← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 131

Sashe 110

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Basu jima sosai ba suka baro asibitin suna tafiya a kan titi Asad baice komai ba ya zubawa titi ido kawai ba tare da yayi magana shi kad'ai yasan abinda yake zuciyar sa. Abinda ya gani shine ya firgita shi ya kalli Suhail ya masa alama da ya tsaya yaja ya tsaya yana kallon gefe inda yake kallon abinda yake haddasa masa bugun zuciya.

Rauda ce a tsaye a wajan mai siyar da kayan marmari hannunta rik'e da leda da alama ta gama siya ma tana bashi kud'i, ransa yaji yayi mugun b'aci ya zuba mata ido kawai yana kallon ta ya saukar da glass d'in K'asa kasancewar akwai duhu a wajan ba kowa ne zai gane shi ba.  Suhail ganin abinda yake kalla sai shima ya kalli wajan ya ganta sanye da dogon hijjabi har k'asa fuskar ta a buɗe tana k'okarin tsallaka titi.

Titin ta tsallaka ta tsaya tana yatsine fuska alamun gajiya a tare da ita tana kallon titin, Suhail ya kalla baiyi magana ba sai ya juya kan motar yaje daidai da ita ya tsaya amma basu sauke glass ba. K'aramin tsaki taja tayi gaba tana sake kallon hanya Suhail ya sake yin gaba ya sauke glass lokacin ta juyo take idon su ya had'u dana Asad.
[17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*085.*

       Zubewa Mama tayi a k'asa tana kuka sosai mai tsuma zuciya Mai cike da tarin dana sani da nadamar duk abinda ta aikata domin gashi ya k'are a kanta da y'arta.
"Mum!." Da sauri Mum ta juya tana kallon Jidda jin muryar ta ta fita tana kallon ta itama ita take kallo.

Shafa cikin ta tayi ta sake kallon Mum tace, "Mum ina cikina?." Mum ta mik'e ta taso tazo kusa da ita ba tare da tunanin komai ba ta chakumi wuyan Jidda tana girgiza ta kafin ta cire hannu ta tsika mata mari tana fad'in, "Jidda kin cuce ni kin gama dani. Me na aikata miki kika zab'i kiyi min wannan hukuncin? Me nayi miki kike k'okarin saka zuciyata ta buga eh Jidda?."

Jidda ta sake fashewa da sabon kuka duk da ciwon da yake tare da ita tace, "Mum ba laifina bane laifin kine Mum, kece kika d'ora ni akan hanyar aikata duk abinda na aikata. Bana son barin gidan sarauta bana son a daina kirana matar sarki shiyasa na amince da Aliyu tun farkon kaini gidan matsayin matar Asad ba. Ban san wannan ranar zata zo ba da na kashe kaina kafin zuwan ta."

"Ko baki kashe kanki ba ni zan kashe ki Jidda. Na tsane ki wallahi bana son ganin ki dan kin aikata zunubin da ban tab'a ganin wanda ya aikata shi ido da ido ba sai kee!." Jidda ta tashi zaune dak'yar tana cize baki tace, "Da nace a kashe Aliyu da an kashe shi duk wannan bata zo ba, a lokacin in nace miki a kashe Aliyu Asad nake nufi domin munyi agreement da Aliyu akan bazan sake kiran sunan sa Aliyu ba sai dai Asad shi kuma Asad nace masa Aliyu. Mum duk laifin kine da baki d'ora ni akan cuta ba da yanzu ina tare da mijina Asad, ke kika koya min son kai, ke kika koya min kisa, ke kika koya min dukkan abinda na aikata a wajan ki na iya...." a haukace Mum tayo kanta ta fara dukan ta ta ko ina.

Nurses ne suka shigo a guje aka kwace Mum amma tuni Jidda ta suma itama Mum d'in baya tayi ya zube a k'asa suka d'auke ta aka shiga bata nata taimakon haka Jiddan ba.

*☆☆☆*

Washe gari ta kama ranar litinin an gabatar da zaman fada mai aji wanda Asad ya gabatar da zafafan hukuncin da ya yanke wanda zai sake farfad'o da martabar masarautar sa. Duk wani abu da ake yi ba daidai ba an dakatar dashi an sake d'ora masarautar akan tafarkin addinin musulunci da kuma kyawawan ayyuka masu kyau da tsari.

Ranar kowa sai da Asad ya burge shi domin yadda yake maganar ma abin burgewa ne balle kuma hukuncin da ya yanke akan komai ya tsara komai yadda ya kamata.

Bayan an tashi daga zaman fada asibitin da Mama take kwance ya wuce ana tafiya ana jiniya mota hud'u a gaba sannan wacce yake ciki sai hud'u a baya ana gudu akan titi.
Duk a k'ofar d'akin suka tsayaa shida Suhail ne kawai suka shiga ciki tunda ya hango Maman sai kuma gaban sa ya fad'i ganin ta dai tana nan yarda ya barta jiya.

Suhaima ya kalla yaga ta rame lokaci d'aya tayi duhu idanunta ya fad'a ya kalle ta yace, "Suhaima meyasa bakya jin magana?." Ta rausayar dakai dan ta gaji da yin kuka tace, "na kasa bacci ne." Ya furzar da iska a bakin sa yace, "Mama bata farka ba?." Kai ta d'aga alamun eh ya girgiza kansa ya kalli Suhail kamar yasan me yake nufi sai ya tashi ya fita jim kad'an sai gashi da Dr sun shigo.

