← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 131 OF 131

Sashe 131

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Asad yace, "Abba ya jikin Aliyu?." Abba ya murmusa yace, "Asad kenan, Allah yayi maka albarka, Allah yasa ka cigaba da ganin albarka a rayuwar ka daga nan har ka bar duniya. Kana son y'an uwanka da zuciya d'aya su kuma suna yi maka zagon k'asa."

Asad ya amsa da amin kafin Abba yace, "Jikin ana samun cigaba sosai, Allah ya yiwa Kawun matar ka baiwa ta sanin magani a ayoyin alkur'ani da kuma maganin gargajiya. Jikinsa yana kyau sosai wani lokacin ma har magana yanayi." Asad ya sauke numfashi yace, "Abba Hydar kuma shiru ban sake jin labarin sa ba, jikina yana bani kamar ciwon sa ta tashi a wani waje daban."

Mai martaba yace, "wataƙila kuma yana can yana shirya hanyar da zai kawar da kai dan ba abin yarda bane ba." Shiru Asad yayi kafin Abba yace, "Asad ka kula da y'an uwan ka maza da mata dukkan su kaine babba a cikin su kai Allah ya zab'a ya bawa matsayin da bai bawa wani a cikin su ba, ka kula dasu kar ka bari wani abu mara dad'i ya sake faruwa a masarautar nan, da kai kad'ai na amince zaka saita koma bisa addini kayi haƙuri da duk qalubalen da zaka fuskanta shine matakin nasarar ka."

Asad ya kalli mahaifin nasa jin yana masa magana kamar wasiya kafin yayi magana ya kuma cewa, "kayi mulkin ka tamkar yadda ka fara cikin ilimi da kuma taimakon na k'asa Asad, kar kayi hange akan wata masarautar kace kaima bara ka gwada abinda suke yi kayi naka tsarin yadda ta hanyar mulkin ka zaka shiga aljanna. Kar ka had'a kai da ko wanne d'an siyasa ka tsaya iya matsayin ka duk wani d'an siyasa da yake burin taimakon talakawa shine naka shima kuma kar ka zak'e da yawa."

Asad yayi shiru yana jin rauni na mamaye masa zuciyar sa baice komai ba Abba yace, "Hydar!." Jin yadda ya ambaci sunan Hydar ya skaa ya kalle shi yaji yace, "Kada a sassauta masa ayi masa hukinci daidai da abinda ya aikata, kar kaji tausayin sa kayi masa hukunci Asad yin hakan shine cikar k'imar ka shine zai saka kowa ya fara shayin aikata laifi sabida zasu ga k'anin ka mafi soyuwa a gare ka yayi baka raga masa ba."

Asad ya girgiza kai yace, "Abba dan Allah ka daina irin wannan maganar sai naji kamar kana bani wasiya ne." Abba yayi murmushi yace, "ita nake baka Asad, bani da tabbacin kaiwa gobe a raye shiyasa nake fad'a maka abinda yake raina, ka kuma yi k'okarin cika abubuwan dana fad'a maka. Kar ka amince da kowa daga Mubarak sai Suhail sai kuma matar ka, hatta mahaifiyar ka ba abar yadda bace wanda na lissafa masa sune zasu tsaya ganin sun kare ka daga duk abinda zai same ka, sune kawai zasu iya sadaukar da ransu sabida kai."

Asad yaji yana k'ok'arin yin hawaye yaji Abba yace, "Kar kuka ya zubo daga idanun ka Asad, kai jarumi ne ka rik'e wannan jarumtar Kar ka bari zuciyar ka ta karye."

Asad ya kasa magana mai martaba ya cigaba da fad'in,  "Addu'a kar kayi wasa da ita, nasan baka yi kana iya k'okarin ka amma ka k'ara a yadda kake yi d'in Asad! Itace ta kawo ka matakin da kake kai ka daure ta sake kaika na gaba. Na amince dakai Asad dukkan dukiyata dana mallaka suna hannun ka bayan na rasu d'an autan ku bana so yayi kuka balle kuma y'an uwan ka mata, ka zamar musu mahaifi ka zamar musu Yaya ka zamar musu shugaba." Ya rik'e hannun Asad yace, "Nasan indai kana raye babu wanda zaiyi kuka Asad, bana so iyalai na su tarwatse sabida rashin kula kayi min alqawarin kula da komai yadda ya kamata."

Asad ya kasa magana sai zuciyar sa da ta karye yayi shiru baice komai ba Abba yace, "Nasan kayi Asad bani da haufi akan alqawarin ka nasan zaka cika dan baka cikin mutane masu sab'a alqawari. Allah ya albarkace ka dakai da abinda matar ka zata haifa, Allah ya kare ku a duk inda kuke yyi maka katanga da alkhairi ya raba ka da sharri."

Shiru falon yayi Asad ya kasa cewa komai jikin sa yayi sanyi sosai Abba yace, "Tashi kaje ana kiran sallar i'sha." Ya kalli mahaifin sa sai yaga yayi murmushi yace, "Muje tare muyi sallah." Jiki a sanyaye Asad yayi sallar i'sha bayan ya idar ya koma b'angaren sa ya zauna shiru ya kasa furta ko wacce kalma maganar Abba nayi masa amsa kuwa a kunnen sa.

Wayar sa yaji tana k'ara ya duba number Mama bazai iya k'in d'auka ba ya d'auka jin abinda tace ya saka shi sauke numfashi ya jima a zaune kafin ya taso ya sakko zuwa k'asa.

A nan ya same su dasu Mum ganin hakan sai ya daure yace, "Mama da an kirani dana zo da kaina." Kallon sa kawai tayi ta tabbatar akwia abinda yake damun sa amma bata muna ba tace, "Sadiya da Eman ne suke so su ganka." Zama yayi Mum tana k'asa ya kalle ta yace, "Ya karin haƙuri?." Mum sai ta fashe da kuka tana fad'in, "Alhamdulillah."

Kafin yayi magana tace, "Dan Allah kayi haƙuri ka yafe min nayi maka abubuwa wanda ni kaina ban san adadin su ba." Ya dakatar da ita a hanyar fad'in, "Ko ban san adadin su ba Allah ya sani kuma zai yafe miki domin ni na yafe miki dukkan ku, har ita Jidda na yafe mata ina yi mata fatan samun rahmar Allah."

"Na gode Asad, Allah ya albarkaci rayuwar ka ya baka abinda kake." Ya sauke numfashi yace, "Amin ya rabbil alamin." Mama ta kalle shi suka had'a ido sai ta sauke kai k'asa maimakon shi ya sauke idanun sa k'asa suka tashi suka fita duk sai yaji wani iri a zuciyar sa.

Komawar sa sama babu wuya Rauda tazo inda yake ganin yanayin da yake ciki sai bata yi masa magana taga ya keb'e kansa ita kanta ranar kasa gane kansa tayi duk da tayi k'okarin ganin damuwar ta ragu amma ko kanzil baice mata ba sai dai ya bita da idanu kawai a haka suka kwana kowa zuciya babu dad'i.

*Bayan wasu kwanaki.*
Chapter 131 · 0% Book details