Sashe 102
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hafiz yace, "Mama sai dai kiyi min duk abinda zakiyi amma bazan fasa fad'ar abinda yake gaskiya ba, duk wani tuggu da ake k'ullawa a gidan nan Hydar ne sila shine yake shirya komai duk su Waziri, Aliyu, Jidda da duk wani mai son ganin bayan Asad umarnin sa suke jira." Mama ta sake tsinke shi da mari ta juyo ta kalli mai martaba tace, "Taya mai martaba yana ji yana fad'ar kalamai mara sa dad'i akan Hydar zaiyi shiru" ta dawo da kallon ta ga Asad tace, "Baka ji me yake cewa bane ba Asad? Hydar d'inka fa yake jifa da wannan kalamai masara dad'in ji."
Asad ya d'ago ido ya kalle ta sai yayi murmushi yace, "Mama duk abinda yace ba K'arya yayi ba gaskiya ce. Duk wani abu da ya faru a gidan nan Hydar ne sila, shine ya shirya komai yake kuma bada umarni."
Mama tayi baya zata fad'i Suhaima tayi saurin tare ta suka zauna jikin ta yayi sanyi kamar wacce aka zarewa rai kanta yana sarawa kamar zai rabe gida biyu. Hafiz yace, "Duk wani abu da ake tunanin Suhail ne ya saka na cutar da Asad nine nayi ba Suhail ba, in Mama ta tuna lokacin da na same ta nace an zubawa Asad abu ya tsallaka yana ciwo ba wani ne yayi ba nine ina sane nake saka Suhail a ciki dan a ture shi gefe ni a amince dani dan tabbas Asad ya yarda da Suhail. Yadda ya amince dashi bai amince dani ba shiyasa nake jin zafi da d'acin hakan. Da ina aiki da Aliyu ne amma da na gano Hydar shine babbar giwar sai na koma tsagin sa badan komai ba sai dai abin duniya."
Hafiz ya sake cewa, "Duk son mulkin da Aliyu yake dashi Hydar ya fishi; iya taku shine ya saka yake nuna ko a jikin sa amma yafi kowa d'aga hankalin sa a kai. Ko Mama tasan da cewa gab da Asad zai dawo Hydar ya kwanta ciwo wannan ciwon bana gaskiya bane na shiri ne...? Yayi amfani da cutar da take damun sa ya kwanta ciwo ya aiwatar da dukkan abinda yake so hankalin kwance babu wanda ya kawo komai a ransa. Hydar yasan Aliyu ne yake mulki ba Asad ba sai kuma abinda yace masa yakeyi. Na fad'a muku abinda zai fi haka gigita ku..?" Ya fad'a yana kallon su dukkan su.
Ya cize baki yace, "Hydar shine silar kwanciya Abba ciwo, shine silar da dukkan gab'obin Abba suka daina motsawa. Yana sane tsarin sane yayi hakan da Mama ta dawo da Asad shi kuma ya aiwatar da duk abinda yake so, ya kuma tabbatar matuk'ar mai martaba yana da lafiya wani abun bazai kasance ba shiyasa na aikata abinda ya aikata ko nace yake kan aikatawa. Lokacin da Asad yana Cairo yana sane yak'i sanar dashi rashin lafiyar Abba ya tafi dashi Germany ya hana ko wanne likita ganin sa in ma sun duba shi da zarar sun fita zai masa allurar da ita Rauda ta bada maganin ta."
Ya kalli Aliyu yace, "A tunanin ka maganin da suka baka ka shafawa Asad a fatar hannun lokacin da ya dawo daga Cairo don yayi swapping layin sa a tunanin ka shine silar da ya saka ya manta da Mama? Hmm ba shine bane domin a abincin da yaci ni da kaina na karb'o maganin da aka zuba masa a ciki a wajan matsafan k'asar turkey. Nasa ne yayi aiki ba naka ba yana sane yayi hakan duk dan ya sake tunzura Mama da take ta dawo dashi. Waye ya fad'awa Mama inda Asad yake a Cairo? shine yayi hakan yana sane a wannan lokacin burin sa ya dawo."
"Aliyu kaima kana naka aikin a wannan lokacin amma aikin Hydar yafi naka k'arfi, kaine kaje gidan su Rauda ka sake ta amma kuma turawa a rushe musu gida ba kai ka yishi ba shine yayi badan komai ba dan ya sake tunzura tsanar Asad a zuciyar ta dan kar tayi marmarin sake waiwayar sa har abada; duk inda muka je ana fad'a mana akwai yuwar dawowar ta kuma barazana ce a gare mu, gashi kuwa daga dawowar tata komai yana bayyana." Hafiz ya kalli Hajiya yace, "kina ta kokwanton waye ya zuba guda a zogalen da kika bawa Asad ko? Ba kowa bane yayi Hydar ne, yana sane dan a jefa zargi a kanki a kawar da hankali daga shirin sa ya kuma jefa kin."
Ya sake kallon kowa na falon yace, "Zuwan Asad Germany ya takura sai an dawo da Abba a wannan tafiyar ya shirya canja Asad inda ya yiwa Aliyu zazzafar message ya tsara masa komai shi kuma ba tare da tunanin komai ba ya hau kan plan d'in ya zauna daman neman mafita yake yi. Duk wani likita da zaku gani a gidan nan indai Hydar ne ya kawo shi yana karya garkuwar jikin Abba ne ba lafiya yake samar masa ba, ya shirya komai nasa tsaf amfani yake da Aliyu so yake da zarar an haukatar dashi sai shi ya maye gurbin kujerar ya mulki kowa son ransa."
