← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 131

Sashe 80

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suhaima ta fara hawaye tace, "Wallahi ko magen Mama bazan iya bawa guba ba balle Maman da kanta." Hydar ya fusata yace, "bance miki ke kika zuba ba malama, tambayar ki nake ya akayi tasha guba?!" Ya fad'a a k'arfi yana kallon ta idanun sa a waje.

Kasa magana tayi kawai sai ta fashe da kuka yaja dogon tsaki ya barta a wajan ya fita ma daga asibitin gabad'aya zuciyar sa duka babu dad'i.  Suhaima d'akin da Mama take kwance ta shiga ta ganta a kwance an saka mata ruwa yana shiga jijiyar ta idanun ta a kulle farin abun ya daina zuba daga bakin ta, zama tayi a gefen ta ta rik'e hannun ta da babu allurar a jiki tana hawaye har lokacin d'aci take ji in ta tuna kalaman Hydar a kanta.

       Bata san ya Hydar sukayi da Dr ba basu kuma had'uwa ba sai da safe sai da gari yayi haske ma Suhaima tayi sallar asuba duk ta k'agara ta koma gida sabida bata jin dad'in jikin ta ga makaranta zata je da azahar. Tana zaune a gefe taga Maman ta buɗe idanunta ta k'arasa wajanta a guje tana fad'in, "Mamana kin farka." Mama ta buɗe idanun ta sai ta fara tari da sauri Suhaima ta fita zuwa wajan Dr ta ganshi a tsaye dashi da Hydar tace, "Dr ta farka."

Tare suka shiga da Hydar d'in ya samu Maman tana ta amai a kwance Suhaima ta sake fashewa da kuka tace, "Dr amai take yi fa." Dr yace, "kwantar da hankalin ki aman shine samun lafiyar ta daman shi muke so tayi ta amayar da poison d'in gabad'aya."

Hydar ya kalli Maman ya kalli Dr yace, "yanzu ya aka gama binciken?."
"Kamar yadda na fad'a maka a cikin shayin aka zuba mata poison d'in tasha, yanzu abinda za'a mayar da hankali wanda ya zuba mata poison d'in." Hydar ya girgiza kai yace, "Yanzu ya jikin nata?." Dr ya k'arasa kusa da Mama da ta mik'e zaune idanun ta a kulle yace, "Ranki ya dad'e ya k'arfin jikin?." Kai ta d'aga kawai tana cize baki hannun ta rik'e da cikin ta.

Hydar ya kalli Dr yace, "Da alama cikin ta nayi mata ciwo." Dr yace, "Ai dole daman in ka duba a cikin ta poison d'in take, yanzu Suhaima ki taimaka mata ta tashi tayi wanka ta kuma sha tea mai zafi sosai." Kai kawai ta girgiza Dr ya fita ta share hawayen ta Hydar ya kalle ta yace, "Ga kayan Maman a jaka, a office d'in Dr sai ki karb'o mata tea" yana fad'a ya fita Suhaima ta bishi da kallo.

        Taimakawa Maman tayi ta tashi tsaye dak'yar ta suka k'arasa band'aki ta fito ta barta Maman tayi wanka ta wanke baki ta fito ta shirya ta zauna tayi sallar asuba a zaune bayan ta idar Suhaima taje office d'in Dr ya nuna mata kettle ta d'ora mata tea ta had'a a cup ta tawo mata ta karb'a tasha dan taji k'arfi a jikinta. Tana cikin sha Hydar ya shigo ya zauna kusa da ita yana kallon ta ganin ta samu lafiya sai yaji dad'i da abubuwan sun masa yawa shima ga mai martaba a kwance ga Mama ga Asad ya zama abinda ya zama ga Aliyu baya nan.

