← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 124 OF 131

Sashe 124

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin kalmar da ta fad'a mutane basu da tausayi da imani sai ya sake yin murmushi yana sauke numfashi yana kallon hannunta kamar me ganin wani abun a hannun nata dan ya kula lokacin da Abba ya fad'i wasu maganganun a taron da akayi duk bata ji ba da alama bata hankalin ta a lokacin kafin yace, "Mama ce!" Ya fad'a yana kallon ta sai yaga ta sauke idonta k'asa bata ce komai ba.

Murmushi yayi yana jin kansa na mugun ciwo amma baya so yayi shiru yace, "Inda tasan akwai idda a kanki a wannan lokacin saki uku zata saka ayi ba saki d'aya ba, dogoranta akwai aikin shine ta amince da saki d'aya" ya fad'a yana murmushi kana kallo kasan murmushin takaici ne da bakin ciki.

Shiru ya sake yi itama tayi shiru aka rasa mai magana a cikin sa yayi baya ya kwanta ya dafe kansa da guda hannayen sa yana ji kansa yana juyawa amma yafi so ya bayyana mata komai ko hankalinta zai kwanta ta daina jin haushin sa shiyasa ya zab'i ya cutar da kansa ta hanyar yin magana mai tsaho badan yana so ba.

"Naso na sanar dake a can ban samu dama ba Mama tazo, daga nan ban sake samun lafiya ba sai da naje Madina daga Bahrain nayi addu'a a Rauda nasha maganin karya asiri da dama a can, manyan malamai suka bani magani da addu'ar tsari a wannan lokacin na fara jin sauk'i a jikina ina jin son dawowa gida yana shiga raina a hankali."

Shiru ya sakeyi ta kafa masa ido tana kuka sosai yana jinta amma bazai hanata ba shima kukan yake so yayi hakan ya saka shi yin shiru kawai baice komai ba. Ya sake d'aukar dogon lokaci kafin yace, "Ranar da abin ya faru shine ranar da aikin ya karye a kaina gabad'aya, a sannan na tabbatar na samu lafiya amma sai kika d'auki abin ba daidai ba, kika kirani mazinaci Muwaddaty, har kika d'auki hannu kika mare ni."

Ta kalle shi yana kwancen idanun ta suka cigaba da zubar da ruwa zatayi magana ya d'aga mata hannu ya sake tashi zaune ya hard'e hannayen sa waje d'aya yana kallon k'asa kafin yace, "Naji zafin kalmar Muwaddaty ba'a tab'a kirana da makanmanciyar ta ba tunda nake a duniya sai a kanki, banji ciwo da zafin marina da kika yi ba amma naji zafin kalmar ki, naji b'acin rai sosai a ganina kina sane baki da wata hujja kin fad'a ne dan ranki yana b'ace akan abinda nayi miki. Daga ranar nace bazan sake neman ki ba tunda kika ce min haka......" yayi shiru ya furzar da iska daga bakin sa ya kulle idanun sa na wani lokaci.

Shiru ya sake ratsa su sai jan numfashin Rauda ake ji ya juyo ya kalle ta ya d'auke kansa ya sake yin shiru kamar bazai yi magana ba kafin yace, "Ina sonki dalilin sonki ya saka na kasa daina neman ki, na shirya ba tare da kowa ya sani ba na tawo gidan ku amma sai na kasa zuwa sbd kunyar su Baba, a nan naga kannen ki k'aramin Khalil shine yake fad'a min abinda ya faru."

Ta kalle shi shima ya kalle ta sai yayi murmushi ya d'ora hannun sa kan cikinta ya matso sosai kusa da ita har tana jin numfashin sa mai zafi da yake fita ya dafe kai da hannu d'aya, hannun sa ta cire ta d'ora akan fatar goshin sa taji zafi sosai jijiyar kan tana ta harbawa ta kalle shi taga ya had'd'iye yawu yace, "hankalina ya tashi da naji yace Baba yana dukan ki dalilin zuwana kenan dan nasan nine silar komai."

Kai ta sunkuyar hawayen ta na zuba akan hannun sa ya shafi hannun sa yana murza ruwan hawayen nata yayi shiru baice komai ba tana kuka tace, "Ban d'auka akwai auren ka kaina ba a wannan lokacin Allah ya sani, banyi dana ci maka fuska ko naci mutuncin ka ba; wallahil azim da gaske na d'auka na aikata Zina ne shiyasa hankalina ya tashi na rasa me yake min dad'i. Ban tab'a sanin kowa ba sai kai ka rabu dani kuma na ake sanin ka sai nake jin k'yamar kaina na gwammace ma wai daban ne ba kai ba. Kayi haƙuri!" ta fad'a tana kuka sosai ta kifa kanta akan hannun sa.

Murmushi yayi yace, "Na zama silar abubuwa da yawa a rayuwar ki Muwaddaty, tun farkon shigowata rayuwar ki abubuwa suke faruwa dake marasa dad'i, sau da dama ina jin ina ma ban shigo rayuwar ki ba na barki ki huta kamar kowa amma k'addara ta riga fata. Abinda ya sake k'ona min rai na rantse da Allah akan ban sake ki ba amma kika shafawa idanun ki toka kina ganin kamar zan rantse akan k'arya ne sabida wani burina."

"Kayi haƙuri, dan Allah ka yafe min wallahi banyi ina sane ba duka nayi ne dan kare mutuncin kaina amma bawai dan na wulaƙanta ka ba. Kayi haƙuri ka yafe min dan Allah!."

