← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 131

Sashe 44

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin harabar gidan y'an mata ne y'ay'an masu kud'i kai da ka gansu da wayoyin hannun su kasan ba y'ay'an talakawa bane. K'atuwar banner ce a manne a bango anyi mata ado da balloons a jikin banner d'in an rubuta _welcome to Jidda's bridal shower_ an had'a da k'aton hoton ta da yayi kyau sosai kanta babu d'ankwali kamar ba y'ar musulmai ba.

An yiwa gidan ado an zuba kujeru ana kid'a ga kayan ciye-ciye da shaye-shaye kamar kamar an dad'e ana tsara abin. Rawa suke matan cikin pink d'in dogayen riguna amaryar kuma ta saka blue mai haske kanta babu d'ankwali ta nad'e gashin ta tayi bala'in kyau kamar ba ita ba sai chasar rawa suke ana hotuna da video.

Tun k'arfe takwas suke rawa ana kid'a har k'arshe sha d'aya a lokacin suka fara watsewa da nufin sai gobe za'a kuma had'uwa masu decoration suka cire kayan su kowa ya kama gaban sa. Jidda da Eman  bayan sun cire kwalliya an kwanta a gefe ana ta sauke numfashi gajiya Mum ta shigo tana fad'in, "kun sha rawa ai dole ku gaji ai." Eman tace, "Sai ma gobe ai Mum, daman ma abin yazo mana a haka da wlh event biyar zamuyi."

Mum tace, "Allah ya kaimu goben, tunda ba'a nan zakuyi ba kuje ku k'arata." Eman tace, "Mum muna so fa gobe Asad yaje dinner d'in kinga ba'a yi dinner babu ango ba." Jidda tace, "abinda yake raina kenan kika riga ni fad'a, in bai je dinner d'in nan gobe ba an gama wulaƙanta ni a idanun k'awayena." Mum ta rik'e k'ugu tace, "Amma dai kin san Asad bazai je wajan dinner ba ko? Kamar kin san halin sa basai an fad'a miki ba."

"Amma Mum wannan ai bikin sane yana da kyau ya ajjiye duk wata halayyar sa ya bari ayi shagali, in fa ranar ta wuce baza ta sake dawowa ba har abada." Mum ta kalli Jidda da take maganar tace, "Kar ki sakawa zuciyar ki domin ba zuwa zaiyu ba na tabbatar, kar abin yazo ya dame ki gwara kar ki saka rai." Eman tace, "Sai mu had'a shi da Mama dan baza mu bari a dinga munafurcin bikin mu kamar yadda muke na wasu ba."

Mum tace, "ku kuka sani dai nidai na fad'a muku" tana fad'a ta fita ta barsu. Jidda tace, "Eman bafa zan bari hakan ya faru ba gaskiya." Eman tace, "Ina bayan ki dole mu san abinda zamuyi." Daga haka suka cigaba da tsara yadda abu zai tafi kafin goben.

      Kamar yadda suka tsara washe gari Thursday tun safe k'awaye ta suka cika gidan aka sake k'aramin event mai taken henna party aka yi musu henna zuwa azahar aka fara make up bayan la'asar sun shirya dukkan su magriba ake jira a tafi wajan event. Duk wata hanya da Jidda tasan zata bi Mama ta saka Asad yazo tayi amma hakan babu nasara domin ta sanar da ita bazai zo ba tayi taron ta ita kad'ai kawai gabad'aya hankalin ta ya tashi.

Magariba tayi k'awaye aka fara tambayar zuwan ango duk taron ya fita a kanta ta fara k'ok'arin kuka sabida a ganin ta ba k'aramin wulaƙanci bane rashin zuwan sa. An firfito harabar gidan Jidda tayi kyau cikin gown ash colour an yi mata mayafi mai adon kalar fabric d'in  a jiki yana jan k'asa sosai, tayi kyau ba kad'an ba henna hannun ta red and black ya haska fatar ta in ka kalle ta sai ka kuma sabida kyaun da tayi, fuskar ta a cushe babu walwala kana gani kasan ranta a b'ace yake daurewa kawai take yi. Babbar k'awar ta Farha tace, "Jidda kince yana hanya yana ina? Ana can fa an cika jiran mu kawai ake yi?." Idanun ta suka ciko da kwalla zatayi magana kenan ash d'in mota kirar benz ta danno hancin ta cikin gidan ta haske su da fitar motar.

Kowa sai da ya kalli motar sabida kyaun ta da yadda aka d'auki hankalin su aka k'i bud'e koda tagar motar Eman ta kalli Jidda itama ta kalle ta Eman ta fara takawa zuwa gaban motar ta kwankwasa glass d'in tana jira a sauke taga waye. Zuuuu aka sauke glass d'in motar ba Eman kad'ai ba hatta Jidda da take tsaye a baya sai da gabanta yayi mugun fad'uwa suka zaro idanun su waje cikin d'inbun mamakin wanda suka gani zaune a cikin motar..........
[17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*048.*

        Eman baya tayi farin ciki ya cika zuciyar ta da fuskar ta lokaci d'aya hakan ya bayyana a gare ta domin basu tab'a tunanin ganin sa a wannan lokacin ba ta kalli Jidda cikin iyayi da yanga da nuna sun isa tace, "Sis your groom is here." Jidda tayi b'oyayyiyar zuciyar nan take fara'a ta bayyana a tare da ita ta fara takawa a hankali da niyar nufar motar.

