← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 131

Sashe 52

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Munafuki ne, fuska biyu ne dashi ni nasan da hakan. Tunda ka riga ka aikata bani da abin cewa amma ka sani; daga wannan kar ka sake duk wanda kake ganin ya dace ka bashi sarauta kazo ka sanar in yayi min sai ayi."
"In sha Allah."
"Wa zaka bawa sarautar tasa?."
"Wanda kika ce" ya furta kamar zaiyi kuka hakan ya saka ta kalle shi taga yana juya kansa sai ta yanke maganar tace, "Zan duba na gani, amma definitely za'a saka Aliyu da Hydar a ciki."

Hanyar fita yaga ta nufa hakan ya saka yace, "A sauka lafiya." Tana jinsa tayi masa banza ta fita ya sauke ajiyar zuciya ya hau sama ya cire kayan zafin da yake jikin sa ya fad'a band'aki yayi wanka ya fito ya saka kaya k'ananu yasha magani ya kwanta domin Allah kad'ai yasan gajiyar da yayi.

Wayar sace take ta k'ara yayi niyar sharewa amma ganin uncle ne yake wayar ya d'auka ya saka a kunne daga can b'angaren yace, "Allah yaja zamanin mai martaba, ina neman afuwa kira ba tare da neman izini ba." Asad yayi shiru hakan ya saka Uncle yace, "Bak'i ne suka zo daga China sunje wajan babban malamin masallacin cikin gari suna neman ganin mai martaba in hakan zai yu."

Asad yace, "A basu appointment amma banda yanzu na gaji bazan iya komai ba." Uncle yace, "Zuwa anjima sai mu iso, A huta lafiya." Asad ya yanke wayar ba tare da ya amsa ba. Kallon notification yayi yaga sunan Suhail yayi masa message ya bud'e message d'in yaga yace, _Allah yaja zamanin sarki, ina neman alfarmar ganawa mai martaba anjima._ Asad ya tura masa da Allah ya kaimu.

       Message din Dr Khalifa ya gani bai bud'e ba ya ajjiye wayar ya kwanta yana sauke numfashi.  _Mutanen gidan duka sunce a mik'a musu gaisuwa, har ita uwar gidan._ kalaman Baba suka dawo kansa ya sake jin kansa ya sara k'irjin sa na harbawa da sauri maimakon yaji tausayin ta kamar d'azu sai yake jin wani abu mai kama da haushin ta ita da iyalanta gabad'aya. Yaja tsaki ya tashi zaune yace, "Ya zama dole na yanke alaqar mu da ita gabad'aya ko zan huta da abinda nake ji a raina, zanje anjima kamar yadda nace" ya fad'a yana kwanciya ya kulle ido dan so yake yayi bacci.

      A b'angaren Mama data koma b'angaren ta a nan ta tarar da Mum a zaune tana jiranta ganin shigowar ta ya saka ta mik'e sai da Mama ta zauna itama ta zauna tana cewa, "Ranki ya dad'e barka da dawowa." Mama tace, "Sadiya yaushe kika shigo?." Mum tace, "Ina shigowa aka sanar dani fitar ki."
Mama ta tashi tace, "Muje ciki." Tare suka shiga suka zauna a k'aramin falo Mama tace, "Naje wajan Asad ne yana neman fara tarwatsa min lissafi daga fara zaman fada yana yanke hukunci ba tare dana sani ba."

     Mum tace, "naji a gidan jarida ana ta sanarwa tawowa ta a mota nima sai da nayi mamaki nace daga farawa har anzo nan." Mama tace, "Barni dashi kawai zanyi maganin abun. Ya akayi na ganki kwatsam ba notice?." Mum tace, "batu ne akan yarinyar nan da aka bada aiki za'ayi."
Mama tace, "bayan kun ya kasa komai, yau d'in nan sai da Asad yayi magana da mahaifinta."

Mum tace, "ai a yanzu aka gabatar da aikin a gabana an kuma tabbatar min da ya tsane ta kenan har abada, domin kuwa an bani tabbacin a yau zaiji babu wacce ya tsana kamar ta kuma zaiyi k'okarin yanke alaqa da ita." Mama tace, "Allah yasa hakan. Ni ina so nayi waya ma da Malam Audu a warware aikin da aka yiwa Asad kwanakin baya."

Mum da mamaki tace, "Wanne aiki aka yi masa?."
Mama tace, "Oh baki sani ba ashe, lokacin da suna tare da yarinyar can ne na saka akayi masa aikin da bazai iya kusantar ta ba koda yayi niyar yin hakan bazai iya ba. Aikin ya same shi shiyasa har yanzu tsakanin sa da Jidda ba labari amma zanyi magana dashi yanzu."

        Gaban Mum yayi mumman fad'uwa ta wara idanunta waje tare da dafe k'irji tace, "What! Fulani da kanki kika bada go ahead d'in wannan d'anyen aikin akan sa?." Mama bata amsa ba Mum ta kuma cewa, "Ina laifin tun a baya kisa ace a yiwa yarinyar aikin da bazata burge shi bama kwata-kwata bazai ji wani abun a kanta ba balle ma ya kai ga aikata wani abun, amma sai kisa a yiwa Asad guda?." Mama tace, "lokacin kaina ya kulle neman mafita kawai nake yi, amma yanzu za'a warware komai ai ba wani abu bane mai wahala kar dai ki sanar da Jiddan."

Mum tace, "Wannan ai tsakanin mune." Mama tace, "Good, yanzu zan kira shi da kaina sai muji yadda za'ayi." Mum tayi shiru bata amsa ba amma zuciyar ta a cushe take da tasan da wannan maganar ai da tuni ta saka an warware komai dan ita ko kusa ko alama bata wata tazara a tsakanin su so take komai ayi a gama shi a wannan lokacin kafin uwar ta farga.