"Duk soyayyar da yake nunawa yana yiwa Asad ta bogi ce a zuciyar sa babu wanda ya tsana sama da Asad, kullum b'acin ransa ta ya Asad ya kasance abin so a wajan iyayen su shi ya koma baya? Ta ya kowa yake zancen Asad bashi ba? Ta yaya za'a ce shida Aliyu suna da makusa shi bashi da ita...?."
Shiru falon babu mai motsin kirki a cikin su kowa yayi shiru yana kallon Hafiz Mama kam ji take zuciyar ta tana gab da bugawa. Mai martaba yace, "ko kun san jiya da daddare Hydar ya shigo har d'akin da nake da niyar kashe ni? Ko kusan ya zuba min poison a a.c dan kawai na shak'a na mutu na bashi waje yayi abinda yake so, bai so yau tazo ba badan tonuwar asirin sa ba sai dan bai shirya kowa yasan waye shi ba dan bai gama tsara abinda yake so ya tsara ba. Hydar yayi kwantan b'auna ya kuma cimma nasara akan abubuwa da yawa amma lokacin bayyanar komai yanzu yayi."
Hafiz yace, "shine master planer, shine yake tsara muku komai a duk sanda yaso shiyasa nace dukkan ku a k'asan sa kuke. Yana amfani da voice changer yana magana daku matsayin mace ku kuma da yake kowa ya saka cuta a zuciyar sa babu wanda ya kawo tunanin da wa kuke magana kawai kun amince dashi. Ku in ba na cikin gida ba taya za'a dinga kawo muku labaran cikin gida wanda na gidan ma basu sani ba?" Ya fad'a yana kallon su dukkan su suma kuma shi suke kallo.
"Mallake Aliyu da Jidda tayi tafi masa dad'i fiye da kowa shiyasa in Mama ta tura shi da magani ya kai mata sai ya zubar ko shi ya shanye amma bazai kai masa ba. Da ace Abba ya bar Hydar ya tafi da Aliyu wata k'asar a jiya tabbas da sai dai gawar Aliyu amma bashi ba, sannan ya dawo kan Asad domin kuwa dukkan ku sai yaga bayan ku harda ke Mama domin kina k'okarin bashi matsala zai kawar dake dan cikar burin Hydar yafi masa komai a duniyar nan."
"K'arya kake Hafiz! K'arya kake Hydar d'ina bazai tab'a aikata abinda kake fad'a ba, taya Hydar d'ina yaga lafiyar da zaiyi abinda kake cewa shida yake kwance cikin ciwo a ko wanne lokaci?. Hydar yana son Asad bazai tab'a cutar dashi ba, Hydar yana son mahaifin sa bazai tab'a aikata abinda kake fad'a ga mahaifin sa ba, Hydar yana sona bazai tab'a yunƙurin yin abinda kake fad'a min ba. Na amince duk abinda kuka fad'a Aliyu zaiyi tabbas ya aikata shi amma banda Hydar K'arya kake bazai tab'a yin abinda ake cewa zaiyi ba" hawaye sharrrr daga idanun Mama sai kuma ta dafe kanta tace,
"Ta ya ma Hydar zaiyi haka? Ta wacce hanya duk abinda ka fad'a za'a ce Hydar ne shi kad'ai ya aikata ta yaya hakan zata kasance banda K'arya?!" Ta fad'a cikin kuka tana kallon Hafiz da take ji kamar ta bindige shi.
Hafiz yace, "Ya aikata fiye da haka domin kuwa har laya ya saka Asad a kujerar zaman a office duk dan yayi masa Farraqu daga gidan nan amma Allah bai bashi sa'a ba. Hydar ya wuce tunanin ki Mama a gaban sa nake fad'ar komai nasan kuma komai domin tare ake shirin dani. Duka wannsn tunanin naku akan sa shiyasa yake cutar daku domin dukkan ku kun amince dashi amma shi kuma ta b'angaren sa ba haka abun yake ba. Shiyasa yayi nasara akaan Asad sabida yasan dukkan lagon Asad yasan abinda yake so yasan wanda baya so, yasan abinda yake ci yasan wanda baya ci. Da ace maqiyin ka na kusa dakai gwara yana nesa dakai domin maqiyin kusa yafi na nesa sharri."
Suhaima da take rik'e da Mama tace, "dan kai kana aikatawa hakan ba yana nufin ka yiwa Yaya Hydar wannan mummunan kazafin ba, wallahi K'arya kake Yaya Hydar babu ta inda zai iya aikata abinda ake fad'a, yana son yaya Asad karen Yaya Asad Bobby Yaya Hydar bazai iya cutar dashi ba balle kuma shi."
"Mama, Suhaima ya kamata ku daina rantsewa duk abinda kuka ji an fad'a ku amince dashi domin kuwa Hydar zai iya aikata abinda yafi haka ma. Kuna yiwa Hydar kallo a baibai ne amma Hydar ya wuce duk inda kuke tunani, dukka abinda aka fad'a yanzu kad'an ne daga cikin shirina kuma har gobe ina kan bakata ban sauka ba!" Muryar sa ta karad'e falon cikin kaushin murya mai fita a zafafe da nuna tsantsar isa da izza da kuma zallar mugunta a cikin ta.
Hydar!🤒🏃🏼♀️
[17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*081*