Sashe 127
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A kan stool d'in dake tsakiyar make makeken kitchen d'in ya ajjiye ta da yatsan sa yayi mata alama da ta zauna ta gani, binsa take da kallo taga ya dafe kai kad'an ya runtse idon sa zatayi magana ya karkad'a mata tsayan sa dole tayi shiru tana binsa da kallo. Sai da ya daidaita kansa sannan ya tsaya yana kallon kitchen da tunanin abinda zai dafa mata taci.
Kettle ya kunna bayan ya zuba ruwa a ciki ya d'auko cup ya d'auraye shi da ruwa ya buɗe drawer ya d'auko coffee ya had'o da madara da sugar ya ajjiye a gefe. Kallon sa take yi yana sanye da rigar wanka wacce da kad'an ta wuce guiwar sa farar k'afar sa a bayyane a cikin takalmi yawo a cikin gida sai d'aukar ido k'afar tasa take hatta farren k'afar sa abin so ka kalla ne.
"Yawan kallo yana saka mutum ya fad'i." Abinda taji yace kenan tayi murmushi ta sunkuyar da kanta k'asa ya kalle ta shima sai yayi murmushin shima ya kashe switch d'in ruwan ya zuba coffee d'in da sugar ya zuba ruwa kad'an ya d'auko coffee maker ya jona ta itama ya saka a cup d'in yayi making coffee yayi kumfa sosai ya cire ya ajjiye, madarar ya zubawa ruwan zafi a wani kofin daban sannan ya zuba akan coffee d'in nan take yayi sama kamar zai zube sai ya dakata da zubawar ya d'auko ya kalle ta yana nuna mata cup d'in.
Jinjina tayi masa yayi murmushi ya fita ya kai coffee d'in falo ya dawo tana inda take ya d'auke ta kamar yarinya har inda ya ajjiye coffee d'in ya zaunar da ita akan kujera ya jawo coffee d'in ya kai bakin ta ta buɗe tasha ta yamutsa fuska ya kalle ta ya d'aga gira tace, "Babu laifi." Murmushi yayi ya d'auki cake a leda cikin wand Suhail ya kwaso masa ya b'are mata ya mik'a mata ta karb'a taci ta kalle shi tace, "kaima kaci."
Wara ido yayi ya girgiza kai baice komai ba tace, "Allah sai kasha." Ya kalle ta na wani lokaci ya lumshe ido ya furzar da iska amma baiyi magana ba tace, "in fa baka karb'a ba nima na fasa." Ya sake kallon ta yace, "In nasha coffee bazan iya bacci ba."
"Ka karb'a kasha a hakan." Ya kalli agogo ya nuna mata itama ta kalla tace, "Nidai kasha kawai."
Sha d'in yayi kamar yadda tace ya d'aga girar sa sama ya kalle ta ya kalli coffee d'in alamun yayi dad'i, ta tab'e baki tace, "Ba laifi dai, na tabbatar shi kad'ai ka iya shima dan kayi zaman garin larabawa ne." Murmushi yayi yana bata tana sha shima yana sha a haka suka shanye cup d'in.
Ta jingina da kujera shima haka ya rik'e hannun ta suna kallon tv ba dan tana kunne ba tace, "Na fara jin bacci." Ya kalle ta yace, "Na fad'a miki bana iya bacci ko?." Tace, "Aini zanyi baccin ba kai ba."
Ya zuba mata ido har sai da ta kawar da fuskar ta tace, "in kana kallona wani iri nake ji a jikina, idanun ka bana iya kallon su sosai" ta fad'a tana buɗe ido taga fuskar sa daidai tata yace, "me kike ji?."
Yadda yayi maganar ya sakata yin shiru tana kallon sa ya d'aga mata gira alamun ta bashi amsa sai tak'i magana ta sauke ido k'asa, "kince nasha abinda bazan bacci ba nasha, so dole kema bazaki ba." Ta kalle shi ya girgiza mata kai alamun abinda yace kenan tace, "To in na zauna me zanyi ga dare yayi?."
Kafin tayi magana taji saukar bakin sa a wuyan ta ta kulle idanun ta tace, "Sultannnn!."
"Sultanaaaa!" Shima ya furta ba tare da ya d'ago daga jikinta ta ba.
"Na gaji fa Sultan."
Rigar ta yake tattarewa ta k'asa tayi saurin rik'e hannun sa tunawa fa da babu komai a jikinta sai rigar kawai tace, "Sultan dan Allah." Bai bari ba ya kwace hannun sa ya kai hannun sa kan fatar cikin ta yana shafawa a hankali.
Shiru tayi dan ya kashe mata baki gabad'aya, daga shafa cikinta taji yana kai hannun sa sama ta sauke numfashi tace, "Sultannnn!." Yadda tayi maganar ya saka shi juyo da fuskar ta ya hanata sake magana ta hanyar saka bakin sa cikin ta dole tayi shiru badan taso ba.
Bata san ya akayi ba sai akwai ganin ta tayi a kan gado zata kuma magana ya sake hana ta dole tayi shiru tana jin sabon yanayi yana sake yin nink'aya a cikin jikin ta, "Say something Sultanaaaa! Ina so naji kinyi magana" ya fad'a a kunne ta amma babu damar yin maganar a wannan lokacin idanun ta a kulle suke gabad'aya ta kasa cewa komai.