          *☆☆5:00pm☆☆☆*

B'angaren saukar bak'i ya cika da manya manyan bak'i fararen fata da bak'aken fata suna ganawa da sabon sarki suna ta hotuna cikin burgewa. Yana jin larabci da turanci shiyasa ganawa dasu baya yi masa wahala ko wanne yare ka juya masa zai baka amsa, abokan sa larabawa sun iso taya shi murna sosai yaji dad'i a ransa sosai.

Asad yayi kyau cikin kaya light blue komai blue hatta takalmin k'afar sa blue ne ga alkyabbar tayi bala'in amsar jikin sa yayi kyau matuk'a hakan ya saka sai hotuna ake masa kana kallo kasan ya saka dukiya a jikin sa. Sun jima kafin bak'in su tashi tafiya su bada kyaututtuka su tafi.

Daga nan ya fara ganawa da mutanen cikin gida duk wani wanda ya shafe shi a wannan lokacin sun tattauna. A wannan shigowar Suhail yazo Asad yana zaune a kan karaga Suhail ya zauna a k'asa yana kai gaisuwa hadiman da suke k'asa suna fad'in, "An gaishe ka Suhail, mai martaba ya karb'i gaisuwar ka."

    Suhail ya zauna a gefen sa yace, "Allah yaja zamanin mai martaba sarki." A tare suka amsa da amin Asad ya kalle shi yace, "Suhail." Suhail ya gyara zama yace, "Ranka ya dad'e." Asad ya murmusa kawai baice komai ba Suhail yace, "Allah yaja da ranka zuwa nayi na gaida mai martaba, ina fatan an karb'i gaisuwata."
"Mai martaba yana godiya" suka had'a baki gabad'aya suka fad'a kafin ya sake yin gaisuwa ya tafi.

Bayan kammala zaman fada Asad yana zaune shine da Uncle Asad yace, "Uncle ina so zanje Germany wajan Abban cikin week d'in nan." Uncle yace, "Allah ya k'ara maka lafiya sai a shirya komai nima daman ina so naje." Asad yace, "Uncle ya kake gani zamuyi da Suhail?."
"Ban fahimta ba kamar ya kenan?."
"Sai nake ganin a bashi sarauta mafi kusa dani."
"Eh kuma a'a, abin ne a cikin duhu in ka duba waye mahaifin sa."
"Na amince da Suhail tun ba yau ba."
"In mai martaba yana ganin hakan babu matsala Allah ya shige mana gaba."

Asad yayi shiru yana kallon wani wajan daban kafin suyi sallama ya hau saman sa ya samu Jidda a zaune a falon sama. Yana shiga ta taso ta k'araso kusa dashi ta zaga ta bayan sa ta zame allyabbar jikin sa tana fad'in, "welcome back my king."
"Thanks" ya furta a tak'aice yana zare hannun sa daga alkyabbar, ta duk'a ta zare masa takalimin k'afar sa ya taka zuwa tsakiyar falon ya zauna.

Ajjiye su tayi ta koma inda yake ta cire rawanin kansa shi kuma ya zare k'atuwar rigar da take saman shaddar jikin sa yana sauke numfashi dan ji yake iska na shigar sa ba kamar d'azu ba da zafi ya dame shi. Wajan fridge ta d'auko ruwa mai sanyi da glass cup ta k'araso kusa dashi ta zuba masa ta mik'a masa, kamar bazai karb'a ba sai kuma ya karb'a yasha farin ciki ya mamaye mata zuciyar ta ganin yasha ya ajjiye glass cup d'in ba tare da ya kalleta ba.

      Tashi tayi ta shiga d'akin sa ya bita da kallo shi bai san me zai yiwa yarinyar nan gabad'aya bata burge shi ko kad'an bata cikin zuciyar sa ga tausayin ta yana ji ta wani b'angaren in ya tuna halin da yake ciki bazai iya sauke hakkinta da yake kansa ba dalilin da ya saka yake d'aga mata k'afa. Jim kad'an ta fito ta k'araso kusa dashi tace, "wanka fa." Bai amsa mata ba hakan ya saka tace, "na ajjiye maka ruwan wanka."

Kai ya d'aga kawai kafin ya d'auki wayar sa yana dannawa suna charting da Hydar akan rashin lafiyar Abba sai kuma ya shiga Ig ya dinga karo da maganganun sa na d'azu da video da hotuna ana ta yabon abinda ya furta ya kashe data ya tashi ya shiga d'akin.

  Tsalle ta buga bayan taga shigar sa tana murna tace, "ka fara zuwa hannu wallahi, wuuuu Allah yaja da ranki Mummyna dole na kira ki na baki labari" ta fad'a tana sauka da sauri.

*☆☆☆*

          Tunda Baba ya koma jikin sa yake rawa ya sanar Umma yadda sukayi da Asad ya tashi hankalin kowa na gidan akan a tashi a shirya masa abin motsa baki gabad'aya ya rud'a su. Rauda jikin ta duka a sanyaye take komai dan bata amince da zuwan wani Asad ba dan bata da yadda zatayi ne baza ta yiwa Baba musu ba shiyasa taja bakin ta tayi shiru kawai.

A zaune ya shigo ya samu Rauda tana duba waya yace, "baza ki tashi kiyi abinda yake gaban ki ba sai yazo?." Umma ta kalle shi tace, "Dan Allah malam ka kwantar da hankalin ka basai an had'a masa komai ba dan ko an bashi ba ci zaiyi ba, ka manta matsayin da yake dashi ne a yanzu? Ba komai suke ci ko suke sha ba in aka basu."
Chapter 52 · 0% Book details