Mama tace, "Sannu Hydar, Allah yayi muku albarka." Suka amsa da amin Hydar yace, "Amin, Allah ya baki lafiya Mama." Mama tace, "Amin." Hydar yace, "Mama poison aka baki a tea fa kika sha."
Tayi murmushin takaici tace, "na san za'ayi haka Hydar, masu neman su kashe ni ai suna da yawa."
"Mama daman an san da hakan shine ba'a fad'a min ba? Da sun kashe mana ke fa shikenan."

Mama tace, "kwantar da hankalin ka nasan shirin bazai wuce na Sadiya ba, Suhaima daman taji Jidda tana waya suna cewa sai an kashe ni, ku barsu su kashe ni d'in kawai ma yafii min zaman duniyar."

Suhaima da Hydar suka kalli juna sannan suka kalli Maman Hydar yace, "Mama me kike cewa ne haka? Mun san da nufin ta a akan ki kuma mu zuba mata idanu?." Mama tace, "to muna da hujja ne?."
"Zamu nemo hujjar Mama tunda har ta furta zata iya aikatawa, wataƙila jiyan ma ita ta saka aka zuba miki guba a tea ni kuma ina zuwa na d'ebo ban sani ba" Suhaima ta fad'a kallon Maman.

Mama ta tab'e baki zuciyar ta na rawa tace, "a barshi dai kawai kome ya faru nice na jawowa kaina da ban bata dama ba da duk hakan bata faru ba. Asad baya son auren jidda na takura masa a kai wacce yake son zama da ita na raba su" ta dafe kanta da yake ciwo tace, "ku k'yale ta kawai abubuwan da suke gabana yafi wannan, burina Asad ya dawo hankalin sa, Aliyu ya dawo, mai martaba ya samu lafiya shine abinda na saka a gaba. Suhaima ina so ma zaki koma wajan Malamin nan da ya bamu maganin nan na k'arshe" ta fad'a tana dafe kanta cikin ta yana juyawa.

"Baza'a bar maganar nan ba Mama!" aka fad'a daga bakin k'ofa duk suka juya jin muryar wanda basuyi zaton jinta ba suka ganshi a tsaye cikin k'ananu kaya fuskar sa babu walwala. K'arasowa ya yake yi ya canja yanayin fuskar sa yana murmushi ya durk'usa a gaban Maman yana kallon ta itama shi take kallo yace, "Barka da safiya Mama, ya k'arfin jikin ki?."

Bakin ta rawa yake tana nuna shi da yatsa cikin mamaki da al'ajabi tace, "Asad ko Aliyu?." Murmushi yayi ta rik'e hannun sa yace, "Aliyun kine Mama, taya zaki ga Mai martaba da kansa da wannan shigar kuma shi kad'ai?."

  Mama ta bayyana farin cikin ta tace, "Yaushe ka dawo? Ashe zan kuma ganin ka a duniya?." Murmushi yayi yace, "Gani na dawo Mama. abinda nake ji kuma baza'a bar maganar nan ba, babu wanda ya isa ya bawa mahaifiyar mu guba ya kwana lafiya."

Ya kalli Hydar yana mik'ewa yace, "An tabbatar da tea d'in da tasha akwai poison?." Hydar da yaji dad'in dawowar d'an uwan nasa yace, "Akwai, bincike ya tabbatar akwai a ciki."
"Suhaima lokacin da kika shiga kitchen wa kika gani?."
"Babu kowa Yaya Aliyu, Amma ruwan a ajjiye yake a cikin kettle kawai dafasa shi nayi."
"You're not serious Suhaima, baki san wanda ya zuba ruwan ba kawai zaki d'auka ki bawa Mama.....?" Sai ya dafe kai yace, "Oh god" ya fad'a yana runtse idanun sa.

Suhaima tace, "Ina so naga taci wani abun ne a lokacin shiyasa." Aliyu ya kalle ta yace, "Duk abinda ya faru kece sila, kuma zaki shiga cikin wanda zan sakawa question mark." Mama da take ta kallon sa tana murmushi tace, "Sai kake min yanayi da Asad Aliyu, musamman yadda kake magana kana tsayawa kamar shine yake magana haka nake ji." Tausayin Maman nasu ya kama su dukkan su dan sun san tsananin kewar sa da take yi ne ya saka take jin hakan.

