← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 131

Sashe 10

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hydar yace, "yanzu kenan umarnin Abba ne baza ka iya cikawa ba?." Kallon sa yayi shima ya kalle shi yace, "Yeah gashi kana k'okarin bijirewa bayan shima umarni ya baka." Jin hakan sai ya sauke numfashi ya tashi jiki a sanyaye ya ahiga band'aki shi kuma ya fita ya k'yale shi. Ya jima sosai sannan ya fito yayi wanka ya shirya cikin k'ananun kaya suit black yayi kyau sosai kamar baturen America ya shiga d'akin karatun sa ya d'auki littafan da yasan zai nema ya zuba a jaka ya kalli agogo.

K'arfe uku na yamma ya rage aww uku kenan jirgin su ya tashi, kan gadon sa ya kalla yaga Passports dinsa dana Rauda babu na iyayen ta bai damu ba ya d'auka ya saka a aljihu a lokacin Hydar ya shigo yana kallon sa yace, "Wow! Ango kayi kyau." Bai iya cewa komai ba Hydar ya d'auki jakar yace, "muje na saka maka a mota, tare ma zamu je in yaso sai na dawo da motar taka gida."

Asad yace, "Ina Aliyu da Suhaima?."
"Suhaima suna Kano da Mama Aliyu kuma kasan yana wajan y'an matan sa yanzu ai ko?."
"Yanzu zan tafi ban yiwa mutanen gidan sallama ba?."
"Haka Abba yace."
Shiru yayi baice komai ba Hydar ya fita ya barshi dan yasna in ya biye masa sai su b'ata lokaci har ayi missing flight.

Kulle d'akin yayi ya zare key d'in ya saka a aljihu yana juyowa Hafiz ya shigo falon yana fad'in, "Asad tafiya ba sallama?." Asad ya kalle shi yace, "urgently ne ban shirya ba." Hafiza yace, "Allah ya dawo da kai lafiya."
"Amin" ya furta yana yin gaba shima yabi bayan sa.

Mota ya shiga Hydar ya shiga mazaunin driver yaja suka fita daga cikin masarautar kewa tana mamaye zuciyar Asad ya juya ya kalli gidan yana ji a jikin sa kamar ya fita kenan har abada. Numfashi ya sauke lokacin da ya daina hango gidan ya lumshe ido yana jin jikin sa wani iri. Hydar ya kalle shi yace, "ya naga kana kallon gidan kamar baza ka dawo ba?." Baice komai ba suka d'auki hanyar gidan su Rauda yana jin sa wani iri kamar bashi ba har suka k'arasa k'ofar gidan suka faka.

Hydar ya kalle shi yace, "muje ciki ko?." Asad kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya fito Hydar ya bud'e bayan motar ya d'auko kujerar kome ya tuna kuma sai ya mayar da ita baya ya kulle boot d'in suka nufi cikin gidan.
Suna zaune dukkan su da alama duka y'an gidan suna nan suka tsaya basu shiga ba sai ga Baba ya fito suka gaisa yayi musu iso zuwa ciki, da sallama suka shiga cikin gidan suka amsa gabad'ayan su Asad shi dai bai kalle su ba ya gaishe su dukkan su suka amsa daga nan yayi shiru baice komai ba.

Hydar yace, "Mama zasu wuce Airport lokacin tashin jirgin su ya kusa kar lokaci ya k'ure." Umma ta sauke numfashi ta kalli Rauda da take zaune cikin doguwar riga ta Abaya mai mayafi cikin kayan da aka siyo mata da Baba ya bada kud'in fuskar ta a cushe baza ka banbance yanayin da take ciki ba lokaci d'aya.

Umma ta kalli Asad da kansa yake k'asa tace, "Amana ce gata zan damk'a maka a hannun ka, na sani kafi k'arfin Rauda ta ko wanne b'angare amma kuma kana naka Allah yana nasa dukkan mu bamu tab'a kawo haka ba ko a mafarki sai gashi ta kasance ana kiran mu matsayin ma'aurata a yanzu. Dan Allah ka duba Allah ka rik'e Rauda hannu biyu kaine ka ganta kace kana sonta a haka kar wata rana ka tuna da asalin ta kayi mata wani abun. gata nan amana ce a hannun ka ka rik'e min ita dakyau dan Allah, kar ka bari wani abun ya same ta."

Yadda Umma tayi magana da sanyi kamar zata zubar da hawaye sai zuciyar sa ta karye nan take yaji anya baiyi kuskuren nuna yana sonta ba duba da irin yanayin gidan da yake?, da ace baice bai furta ba da yanzu ba'a aura masa ita ba, tabbas yasan baza'a k'yale ta ba a yanzu haka baza'a rasa wanda suke neman su ga sun mata wani abun ba kawai dan a raba su. Sai yake ji a zuciyar sa ina ma ya danne bai nuna ba kodan ta zauna lafiya ita da iyayen ta, yanzu in wani abun ya same ta shi ya zaiyi kenan?. A sanyaye ya kalli Umman yace, "Ina sha Allah Mama ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai faru." Maganar sa ta fita kamar koda yaushe a tausashe kuma a k'asa in ba nutsuwa kayi ba baza kaji me yake cewa ba.

Sosai Umma taji dad'in abinda yace tace, "na gode sosai, Allah ya bada ikon rik'e ta ya kawar da duk wani abun k'i a zaman ku na tafiyar da dawowar ku." Da amin Hydar ya amsa shi kam a ciki ya amsa Hydar ya kalli agogon hannun sa yace, "lokaci na tafiya yana dakyau muje."