K'awar ta d'aya ce ta rik'e mata hannu tace, "Eman kice masa ya fito muyi pics before muje can please." Eman ta kalle shi a lokacin glass d'in motar yake kallo tace, "prince can u come out please?." Agogon Rolex d'in hannun sa kalar golden ya kalla ya kalli Eman ya sake d'auke kansa alamun bazai fito ba. Eman ta kalle su tace, "yace dare yana yi kuzo in an je can ayi hotunan."

Jidda ta tako ta bud'e gaban motar ta shiga k'awayenta suka gyara maza zaman mayafin nata suka kalle shi suka ce, "Ango harda sha mana khamshi? Duk da yadda bikin naku yazo without mun shirya komai muka zo akayi abu kamar an jima ana shiri amma shine baza ka fito ba?." Kallon ta yayi kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa yayi murmushi kawai da ya tafi da hankalin su dukkan su.

Kulle k'ofar sukayi ko wacce ta shiga tata motar ya fara juya motar ya fita suka biyo bayan sa. Kallon sa Jidda take yi kawai cikin zallar mamakin ta yadda akayi ya amince har ya fitar da ita kunya haka amma ta kasa magana sai murmushi da take yi cikin farin ciki.  Shi kuma gabad'aya khamshin turaren ta ya addabe shi nema yake ya dagwagwala masa lissafi hakan ya saka baya kallon ta driving kawai yake hankali kwance.

     Kallon sa ta kuma yi sanye yake da shadda fara sai maiko take tana d'aukar ido hular kansa brown kalar aikin jiki yayi kyau sosai ba kad'an ba kamar ka sace shi ka gudu.  Juyowa yayi suka had'a ido ya d'aga mata gira d'aya ya kyalkyale da dariya kana yace, "Amaryar Prince Asad ko nace his princess, kinyi kyau fa sosai ba kad'an ba but turaren ki yayi yawa" ya fad'a yana cigaba da tuk'in sa.

Ras ras rasss gaban Jidda ya fad'i yadda yayi maganar ya tabbatar mata da Aliyu ne ba Asad ba ta dafe k'irji tana binsa da kallon mamaki tace, "Aliyu!." Ya kalle ta yace, "Yeah Jidda."
"Daman kaine ba Asad ba?."
"Yeah nine, kema kin san ko za'a sake haifo ki ne Asad bazai zo ba dalilin da ya saka Mama tace kiyi hak'uri kenan."

Kai ta dafe fuskar ta ta canja gabad'aya ta kalle shi tace, "kai kuma shine ya turo ka kenan ko kai ka turo kanka?." Ya d'aure fuska kamar ba shi ba shine ya gama dariya ba yace, "ni na turo kaina dan na taimake ki, kamar ki ace anyi bikin ki dinner babu ango akwai disgracing da yawa a cikin lamarin, time d'in da kuke waya da Mama naji komai na kuma yi niyar taimaka miki but in bakya so zan k'yale ki ne."

Jidda ta sauke numfashi tace, "Na gode ka taimake ni amma yau sak ka koma min Asad har acting din rashin maganar sa kayi." Yayi murmushi yace, "Ina sane nayi hakan." Hannun ta ya rik'e yana murzawa kafin ya kai hannun sa bakin ta yayi mata kiss a hannun ta k'wace tace, "nifa matar k'anin kace ka dinga controlling kanka mana." Murmushi yayi mata kawai ya cigaba da tafiya har suka zo inda suke so.

A nan aka fito ya fito shima suka tsaya shida Jidda ana hotuna kamar daman hoton akazo yi, sai daga baya aka shiga wajan taro da ya cika da k'awaye da yayyen k'awaye Mum harda Suhaima tunda taga shigowar su tasan ba Asad bane sai dai Aliyu dan yanayin rawar kan kawai ya nuna mata hakan dan tasan ko za'a yi ruwa da kankara Asad bazai zo ba. Sun ci sun sha sun kuma sha rawa abinsu anyi hotuna kamar babu gobe kafin kace kwabo hotuna sun zaga duniya.

Sha biyu na dare suka tashi kowa ya koma gida Jidda taji dad'in bikin domin kuwa kaf k'awayen ta tasan babu wanda ya d'auko kyau da kud'i da mulkin Asad sai ita kawai, sunga Aliyu sun rikice gabad'ayan ina ga sun ga babbar giwar Asad? Duk da kamar d'aya ce amma akwai banbancin class.

Facebook, whatsapp, Instagram, Twitter da sauran su kafin kace kwabo hotunan sun yad'u kana bud'e wayar ka ka shiga da abinda zaka fara karo kenan hotunann Aliyu da Jidda a jikin ko wanne an saka prince Asad and his princess Jidda. Mum ma kafin su dawo a nan taga hoton tun da ta gani itama tasan sai dai aikin Aliyu bana Asad ba ranta ya b'aci matuk'a jira take Jiddan ta dawo tayi mata fad'a.
Lokacin da suka dawo kamar jiya kwaliyya aka goge ana cire kaya ita dasu Eman da sauran cousins d'insu da suka tawo tare Mum ta shigo d'akin ta kira Jiddan ta fita.

A d'aki Jiddan ta same ta tana fad'in, "Mum na gaji bacci zanyi fa." Mum tace, "ashe bki da hankali ban sani ba Jidda?." Da mamaki tace, "me nayi Mum?."
"Baki san ma me kika yi ba kenan ko? Dan baki da hankali an fad'a miki halin Asad akan kishi amma kika gayyato Aliyu yaje ya tsaya a gefen ki kamar shi zaki aura ko? Kalli wannan hoton har hannun ki ya rik'e, meyasa bakya gudun matsala ne kewai?, kin san da yadda auren nan zai yu kuwa?."
Chapter 44 · 0% Book details