Sashe 81
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Aliyu meyasa?" Ta fad'a tana kallon sa. Shima kallon nata yayi ya rasa me ya canja maman nasa lokaci d'aya itace take cewa meyasa aka yiwa Hadimai hukunci...? Baice komai ba ya kalli Hydar yace, "Ina so na had'u da Asad." Hydar yace, "Yana k'aramin falon sa yana tare da bak'i."
Baice komai ba kawai ya mik'e ya fita Mama ta bishi da kallo zuciyar ta tana mata rawa a kansa dan gani tayi gabad'aya ya canja kamar ba shi ba kamar kuma shi ta girgiza kai tace, "Akwai alamar tambaya akan sa, meya canja Ali haka?." Hydar yace, "Mama ashe bani kad'ai na gani ba, tabbas Aliyu ya canja kamar bashi ba." Kai take girgizawa ta koma ta kwanta a jikin kujera dan har lokacin cikin ta ciwo yake yi mata.
A k'aramin falon cikin gida kamar yadda akace Asad ya gama ganawa da bak'i yana kashingid'e yana duba wani littafi a hannun Aliyu ya shigo da sallama, amsawa yayi yana kallon sa shima shi yake kallo Asad bai san ya mik'e tsaye ba sai murmushi yaga Aliyun yayi yace, "Our king surprise" ya fad'a yana bashi hannu alamun su gaisa. Sai kuma ya janye hannun yace, "Oh sorry ba haka ake gaida ku ba" sai ya duk'a kamar yadda ake yiwa sarakuna yace, "Allah ya taimaki sarki ya k'arawa sarki lafiya."
Asad ya saka hannu biyu ya d'ago Aliyu ya mik'e tsaye yana kallon sa da farin ciki a kan fuskar sa ya mik'a masa hannun alamun su gaisa, Aliyu daman abinda yake so kenan da sauri ya bashi hannu suka gaisa yana kallon Asad yana wani irin murmushi mai d'auke da ma'anoni da dama a cikin sa.........
*karfa muje ya shafawa Asad maganin hauka Fans....*😨
[17/12, 10:41 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*066.*
Kallon kallo suke dukkan su baza ka iya fassara yanayin su ba duk da akwai murmushi akan fuskar ko wannen su amma yadda suke kallon juna hakan zai baka tabbacin akwai wani abun a k'asa a dinne wanda ba kowa yasan dashi ba. Asad ne ya fara janye hannun sa Aliyun ma ya janye Asad ya sake fad'ada murmushin sa yace, "Yaushe ka dawo?."
Jin yadda maganar Asad ta fita cike da iyayi ana bawa ko wanne harami na kalmomin hakkin sa sai abin ya bawa Aliyu dariya ya dara kad'an yace, "Ba'a jima ba ranka ya dad'e." Asad ya murmushi ya koma ya zauna Aliyu ya zauna shima a k'asa kamar yadda Asad d'in ya zauna kana Asad yace, "Barka da zuwa." Murmushi ya kuma yi yace, "Na gode."
Shiru wajan yayi babu mai magana ko wanne da abinda yake sak'awa a ransa Aliyu ka katse shirun da fad'in, "In mai martaba yayi min izini zan shiga wajan Abba naga yanayin jikin sa." Asad ya kalle shi yace, "A fito lafiya." Tashi yayi yace, "A tashi lafiya our king" ya fad'a yana niyar tafiya har yaje gab da k'ofa sai kuma ya juyo yaga Asad d'in ma kallon sa yake yi sai suka saki murmushi a tare Aliyu ya fita.
Da wannan murmushi a fuskar sa ya shiga b'angaren mai martaba ya samu an zaunar dashi idanun sa a buɗe Uncle ya bashi alkur'ani yana karantawa, sallamar Aliyu ya saka shi kallon k'ofa Aliyu sai ya saki murmushi ya k'araso kusa dashi ya kalli Uncle yace, "Uncle barka da safiya." Uncle yace, "Aliyu yau kaine a k'asar tamu?." Murmushi yayi ya shafa kansa kafin ya kalli Abba da yake kallon sa shima ya rik'e hannun sa yace, "Ina farin ciki da naga mahaifina lafiyar sa tana samuwa, Allah ya tashi k'afadun mai martaba nan bada jimawa ba."
Uncle ya amsa da amin sai mai martaba ya murmusa ya cigaba da karatun sa bai kuma kallon sa ba, Aliyu kallon gefen drawer yayi yaga allurai a ajjiye da yawa ya kalli Uncle yace, "wannan fa?." Uncle yace, "itace wacce ake masa duk sati." Aliyu ya girgiza kai ya d'auki allurar ya d'auka a waya ya ajjiye sai suka had'a ido da Uncle sai yace, "zan nunawa wani Dr ne naji ya ingancin ta." Uncle yace, "ba laifi."
Aliyu yace, "Ina dawowa" ya fad'a yana fita daga b'angaren ya wuce tsohon b'angaren su wanda suke da d'akuna a can. Har zai gota b'angaren Jidda sai kuma ya tsaya cak ya kalli b'angaren nata yaga dogarai maza biyu masu gadin ta a tsaye a k'ofar da zata shigar da kai wajan nata, ba tare da wani tunani ba ya nufi wajan hango shi da sukayi sai suka mik'e suka zube a k'asa yana zuwa bai bi ta kansu ba kai tsaye ciki ya shiga.
A cikin falon kuwa Jidda na zaune ita kad'ai ta kori kowa na b'angaren nata waya na hannun ta kamar ko yaushe suna waya da Mum tana fad'in, "Mum naga Aliyu wallahi na ganshi ya dawo!, na shiga uku na lalace Mum komai zai lalace." Daga can b'angaren Mum tace, "Dallah malama ki nutsu, me Aliyun zai miki kika bi kika tsorata da dawowar sa haka? Mukayi maganin Asad sa balle shi karan kad'a miya."