Yayi murmushi kad'an jin yadda take kuka ya cize baki yace,  "Akan gaskiyar ki kike Muwaddaty banga laifin ki ba ina fad'a miki abubuwan da banji dad'in su bane amma badan ina jin haushin ki ba."
"Kaima akan gaskiyar ka kake Sultan nice na kasa fahimtar ka duk da dole kaina ya kulle sabida abubuwan da suka faru bazan yi saurin fahimta da wuri ba. Kayi haƙuri ka yafe min dan Allah. Ka kuma yi min duk abinda kasan zaka wuce akan marin da nayi maka wallahi nayi dana sani."

Fatar cikin ta ya murza yana murmushi kad'an amma bai ce komai ba tace, "Kanka akwai zafi sosai fa, ka daina maganar ka huta dan Allah kar ya jawo maka matsala."
"Rabon samun abinda yake cikin ki shine silar faruwar duka wannan k'addarar. Tun farkon had'uwa ta dake abinda ya faru wanda Mama tayi miki ko ni nayi miki dan Allah ki yafe mana dukkan mu."

Kai take girgizawa tace, "Ka daina rok'ona Sultan ni ya kamata na roƙe ka afuwa nayi maka abubuwa da yawa, na kira ka da kalma mara dad'i na jefa ka da munanan kalamai sabida rufewar idanuna, na d'aga hannu na mare ka matsayin ka na shugaba ban duba wannan ba, kayi hak'uri ka yafe min Sultan bazan sake aikata makanancin haka ba in sha Allah."

Janta yayi zuwa jikin sa ya rungume ta sosai a jikin sa ta sake fashewa sosai da kuka yana shafa fatar bayan ta yace, "Ya isa ki bar kuka, amma ki yafe min ki yafewa Mamana, ki yafewa Aliyu ma Muwaddaty dan Allah."

"Ni na yafewa kowa ma har Hydar na yafe masa, kaima ka yafe min." Jin ta ambaci Hydar sai ya matse ta a jikin sa yace, "Ina son Hydar Muwaddaty, ina Qaunar Hydar, ban saba da kowa ba sai Hydar, bani da aboki sai Hydar, bani da d'an uwa sama Hydar. Shine abokin shawarata shine abokin kukana, amma Hydar......!" Sai ya kasa maganar ya kulle idanun sa yana furzar da iska sannan yace, "Har yanzu ina son shi."

Tausayi ya bata sosai ta d'ago daga jikin sa tana kallon sa ganin gabad'aya ya canja tace, "kayi haƙuri duk tsanani yana tare da sauk'i, ka yiwa Hydar addu'ar shiriya da fatan samun nutsuwa da sassaucin abinda yake zuciyar sa. Nasan zaka ji ciwo sabida nima da Hydar na sanka amma kayi haƙuri, haka rayuwa take koda hakan bta faru ba wata rana zaka mutu ko shi ya mutu dole wani ya tafi ya bar wani a cikin ku. Ka kwantar da hankalin ka kaga jinin ka ya hau saka damuwa ba naka bane ba. Na tabbatar shima yana sonka wani abun ne kawai ya rufe masa ido amma in kana mas addu'a sai kaga ya dawo Hydar d'in da ka sani a baya."

Numfashi ya sauke yaji dad'in kalaman ta sosai a ransa ya matse ta sosai ya kulle ido yace, "Ina sonki Muwaddaty, ki daina nisa dani in ba haka ba zan iya rasa raina abubuwa sunyi min yawa kece maganin damuwana. Dan Allah ki zauna tare dani."

"Ina sonka Sultan, ina sonka sosai bzan sake yin nesa da kai ba in sha Allah, kullum ina tare dakai daga ban har aljanna." Yayi murmushi ya sassauta rik'on da yayi mata yana kallon ta ya share mata hawayen fuskar ta da hannu yayi mata alamun da tayi murmushi tayi shima yayi murmushin kafin tace, "Yunwa nake ji, kaina na ciwo." Mik'ewa tsaye yayi sa kuma yayi saurin dafe kansa tare da dafa bango tayi hanzarin Mik'ewa itama tace, "Ka zauna Sultan baka da lafiya."

Kai ya girgiza ya kalli agogo yaga k'arfe d'aya na dare harda wani abun ya k'arasa inda kayan sa suke ya buɗe kaya ne a ciki kamar a gidan yake rayuwa ya d'auko doguwar rigar sa ya k'araso ya saka mata towel d'in ya fad'i ya d'auke ya saka mata hular ta da tazo da ita ya rik'e hannun ta yace, "muje na miki girki."

Jan hannun ta yayi ta turje tace, "Baka da lafiya Sultan, ka dawo ka zauna dan Allah kanka yayi zafi sosai fa." Kai ya girgiza mata ya sake jan hannunta ta sake turjewa ya juyo yana kallon ta ya kama k'ugu zatayi magana ya d'auke ta cak suka fita daga d'akin kai tsaye kitchen d'in gidan suka nufa.
[17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*093*

           Tana jin fitar Suhail ta fito ya kalle ta yaga ta b'ata fuska suka had'a ido sai ya d'aga mata gira yaga ta sake d'aure fuska sai yayi dariya kad'an ya tashi ya d'auki abincin da Suhail ya buɗe yaga abinci ne har kala uku, kallon abincin yaga tayi alamun sun bata sha'awa ya d'auki wanda yaga tana kallo ya kalle ta taga tana kallon sa sai ya mik'a mata hannu ba musu ta d'ora hannun ta man nasa ya zaunar da ita a cinyar sa.
Chapter 124 · 0% Book details