Aliyu bai magana ba ya tashi kawai ya fita dan bazai bar wanda suka kusa kashe masa uwa su kwana lafiya ba. Dan shi kaf cikin plan d'in sa babu kashe Mama. Lokaci d'aya sai Mama taji dad'in jikin ta ganin addu'ar ta biyu ta karb'u har Allah ya biya mata saura guda biyu da take jiran tabbatuwar su. Basu jima sosai a asibitin ba tace sai an sallame su ganin taji sauk'i sai ciwon cikin kad'an-kad'an sai aka sallamo su suka dawo gida.

        Aliyu gida ya koma sai a ranar ya shiga cikin masarauta ya tattara gabad'aya ma'aikatan b'angaren Mama ya saka su a gaba yana kallon ko waccen su yace, "Wacece k'arshen aiki a kitchen d'in Mama jiya?." Suna durk'ushe dukkan su duk sun tsorata dan sun san hali ba kirki ne dashi ba d'aya tace, "Nice ranka ya dad'e."

Ya hard'e hannu a k'irji yana kallon ta sai ta sunkuyar da kai yace, "ke kika zuba ruwa a kettle d'in da ake dafa tea?." Kallon sa tayi suka had'a ido yayi mata mugun kwarjini ta sauke kai yace, "Duk wacce tayi min k'arya wallahil azimi saina hukunta, kun san halina."

"Ranka ya dad'e nidai na gama gyara kitchen d'in amma ban zuba ruwa a butar ba" ta fad'a kanta na k'asa ya kalle su yace, "Wacece ta zuba a cikin ku?." Duk sukayi shiru ya girgiza kai yana kad'a k'afar sa yace, "in na sake maimaitawa sai kunyi kuka." D'aya daga ciki tace, "Nice ranka ya dad'e, amma wallahi ban zuba komai a ciki ba ruwa kawai na tara a fanfo na zuba na ajjiye kuma bada niyar wani abun nayi ba."

"Nace daman an zuba wani abun ne?" Ya jefe ta da tambayar muryar sa a can ciki dan in baka nutsu nama baza ka san me yace ba yana kallon ta. Tayi shiru ya kuma cewa, "Bayan ku waye ya shigo?." Suka had'a baki suka ce, "Babu kowa."
"Kenan dai a cikin ku wata ta zuba gubar a ruwan."

Sun tsorata matuk'a jikin su sai rawa yake ya girgiza kai yace, "Better, zan saka a kulle ku yanzun nan then ayi muku bulala goma sannan ku share harabar gidan nan gabad'aya, in kun gama sai mu sake zama muji wacece tayi a cikin ku."

Kafin suyi magana yace, "kana ina!." A guje dogarai biyu suka shigo yace, "aje ayi musu hukunci kar a k'yale su har sai rana ta fad'i" yana fad'a ya tashi zai bar wajan suka rushe da kuka d'aya tace, "Dan girman Allah ranka ya dad'e kayi hak'uri kayi mana rai, nidai wallahi ban san komai ba ban aikata komai ba kuma."

Ko kallon su ma baiyi ba ya wuce abinsa aka tasa kewar su dan su karb'i hukunci ko wacce cikin su kuka take yi dan hukuncin da ya zayyana bamai sauki bane ba.

     Ba jimawa su Mama suka dawo ta tarar b'angaren nata babu kowa hatta jakadiyar ta ladidi bata nan suna zaune a k'aramin falon Aliyu ya shigo ya zauna a kusa da k'afar ta kamar yadda Hydar yake a gefe tace, "Ina hadiman nan suke?." Aliyu yace, "na saka ayi musu hukunci sai sun fad'a min wacece ta zuba poison a tea."
Chapter 80 · 0% Book details