← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 131

Sashe 50

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Asad yayi shiru Uncle ya kuma cewa, "yana dakyau ka had'a lunch a gayyato mutane da yawa azo a taya ka murna, dan ko iya ranar Monday din Allah kad'ai yasan adadin bak'in da zakayi."
"Not now Uncle, mu fara gamawa da jikin Abba."
"Hakan yana dakyau." Asad yayi shiru baice komai ba Uncle ya kalle shi yace, "kamar akwai abinda kake so ka Fad'a min." Asad ya sosa girar sa guda d'aya ya girgiza kai alamun babu Uncle yace, "Ma sha Allah haka ake so."

Shiru suka kuma yi kafin Uncle yace, "in anyi min izini zan koma." Asad yace, "Thanks you Uncle." Murmushi yayi yace, "koda yaushe ina tare dakai. Ka huta lafiya" ya fad'a yana tashi ya fita.

*☆☆☆*

           "Yanzu Daddy haka zaka yi mubaya'a k'aramin yaro kamar Asad sa'an d'anka ya mulke ka?" Suhail ya fad'a cikin zallar nuna b'acin ransa yana kallon mahaifin sa. Waziri yayi murmushi cikin kunar zuci yace, "Ya zanyi Suhail? In ban bishi ba ya kake so ayi?."
"Ka ajjiye rawanin yafi ka dinga duk'awa masa bazan jure hakan ba ko kad'an." Waziri ya sauke numfashi yace, "Zan ajjiye Suhail daman banyi niyar yin tafiyar nan dashi ba, ba ta yadda za'ayi na kasance a k'ark'ashin baba sa sannan shima na kasance a k'arkashin sa bazai yu ba."

       Suhail yace, "Daddy har yanzu babu wani cigaba da ake samu ne akan tafiyar nan?." Yayi murmushi yace, "Lokaci ya kusa Suhail saura kad'an, babban burina shine daman ya hau karagar mulkin kuma ya hau. Ni yanzu Suhail akwai abinda zakayi ka shiga jikin sa sosai? Naga abotar ku taja baya sosai ba kamar da ba."
"Babar sace take hana shi mu'amala dani kasan kuma yana matuk'ar jin maganar ta shiyasa hakan take kasancewa amma shi har gobe ya amince dani, amma zanyi k'ok'ari naga na koma masa dan shi har gobe bai gano ni ba."

       "Yauwa haka nake so, komawar ka kusa dashi zai bamu damar yin duk abinda muke so tunda ya amince dakai har abin hannun ka yana ci." Suhail yace, "zan koma Baba, Amma sai anyi maganin babar sa." Waziri yace, "Zamuyi wallahi, ita bata isa ba sai munyi abinda muke so, wannan shine lokacin mu ne."

Suhail yace, "zanyi Daddy, sai nayi iya bakin k'ok'arina wajan ganin mulkin katagum ya dawo hannun ka, bazan bari Asad ya dinga juya ka yadda yake so ba matsayin sa na d'an cikin ka, lokacin da komai zai dawo hannun ka yayi."
Murmushi waziri yake yi kana yace, "Allah ya yi maka albarka. Tabbas kai d'an dana haifa ne."
Suhail yace, "in kayi min izini zan tafi."
"Jeka duk inda zaka je."
"A tashi lafiya" ya fad'a yana tashi ya fita zuciyar sa cike da saqe-saqen yadda zai b'ullowa lamarin Asad.

       *☆☆ 8:00pm ☆☆.*

       Tun bayan magriba matar sarki Asad ta hallara a apartment d'insa tayi kwalliya cikin rigar bacci fara mai kyau wacce tafi ta jiya nuna jiki kanta babu d'ankwali gashin kanta ya kwanta luf bak'i sud'ik sai tashin khamshi jikinta yake yi tana zaune tana danna waya a falon saman.

K'arar k'ofa taji hakan ya saka ta kalle shi ya fito daga d'akin karatu sanye jikin jallabiya maroon mai gajeren hannun hannun sa rik'e da wayar sa. 
Cak ya tsaya ya d'auke numfashin sa sabida barazanar da turaren ta ya kawo masa ba tsammani ya jita kwance a k'irjin sa ta zagaya da hannun ta bayan sa ta rik'e shi gam idannun ta a kulle.

Shiru yayi ko motsin kirki baiyi ba sai numfashi da ya sauke a hankali ya lumshe idanunsa ya bud'e ya saka hannun sa ya janye ta daga jikin sa ya kalle ta na sakan 1,2,3, ya d'auke idanun sa daga kanta ya rab'a ta zai wuce tayi saurin sake rik'e shi tana fad'in, "my king wai laifi nayi maka baka kulani?."

Kulle ido ya sake yi ya bud'e kana ya sake janye ta daga jikin sa ya kalle ta suka had'a ido yaga ta kwab'e fuska tana kallon sa bakin ta a gaba alamun shagwab'a.
Wucewa Asad yayi ba tare da ya ce komai ba ya shiga d'aki ya ajjiye wayar sa ya cire agogon hannun sa ya shiga band'aki. Wanka yayi ya fito d'aure da towel a k'ugun sa da k'arami a hannun sa yana goge kansa da k'irjin sa. Without permission ta turo k'ofar ta shigo bai juya ba balle ya kalle ta ya cigaba da abinda yake yi.

