Sashe 104
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Baba ya sake cewa, "Duk abinda mai martaba yace shine daidai a wajan mu, Allah ya kaimu lokacin da rai da lafiya." Mai martaba ya amsa da amin ya kalli Asad yace, "banji kace komai ba? Ko na k'yale ka sai kaje can gidan?" Ya fad'a cikin zolayar Asad d'in. Murmushi ya kubce masa wnada baiyi niya ba ya shafa kansa yana jin nauyi da kunyar mahaifin nasa. Shima murmushin yayi yace, "Muje muyi sallah ayi jana'izar yaran da aka rasa" ya fad'a yana mik'ewa kowa ya mik'e ya kalli Baba yace, "Malam ya kamata a tsaya a samu ladan jana'iza in yaso sai su matan su tafi gida." Tare suka fito yana gaba Asad yana bayan sa har lokacin yak'i kallon inda Rauda take balle ma yayi mata magana.
Mota Umma da Rauda suka shiga aka tafi dasu gida su Baba kuma aka shiga masallaci akayi sallah.
*☆☆* A b'angaren Waziri lokacin da ya koma gida ya tarar har an musu suttura har lokacin kumfar bata daina fita daga bakin su ba, wani abu yaji mai nauyi ya tsirga masa ya tsaya a tsakiyar zuciyar sa ya fita da sauri zuwa falon nasa da akace a nan aka gansu. Shigar sa keda wuya yayi karo da kwalbar turaren da aka bashi wanda akace masa matuk'ar mai martaba da Asad ya shek'e su ya gama zaman gida kenan domin guba ne a cikin sa bana wasa ba.
Kai ya dafe yana kallon kwalbar dan yasan Y'ay'an sa guda biyun da suka rasu akwai su da son turare tabbas sun shigo sun ganshi sun buɗe da nufin jin khamshin sa ya zama silar barin su duniya, zama yayi a kan kujera ya dafe kai maganar mai martaba ta fad'o masa inda yake cewa akwai sakayya ko yanzu ko nan gaba.
Bai san ya kuma fashewa da kuka ba zuciyar sa na k'una tashin hankalin sa ya nikku dan ya tabbatar shine ya kashe y'ay'an sa a dalilin son zuciyar sa. Bai san lokacin da ya d'auka a haka ba sai buga k'ofar yaji ana yi yana d'ago kai suka had'a ido da Suhail da idanun sa shima yayi ja alamun yasha kuka shima yace, "Ana jiran Abba dan gabatar da jana'iza" ya fad'a da girmamawa kansa a k'asa.
Haka ta taso jiki a salub'e badan yaso ba yayi gaba Suhail yana bin bayan sa limamin garin Katagum yaja sallar gawar aka sallace su daga nan aka wuce dasu gidan su na gaskiya.
_Son zuciya hausawa suka ce b'acin ta. Allah kasa mufi karfin zuciyar mu Amin._😭😭😭
[17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*082.*
Tunda aka shiga da Jidda d'akin da za'a duba ta Mum take safa da marwa hankalin ta ya tashi abubuwa biyu sun cushe mata zuciyar ta a wannan lokacin, tunanin abinda ya faru da kuma rashin lafiyar Jidda sun d'aga mata hankali sosai ta kasa nutsuwa ko kad'an.
Daddy ne ya k'araso wajan ya kalli Mum d'in yace, "Sadiya lafiya? Meya faru da Jiddan haka?." Mum bata iya magana ba dan bata da nutsuwa a wannan lokacin nuna masa d'akin tayi yaja ya tsaya shima yana kallon d'akin zuciyar sa na harbawa cikin tsoron abinda zai biyo baya.
Tun suna tsaye sai da suka zauna jikin Mum har rawa yake yi so take ma ta zubar da hawaye ma ta kasa sabida bala'in rud'anin da take ciki. Buɗe d'akin da aka shigar da Jidda akayi likita da nurses biyu suka fito Mum ta mik'e ta k'arasa wajan sa tace, "Dr ya jikin nata?." Likitan ya kalli Daddy ya kalli Mum d'in sannan yace, "Ta haihu." Da mamaki Mum ta kalli Daddy shima ya kalle ta ta dawo da kallon ta ga likitan tace, "Kamar ya ta haihu? Yi min bayani ban gane ba."
Dr yace, "Eh ta haihu, ta haifi yaro namiji d'an wata bakwai wanda ake kira bakwaini." Daddy yayi shiru na wani lokaci kafin yace, "Haihuwa Dr?."
"Eh yallabai, tsoro da firgici da tashin hankalin da take a ciki ne ya jawo haihuwar da gaggawa, inda ace cikin k'arami ne bai zama mutum ba da zai zube ne sabida ta firgita sosai."
Mum tace, "Yanzu ya jikin nata ita?." Dr yace, "gaskiya jikin ta babu dad'i, jinin ta ya hau sosai ga kuma haihuwa ga zuciyar ta da take bugawa very fast har yanzu unconsciously take. Babyn kuma yana inda aka tanada domin cigaba da rainon sa."
Baya Mum tayi ta zauna a wannan lokacin Eman tazo wajan ganin yanayin da Mum take ciki ya skaa ta rik'e ta tana fad'in, "Mum meye faru da Jiddan?." Zama tayi kusa da ita Daddy ma ya zauna ya kalli Mum yace, "Ki sanar dani abinda ya firgita Jidda haka dan nasan kuna tare, sannan ya banga mijin ta ko wani nata a nan ba sai ke kad'ai?. Ba taro aka kira ku a gidan sarki ba?."