Tare aka mik'e shida Hydar suka yo gaba kafin su fito ma har sun shiga mota. Yaya Ummi ce take taimakawa Rauda tana tafiya fuskar ta duk ta jik'e da hawaye ta kuma kasa tantance kukan me takeyi, na farin ciki zata samu lafiya ko kuma kukan tausayin kanta take yi. Lokacin da suka isa bakin motar aka bud'e mata bayan motar ta shiga Hydar yace, "Ammmm basai ta shiga dasu ba akwai abinda zatayi amfani dashi in mun fita" ya fad'a yana kallon Yaya Ummi ganin zata saka sandinan a cikin motar.

Yaya Ummi ta kalle ta tace, "Dan Allah ki daina Kuka Rauda kamar baki karb'i k'addara ba?. Da kanki kika cemin kin daina kuka meyasa kuma kikeyi yanzu?, dan Allah ki daina tafiya ce ta d'an lokaci zakuyi zaki dawo gida dan ba tarewa kikayi ba gabad'aya. Kiyi hak'uri ban san me kike ji ba amma nasan da ciwo abinda kike ji shiyasa nace kiyi hak'uri." Kai kawai Rauda ta d'aga bata iya cewa komai ba.

Asad da yake tsaye ya kalli su Baba da murmushi a fuskar sa yace, "Sai mun dawo." Baba ya washe baki yace, "Allah ya kai ku lafiya ya dawo daku lafiya ya bada lafiyar daka je nema." Da amin ya amsa ya bud'e gaban motar ya shiga suka ja motar suka bar k'ofar gidan a daidai wannan lokacin sautin kukan ta ya cika mota.

Shiru motar babu mai magana sai kuka da take yi sosai babu wanda yace mata kanzil dan daman kuka dole tayi shi lokaci d'aya ba tare da ta shirya ba a raba ta da iyayen ta ai dole ta zubar da hawaye. Wayar Asad ce take k'ara duk hankalin sa baya jikin sa kukan da take yi har ta katse bai ji ba aka kuma kira Hydar ya kalle shi yace, "Relax Mr man, ana kiran ka." D'auko wayar yayi ya duba gaban sa ya fad'i ganin sunan Mama yana yawo a kan screen d'in wayar tasa.

Daurewa yayi ya d'auka ya saka a kunne take cewa, "Asad kana ina yanzu?." Shiru yayi kana yace, "Ina hanyar Bauchi zanje airport."
"Airport kayi me a can?." Shiru yayi bai amsa ba ta kuma cewa, "ko Kano zaka zo?." Nan ma bai bata amsa ba sai taja tsaki tace, "Bana son rashin hankali ina yi maka magana kayi min banza, wani lokacin shirun nan naka na iskanci ne in kaso maganar kana yi na lura da hakan."

Ya bud'e baki zaiyi magana tace, "kome kaje yi a airport d'in ka tsaya yanzu jirgin su Jidda zai sauka ka kaisu gida ita da Mum dinta kar kace min kuma wani abun ya tsayar dakai" tana fad'ar hakan ta yanke kiran dan a tunanin ta ba k'asar zai bari ba dan tasan baya barin k'asar sai ta sani. Sauke wayar yayi daga kunnen sa ya kalli Hydar da yake tuk'in sa ya d'auke kai baice komai ba har suka isa airport d'in.

Mintina talatin ya rage jirgin su ya tashi suka fito daga motar Hydar ya fito da jakunnan su ya fito da kujerar ya turawa Asad alamun ya fito da ita, bud'e gefen da take yayi har lokacin kanta na kan cinyoyin ta tana kuka mai sauti, ya kasa mata magana ya kuma kasa tab'a ta balle ta d'ago yayi mata alama ta sakko ya tsaya cak kawai yana kallon ta ya rasa me zaiyi. Hydar ganin yana b'ata lokaci yace, "Asad lokaci yana tafiya fa." Kamar bazai yi ba sai kuma ya mik'a hannu a hankali ya bubbuga kafad'ar ta tana jin sa tayi masa banza dan tayi alqawarin indai bai magana ba wallahi baza ta fito ba.

"Raudaaaaaa!" Ya furta in sweet voice wacce ta ratsa shi kansa balle kuma ita da aka kira sunan nata ba shiri ta d'ago kanta tana kallon sa da idanun ta da suka jik'e sabida hawaye shima kuma ita yake kallo, yamutsa fuska yayi ganin yadda hawaye ya b'ata mata fuska idanun ta sunyi ja da hannu yayi mata alama da ta goge idanun ta ya nuna mata kujarar alamun ta sakko. Bata motsa ba sai kanta da ta mayar k'asa ya matsa sosai kusa da ita ya rik'e hannayen ta duka ya fito da ita ya zaunar da ita da kansa a kan kujerar ya kulle k'ofar motar ya danna madannin tafiya a jikin kujerar ta fara tafiya a hankali shi kuma yana bayan ta Hydar kuma yana jawo musu jakar su.

Kusa dashi Hydar ya koma yana dariya yana fad'in, "Wannan ita ake kira da silent love." Bai kula shi ba har suka shiga ciki aka duba jakar su kamar yadda ake yi suka shiga ciki Hydar ya d'aga musu hannu yana murmushi zuciyar sa cike taf da farin ciki ya juyo.

Wara idanu yayi lokacin da idanun sa ya fad'a kan na Mum da Jidda dukkan su a firgice da alama sunga wucewar Asad da Rauda sai ya basar ya maze ya d'auko izzar da ya ajjiye ya d'orawa zuciyar sa ya kalle su yace, "Mum kece?."
Chapter 10 · 0% Book details