     "Subahanallah" ya furta a can k'asan makoshi lokacin da ya sake jin jikinta a jikin sa tana goga fuskar ta a fatar k'irjin sa muryar ta can k'asa tace, "My king......" hannu biyu ya saka ya d'ago ta daga jikin sa ya kalli face d'in ta yace, "leave me pls."
"I can't, ina so na kasance dakai a ko yaushe" ta fad'a kamar zatayi masa kuka ya zagaye ta ya wuce ya bud'e inda kayan sa suke ya d'auko dogayen kaya milk colour ya juyo ya kalle ta suka had'a ido ya d'auke kansa domin shi kam bazai iya saka kaya a gabanta ba.

       Kamar tasan tunanin da yake yi sai ta fita ya girgiza kansa zuciyar sa wani iri babu dad'i domin bai san ya zai mata ba baiga kuma laifin ta dan tana neman hakkinta a wajan sa ba dalilin da ya saka yake jin sa wani iri kenan kamar ya tauye mata hakki. Yana tsaka da shiryawa unexpected yaji an kashe hasken d'akin an fad'a jikin sa a guje an fashe da kuka mai tsuma zuciya.
"Oh my god!" Ya furta a hankali yana jin yadda take shafa k'irjin sa sam hakan baya masa dad'i.

Jin abin nata yana neman wuce gona da iri ya fincike ta daga jikin sa yace, "I said leave! Baza ki samu abinda kika so ba so please ki barni" ya fad'a yana kallonta yana k'ok'arin gifta ta ta rik'e hannun sa tace, "Why zan k'yale ka? Bayan kasan ina neman hakkina a wajan ka."
"Nace baza ki samu ba, sorry please" yana fad'a ya fita ya k'yale ta ta zube a akan gadon tana girgiza kanta a zuciyar ta tayi aniyar bazata bari yau d'in nan ta wuce ta ba.

       D'akin kusa da wanda ya fito ya shiga ya jingina da bango yana sauke numfashi haka kawai ana neman yi masa fyad'e, sai da ya daidaita kansa ya dafe kansa da yake masa ciwo duk abin nan da ya faru ko kaɗan baiji wani da zai tabbatar da yana cikin wani yanayi ba kawai haushin yarinyar yake ji shiyasa baya so ta rab'e amma bawai dan yana cikin yanayi da baya son hakan ba, ya furzar da iska yana kallon kansa a mudubi yana tuna lokacin da lalaurar ta same shi rana tsaka ba tare ya shiryawa haka ba. Zama yayi a kan stool na mudubi rigar sa da take hannun sa ya saka ya sunkuyar da kansa ya rasa tunanin ma me zaiyi.

_Ko wanne yanayi take ciki yanzu?_ya furta a zuciyar sa sai yaja k'aramin tsaki ya dafe kansa da hannayen sa duka biyun, duk da baya sonta ko kad'an amma matar sace tana da hakki a kansa ko wanne yanayi ta shiga shine ya jawo gashi bashi da damar sauke mata wannan hakkin.  Bai san adadin lokacin da ya d'auka yana tunanin ba ya tashi yana so ya fita amma baya so su had'u dan bai san me zaice mata, fasa fitar yayi ya kwanta a kan gadon badan yana jin bacci ba.

        *Monday.*

     Babbar fadar mai martaba sarki Asad ta cika maqil da hakimai wajan fadar bak'i ne manya da yara an cika kowa yana neman hanyar da zai bi yaga sarki. Asad yana zaune a kan kujerar da babu wanda yake zama sai ka kasance sarki a wannan gari an cika gefen sa dogarai biyu ne suna yi masa fifita, k'asan sa shamakin sane d'aya b'angaren kuma babu kowa wajan zaman Waziri ne kuma ba'a ganshi a wajan ba.

Camera ce a kansa ta ko ina yayi gyaran murya kowa yana sauraron abinda zaice yace, "Alhamdulillah, muna godewa Allah ya nuna mana wannan rana cikin k'oshin lafiya da kwanciyar hankali. Ina rok'on Allah yadda ya nuna mana wannan rana lafiya ya had'a mu da alkhairin da yake cikin ta."

Aka amsa da Amin yayi shiru kafin yace, "A matsayina na sarkin wannan gari nayi alqawarin d'aukar nauyin duk wani wanda yake k'arkashin garin nan. Mace, namiji, yaro da babba mai kud'i da talaka, bazan yi cuta ba bazan amince ayi cuta ba da izinin Allah."

Shiru yayi jin yadda kansa yake bala'in harbawa ya lumshe idanu ya bud'e ga rawanin da yake kansa ya k'ara masa ciwon kai ga kayan zafi a jikin sa dan riga ma guda uku ce a jikin sa kuma manya hakan ya sake rud'a shi ba kad'an ba, "Allah yaja zamanin Sabon sarki, Allah ya karya mak'iyan ka ya datar dakai ga duka abinda ka saka a gaba!" Aka furta da k'arfin gaske daga can k'arshen fadar.

        "Duba da yanayin da ake ciki na rashin abinci munyi alqawari da aljihun mu bada aljihun gwamnati ba zamu bunk'asa sadakar da ake yi kullum domin wanda basa samu su amfana, zamu rarrbawa mutane maza da mata jari dan su dogara da kansu, za'a bud'e makarantu na koyan sana'a ga mata da maza in sha Allah."

"Allah ya amince maka amintattacen sarki mai zuciyar alkhairi, Allah ya dafa mata zab'ebben sarki mai zab'in alkhairi, Allah ya baka ikon ganin bayan mak'iyan ka!" Dogarai suka sake fad'a aka amsa da amin.
Chapter 50 · 0% Book details