Jidda ta rausayar da kai tace, "Mum baza ki gane ba, Aliyu ya wuce duk inda kike tunani wallahi tsaf zai lalata mana shirin da muka jima munayi. Dawowar sa ba alkhairi bace ba a rayuwar mu meyasa ba'a kashe shi a can k'asar b......." cak maganar ta maqale baki bud'e ta mik'e tsaye tana kallon inda ta ganshi a tsaye ya hard'e hannayen sa a k'irji yana kallon ta fuskar nan tasa a tamke babu alamun fara'a a cikinta.
A hankali yake takawo hannun sa na cikin aljihu yana Isowa kusa da ita ya saka hannu ya zare wayar hannun ta ya saka a speaker yaji Mum na cewa, "Waye Aliyu nayi maganin Asad da uwar su ma balle wani shi jiki duk neman mata...?. Ki nutsu Malama ina so na gama da babar sune sannan na juyo kansa amma tunda naga kin tsorata sosai zan dawo da aikin kansa ko ba'a kashe shi ba za'a kulle bakin sa ko meye ma ya kasa fad'a. Nayi maganin Asad ma mai k'arfin ibada balle shi karan kad'a miya, ita kanta Rabi tana tsalle rijiya da baya ne amma gab nake da kawo k'arshen ita da yaran nata gabad'aya."
Jidda ta k'ame babu damar magana sai kallon sa da take yi yana sauraron abinda Mum take cewa da hannu yayi mata alama da ta bata amsa Jidda ta had'd'iye yawu murya na rawa tace, "Toh Mum." Mum tace, "Yauwa ki kwantar da hankali babu abinda zai faru ina tabbatar miki da hakan. Naji ya saka an kama hadiman babar sa akan yana zargin an zubawa babar sa guba zan gargad'i Ladidi kar ta bari sunana ya fito a cikin tuhumar su kome zai faru kar tace nice na saka ta dan Aliyun nan ba hankali ne dashi ba sai yayi min hauka." Mum tana gama fad'ar hakan ta yanke wayar Aliyu wayar da kallo suka had'a ido da Jidda ya saukar da idanun sa zuwa cikinta yaga ciki ya fito ya tab'e baki yana girgiza kai bace komai ba ya dire mata wayar ya fita.
Hannu Jidda ta d'ora a ka tace, "Na shiga uku! Shikenan ta faru ta k'are!" ta fad'a hannun ta na rawa sosai zuciyar ta a tsorace tana sake kiran Mum amma bata samun ta sai kawai ta d'auki wayar ta shiga d'aki ta saka babban hijjabi ta fito ta saka aka kira jakadiyar ta suka rufa mata baya zuwa inda mota take ajjiye driver ya shiga yaja su sai gidan Mum jikin ta har rawa yake sosai.
Aliyu yana fita b'angaren nasu ya nufa a kan hanyar sa ta tafiya yaga ana yiwa su Ladidi hukuncin da yace ayi musu duk sun galabaita sai kuka suke da hannu yayi musu alamun da su kawo masa su ya shiga falon ya zauna, a lokacin aka shigo dasu duk suka zube a k'asa dogaran suna baya yayi musu alama da su koma su suka fita yabi su da kallo dukkan su kuka suke yi har ita Ladidin.
"Allah yaja da ranka kayi mana rai, wallahi ban aikata komai ba bazan iya cutar da Fulani ba ko sau d'aya" wacce take kula da kitchen d'in ta fad'a tana kuka. Da yatsa ya nuna su yayi musu alama da su fita su jiki na rawa suka mik'e duk da gab'ob'in su duk sun gashi suka ce, "Mun gode, Allah yaja da ranka yasa kafi haka."
Sai da suka fita ya kalli Ladidi da take raba idanu rashin gaskiya ya bayyana a tare da ita yace, "Bana son cin amana in na kama mutum da cin amana ina sakawa a b'atar dashi daga duniya ne ma'ana a kashe shi!" Ya fad'a yana kallon ta sai jikinta ya cigaba da rawa dan ta tabbatar ya gano ta ta rushe da kuka tace, "Allah ya taimake ka wallahi sharrin shaidan ne ban san kuma guba bace, Hajiya Sadiya ta bani tace maganin da zai ragewa Fulani zazzaɓi ne ni kuma ganin alaqar su sai na amince na zuba kamar yadda tace. Ka yafe min ranka ya dad'e nasan na aikata babban laifi amma bazan sake ba."
"Ai sai kina raye zaki sake" ya bata amsa ba tare da ya kalle ta ba yana danna wayar sa tana sharb'ar majina tace, "Dan Allah annabi Muhammad S.A.W kayi hak'uri ka yafe min ranka ya dad'e, kuskure ne kuma baza'a sake ba wallahi anyi na farko anyi na k'arshe. Nabi Allah na bika ranka ya dad'e ka taimake nj." Aliyu ya sauke numfashi ya kalle ta yace, "Zan k'yale ki amma da sharaɗi d'aya."
Jikin ta na rawa ta nutsu taji yace, "yadda na gano ki cikin sauk'i kin san duk abinda kika kuma aikatawa bazai min wahalar gano ki ba ko?." Ta d'aga kai tace, "Kwarai ranka ya dad'e." Ya gyara zama yace, "bayan wannan Sadiyan ta tab'a baki wani maganin ki bawa Mama?."
"Bata tab'a ba wallahi, jiya ne rana ta farko."
"To ki nuna mana aiki kike mata har yanzu, duk abinda ta baki ki karb'a ki amsa kice zakiyi in kun rabu sai kizo ki bani duk abinda ta baki."