Kuka Mum take yi sosai babu alamun zata tsayar dashi balle kuma ta iya masa magana ganin hakan sai ya tashi ya fita daga asibitin ma gabad'aya ya barsu a wajan dan firgice shima yake jin ance tsoro ya saka ta haihu. Duk yadda Eman taso rarrshin Mum abin yaci tura kuka take kamar wacce aka yiwa rasuwa itama sai ta fara kukan duk da bata san abinda ya faru ba amma kukan Mum d'in ya sakata kuka dan tasan akwai wani abun a k'asa.
*☆☆*
Kuka Suhaima take yi sosai ganin Mama a kwance ko motsin kirki batayi an saka mata abinda zai taimaka mata wajan yin numfashi amma duk da haka numfashin baya fita yadda ya kamata a kirjin ta yake tsayawa baya sauka ciki.
Tana zaune a kan kujerar kusa da gadon Maman tayi pillow da gadon tana cigaba da zubar da hawaye. "Yaya Hydar, Yaya Aliyu meyasa kukayi abinda kuka yi? Meyasa baku duba halin da Mama dani kaina zan shiga ba kuka zab'i son zuciyar ku akan farin cikin Mama?. Allah sarki Yaya Asad ya zaiji? Duk qaunar da yake yiwa Yaya Hydar amma da abinda zai saka masa kenan?. Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" ta fad'a a bayyane tana sake fashewa da kuka mai tsuma zuciya bata tab'a shiga kwatankwacin rud'ani kamar wannan ba.
Tun daga bakin k'ofar ake jin sautin kukan Suhaima Dr Yasir ya shigo da sauri yana kallon ta murya can k'asa yace, "Suhaima please ki daina wannan kukan baki ga a gaban patient kike bane ba? In kika tashe ta fa?."
Maimakon tayi shiru sai ta nuna masa Mama tana kuka tace, "Mama ce fa a kwance a haka, kalli Mamana ita kad'ai ba Yaya Hydar babu Yaya Aliyu babu Yaya Asad a tare da ita. Ya Mama zataji in ta farka ta ganta ita kad'ai babu su a tare da ita?. Bazan iya yin shiru ba ka barni nayi kukana bazan iya daina kuka ba."
Ganin yadda take maganar kamar bata cikin hankalin ta hakan ya saka shi fita da sauri suka shigo da nurses mata guda biyu aka d'auke Suhaima daga wajan suka fita da ita zuwa wani d'akin daban aka yi mata allurar bacci suka saka mata ruwa dan itama tana buk'atar magani.
*☆☆☆*
Ciwon kai mai tsakani ya saka Rauda a gaba tunda suka koma gida ko buɗe ido bata son yi sabida yadda kan yake mata mugun ciwo ga zuciyar ta da take bugawa tunda take a duniya bata tab'a jin tashin hankali kamar wanda take ciki ba, ji take zuciyar ta na fizga sabida bala'in rud'ani jikinta har rawa yake yi.
Umma da take zaune a gefen ta a zaune ita kuma ta jingina da kujera ta rik'e kai da hannu biyu tana kallon sama. Umma tace, "Sannu Rauda, kodai muje asibiti wannan ciwon kan bana k'are bane ba." Kai ta girgiza alamun a'a Umma tayi shiru tana girgiza kai in ta tuna irin abubuwan da suka ji sai taji amana ta k'are a duniya kowa ma ba abin yarda bane.
Umma ta kalle ta tace, "Gwara muje asibitin kar kiyi b'ari, dan abinda kike ji a zuciyar ki a yanzu tsaf zai iya sakawa cikin jikin ki ya zube." Lumshe ido Rauda tayi ta d'ago kai ta kalli Umma ta mayar da idon ta ta kulle. Umma ta mik'e tsaye ta mik'ar da ita itama tace, "Muje ki kwanta ko zaki samu sauk'in abinda kike ji."
D'aki Umma ta kai Rauda ta kwantar da ita ta bata magani tasha ta zauna a gefen ta har sai da bacci ya d'auke ta sannan ta fito ta k'yale ta. Baba bai dawo ba sai magriba har lokacin Rauda bacci take yi kai tsaye b'angaren Umman ya nufo yana zuwa ya same ta ta idar da sallah tana lazimi a kan kujera ita kad'ai Ummulkhairi da Khalil suna wajan Innan su.
Da sallama ya shigo ta amsa tana sauke numfashi ya k'araso ya zauna yace, "Ya jikin Raudan?." Umma tace, "bacci take har yanzu, dak'yar baccin ya d'auke ta shiyasa ko sallah ban tashe ta ba." Baba ya girgiz kansa yace, "Ai gwara ta samu baccin, irin wannan tashin hankalin sai ya saka zuciyar ka ta buga."
Umma tace, "ita da take da k'aramin ciki ma sai ya zube, wacce ya girma ta fad'i tana zubar da jini ina ga wacce bai girma ba?" Ta fad'a tana tagumi domin abubuwan da suka faru ganin su take kamar almara.
Baba ya girgiza kansa yace, "Wato Binta tunda Allah ya kawo ni duniya ban tab'a jin tashin hankali kamar wanda naji yau ba, ace wanda kuke ciki d'aya uwa d'aya kuma uba d'aya sune suke k'okarin ganin bayan ka akan abinda ba kaine ka bawa kanka ba?. Ke duniya ina zaki je damu? Amana tayi k'aranci kowa ba abin yarda bane ba."