*☆* Tana cikin bargo a jikin sa gabad'aya tana kukan shagwab'a tana fad'in, "Sultan ka b'alla min bayana, wayyo k'afana, cikina zai cire Sultan." Duk ta rud'a shi hankalin sa ya tashi yace, "to ki daina kuka, I'm sorry Sultana." Ta sake shigewa jikin sa tana fad'in, "nidai na gaji bayana ciwo yake min."
"Shiiiii!" Ya furta a kunnen ta ta sauke numfashi jin yana mata tausa a bayan dan da gaske ciwo yake mata sai tayi shiru ta lumshe idanunta bacci yana k'ok'arin d'auke ta. Sai da yaji ta fara bacci sannan ya k'yale ta ya zame ta daga jikin sa yana kallon fuskar ta ynaa murmushi. Allah ya sani yana son wannan baiwar Allah, yana Qaunar ta fiye da tunanin mai tunani, baya so yaga tayi nisa dashi hakan yana sakawa yaji kamar shi kad'ai ya rage a duniya sabida kewa. Kiss ya mata a goshi ya tashi ya shiga band'aki.
Alwala yayi ya fito ya saka doguwar riga ya shinfid'a sallaya, "Sultan ina so nayi sallah nima amma bazan iya ba." Yaji ta fad'a ya juya ya kalle ta sai ya k'arasa kusa da ita ya zauna yana shafa kanta yace, "Zan miki duk addu'ar da kike so, kiyi bacci." Kulle ido tayi baccin ya sake d'auke ta ya gyara mata abinda ya rufe ta ya tashi ya koma kan sallayar ya tayar da sallah.
Har akayi asuba yana sallah sai da ya idar da sallar asuba ya k'arasa inda take ya zauna ya yaye abinda ta furta yana matse mata hancin ta, bata buɗe ido ba dan bacci take sosai ya sake matse hancin ta nan ma bata buɗe idanun ta ba. Sunkuyawa yayi ya cizi kunnen ta yana jan sa da hak"oran sa.
Buɗe ido tayi idanun ta sunyi nauyi sabida bacci ta kalle shi yace, "Sallah Muwaddaty" ya fad'a yana yaye bargon gabad'aya ya d'auke ta bai sauke a ko ina ba sai a band'aki. A gefen bathtub ya ajjiye ta yace, "lokaci yana tafiya." Idanun ta har lokacin akwai bacci sosai ga kanta yayi nauyi hakan ya saka shi zuba ruwa a hannun sa ya shafa a fuskarta, ta yatsine fuska tana shafa fuskar ta ta d'ago ta kalle shi ya d'aga mata kai.
Fita yayi ya barta bata jima sosai ba ta fito tayi alwala cikin kayan sa riga da wando marasa tsaho masu kama jiki sai sukayi mata kamar nata, tana fitowa ya bata abayar ta ta jiya ta saka ta yafa mayafin ta tayar da raka'atanul fijir, bayan ta idar tayi sallar asuba dak'yar ta iya karanta ayatul kursi bayan ta idar ta mik'e ta zauna a kan gadon tana kallon sa yana karatu.
"Barka da safiya Sultan" ta fad'a tana kwanciya ta sake lullub'e jikin ta yayi murmushi dan yasan dole taji bacci badan baya so ta rasa sallah bama da bazai tashe ta ba yace, "Barka da safiya Sultana." Bata sake magana ba bacci ya d'auke ta. Sai da gari yayi haske sannan ya kashe hasken d'akin shima ya kwanta a bayan ta ya dawo da ita jikin sa gabad'aya a haka shima bacci ya d'auke shi.
*☆☆☆*
Yadda take kuka sosai sai ta baka tausayi jaririn d'anta da bai gama zama cikakken mutum ba har lokacin take kallo tana zubar da hawaye tana fad'in, "Ina son shi a haka, dan Allah ya tashi kar ya mutu ya barni."
Mum da take jingine a gado ta rame gabad'aya ta koma kamar ba ita ba saboda rama ta firgice lokaci d'aya, maza ne a tsaye a kanta sai Eman da take kuka ta saka hannu ta karb'i yaron ta mik'awa mazan tace, "Ki daina kuka Allah ne ya baki kuma ya karb'i abin sa, ki bari a kaishi makwancin sa." Mazan suka fita da yaron a hannun sa Jidda ta sake fashewa da kuka ta rik'e hannun Eman tace, "Eman na cuci kaina na cuci rayuwata, Mum ta lalata min rayuwata gabad'aya ta gurb'ata min tarbiyya da addini na. Wallahi badan Mum ba da zuciya d'aya naso zama da Asad ita take zuga ni akan sai na mallake shi Eman."
Eman kuka take itama tace, "Kiyi haƙuri k'addarar ki kenan." Jidda tace, "Ba k'addara bace Eman nice na jawowa kaina, nice na biyewa son zuciya da son mulkin da Mum ta dasa min a zuciyta na biyewa Aliyu muka aikata sabon Allah da auren k'anin sa a kaina. Wallahi Asad ko hannuna bana tunanin ya tab'a riƙewa sai dai ni na rik'e shi amma Aliyu tamkar shine Asad haka ya koma wajan mu'amalar aure dani bana jin tsoron Allah haka nake biye masa dan kawai na kai kaina matsayin da Mum take fad'a min."
"Na raba Aliyu da babar shi duk a tunanin su Asad ne nida shi ne kawai muka san ba Asad bane Aliyu ne...... Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, na shiga uku Eman a ina zanga Asad ya yafe kin?" Ta fad'a yana sake fashewa da kuka sosai.