine daidai. Ita rayuwa haka take akwai lokacin da baka so aikata abu ba In ka aikata sai ya zamar maka alkhairi, ki saka a ranki alkhairin kenan kuma ki taimaki wanda yazo inda kike." ya kalli su Mama yace, "na barku lafiya" ya fad'a yana tashi ya koma ciki suma suks mik'e hannun Mama rik'e da leda mai girma suka fita zuwa wajan mota kamar d'azu suka shiga mota suka d'auki hanya.
Tafiya suke yi shiru motar Suhaima ta d'an taka burki taji motar ta tsaya ta cigaba da tafiya ta sake taka burki ya sake tsayawa Mama tacee, "Tsayuwar meye?." Suhaima tace, "Burkin nake ji yana cizewa ne" ta cigaba da tafiya.
K'atuwar mota ce tawo ta gaban su Suhaima tayi gefe mai motar ya danna horn ya gigita Suhaima tana k'okarin taka burki amma abin yaci tura hankalin Mama ya tashi ta kank'ame ledar da Baba malam ya bata tace, "Suhaima ki tsaya mana zaki kashe mu fa." Suhaima hankali tace, "Mama taki tsayawa, tak'i tsayawa wallahi." Motar ce take sake tunkaro su gashi suma tafiya suke babu sitiyarin yak'i juyawa yayi baya. Rauda ganin mutuwa kusa hankalin ta ya tashi tana kuka tace, "Mu fita a haka!."
Kamar jira suke kuwa Mama ta bud'e motar duk da tafiyar da take yi ta fad'a gefe itama Suhaima tayi gefe Rauda ma ta fita ta buge da k'aton dutse a gefe hannun ta ya daki motar da take gudu akan titi ita kad'ai. Garam motar ta daki babbar motar wata motar daga bayan su a guje tayo kansu daidai saitin da Mama take ba tare da sun farga ba, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Mamaaaaaa!" Suhaima ta fad'a da k'arfin gaske cikin ihu tana yin inda Maman take a guje.
*Mama ta ware fa*🤣🤣
[17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*062*
Da zafin nama Rauda ta jawo Mama da k'arfin gaske suka fad'i a k'asa motar ta wuce a guje ba tare da ta kalle su bama balle ta bada haƙuri, Suhaima ta k'araso inda suke ta d'ago Mama ta d'ago Raudan ma ta kalle ta tace, "Na gode, badan ke ba da yanzu mota tabi ta kan Mamana" ta juya ta kalli Mama tace, "Mama babu inda yake miki ciwo?." Mama kallon Rauda take yi suka had'a ido Rauda ta d'auke kai domin hannun ta zafi yake mata sosai ga kashin bayan ta da ya bugu fad'owar da tayi daga mota.
Mama so take tace mata ta gode da ceton ranta da tayi amma ta gaza fad'ar hakan sai kallo kawai hannun ta k'amkame da ledar da Baba malam ya bata; ta bar wayar a cikin motar amma bata iya barin ledar ba sabida mahimmacin ta a wajan ta. Kallon motar Mama tayi ta ga gaban motar yayi kwatsa-kwatsa shi kuma mai babbar motar ya gudu ganin basu lura dashi ba.
Suhaima tace, "Mama ina zamu je yanzu? Ban fito da waya ba balle na kira driver yazo ya d'auke mu, taki kin barta a ciki na tabbatar baza ta amfanu ba" ta fad'a tana dafe kanta dan itama ta bugu kanta ciwo yake sosai. Rauda da take hango gidan su tace, "Sai anjiman ku." Ganin ta fara tafiya tana rik'e bayan ta ga hannun da take yarfe shi kana gani kasan yana mata ciwo Suhaima tace, "bai kamata ki tafi ba asibiti ya kamata mu wuce a duba ki." Rauda ta kalle ta tace, "Babu komai" tana fad'ar hakan ta cigaba da tafiya.
"Na gode." Ta tsinci muryar Mama a bayan ta hakan ya saka Rauda tsayawa cak ta juyo yanayin fuskar ta ya nuna tana jin ciwo a jikin ta tace, "Aikin musulmi na gari ceton rai ne ba d'aukar rai ba" tana fad'ar haka tayi gaba abinta ba tare da ta sake kallon su ba sai a lokacin take jin haushin kanta ji take ina ma ta bari motar ta markad'e ta kowa ya huta.
Mai keke napep Suhaima ta tsayar ta fad'a masa asibitin da zai kai su ta shiga tace, "Mama shigo muje." Mama ta kalle ta ta kalli napep d'in wai yau itace zata shiga keke napep lallai rayuwa ta fara canja mata baya. Babu yadda ta iya haka ta shiga suka tafi wajan Dr Yasir sukayi sa'a yana nan ya duba hannun Mama ya duba na Suhaima ma yaga duka buguwa ce ba ciwo bane ya basu magani da kansa ya d'auko su a mota zuwa gida.