Dr Yasir ne ya gyara tsayuwa yace, "Barka da zuwa ranka ya Dade." Asad bai amsa ba yace, "ya jikin Mama?." Ya sake saukar da murya cikin girmamawa yace, "Ranka ya dad'e jinin Mama ne ya hau sosai, sannan zuciyar Mama tana bugawa da sauri har muna expecting heart attack ya kama Mama but bamu yi confirming ba. Akwai firgici sosai a tare da Mama dalilin da ya saka har yanzu jinin ta baiyi daidai ba har yanzu zuciyar Mama a firgice take."

Asad ya sauke numfashi ya kalle shi sannan ya kalli Suhaima Dr ma ya kalli Suhaima yace, "Allah ya k'ara maka lafiya itama Suhaima akwai firgici a tare da ita shine ya haifar mata da zazzaɓi amma tak'i zama ayi mata treatment." Asad ya kalle ta ya kalli Dr din sai ya kalli Suhail gnin kallon sai yace, "Ayi mata yanzu Dr duk abinda ya kamata ayi. Sannan zuwa yaushe Mama zata farka?."

Dr yace, "in sha Allah zuwa gobe zata farfad'o, muna so bp d'in nata ne yayi k'asa kafin allurar ta sake ta." Suhail yace, "Ayi duk abinda ya kamata Dr."
"In sha Allah ranka ya dad'e." Asad addu'a ya yiwa Mama sosai kafin a kawo gado a kwantar da Suhaima a kai a saka mata ruwa a gaban sa bacci ya d'auke ta.

Security aka k'aro mace mai uniform aka ajjiye ta da kula da Mama aka saka maza biyu a bakin k'ofa ya bada umarnin ko waye yazo kar a barshi ya shigo suka amsa da girmamawa sannan suka fito suka koma gida.

*☆☆☆*

       Yadda waziri yake kuka sai ka d'auka k'aramin yaro ne har majina ce take zuba daga hancin sa matar sa na tsaye a kansa itama cikin kuka da tashin hankali tana fad'in, "Na rantse da Allah sai ka fad'a min matsafan da ka bawa y'ay'ana suka tsafe akan son mulkin ka na banza da wofi. Wallahi bazan bar maganar nan ba zan kaita gaba wajan human right domin su kwatar min hakkina."

Kuka sosai yake yi zuciyar sa tana bugawa yayi tari yana dukan k'irjin sa kana ya d'ago jajayen idanun sa ya kalle ta muryar sa har rawa take yace, "Yanzu ni kike kalla kike sanar dani na kai y'ay'ana anyi tsafi dasu?." Ta kalle shi tace, "Na fad'a, ai nasan zaka iya ne akan son mulkin ka babu abinda baza ka iya aikatawa ba. Ko ka saka a dawo min da y'ay'ana ko na kai ka k'ara" ta fad'a tana fashewa da sabon kuka ta zube a wajan.

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, kaicona ni Yahuza kaico da masu hali irin nawa na son duniya da k'ok'arin ganin bayan wani.  Yanzu me gari ya waya a gare ni? Na rasa y'ay'ana har guda biyu akan abinda ba addini ba" ya fad'a yana kulle fuskar sa yana kuka mai tsuma zuciya.

"Ban amince da wannan jawabin naka ba, wallahi Allah sai an karbar min hakkina sai an saka min abinda akayi min nida y'ay'ana, bazan amince ba wallahil azim sai bazan bar maganar nan ba kaji na rantse, jira nake a share makoki in kai maganar gaban hukuma" tana fad'a ta tashi ta fita bai iya kallon ta ba ya cigaba da kuka sosai.

Bai daina kuka ba dan kukan daga zuciyar sa yake zuwa shiyasa hawayen idanun sa suka ki tsayawa kuka yake sosai kana kallon sa kasan yana cikin rad'ad'in zuciya da tashin hankali. Ya jima a haka kansa yana sarawa yana yi masa ciwo ya kwanta yana kallon sama.

"Assalamu alaikum, ranka ya dad'e anyi baki daga Kano" wani dogari ya fad'a daga bakin k'ofa. Bai iya d'agowa ya kalle shi ba da hannu yayi masa alama da yaje ya juya ya tafi ya jima kafin ya tashi ya shiga band'aki ya wanke fuskar sa ya fito. Sai da yazo gab da mutanen da suka zo masa gaisuwa jiri sai ya kwashe shi nan take ya zube a wajan a sume.

*☆☆☆*

          Falo na musamman suke a zaune Asad ya kalli mahaifin sa murya a sanyaye yace, "Abba ina neman alfarma." Mai martaba ya ajjiye abinda yake hannun sa ya kalle shi yace, "Ina jinka."
"Ranka ya dad'e alfarma nake nema a madadin Mama, ina rok'on mahaifina da ya yafe mata kuskuren da ta aikata a baya, tana jin jiki yanzu daga can nake har yanzu bata san a inda take ba."

Mai martaba yayi murmushi yace, "Asad babu kai a cikin maganar dake tsakanina da mahaifiyar ka, ina so tayi nadamar dukkan abinda ta aikata da wanda take son aikatawar wannan abun ya faru. Ina so tayi nadamar abubuwa da yawa ta wanke zuciyar ta dukka halayen ta marasa kyau ta ajjiye su a gefe."

Asad yayi shiru har Abba yakai k'arshe kafin yace, "A duba dai Abba."
"Ai kad'an ta fara gani Asad abinda ta aikata ko hakkin matar ka Rauda bazai barta ba balle hakkin sauran mutane. Ni sai ka tuna min ma batun matar taka jibi juma'a za'ayi bikin dawowar ta gidan na shugaba guda bazai yu ya zauna a gidan nan babu mata ba."
Chapter 110 · 0% Book details