← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 131

Sashe 31

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

K'arewa musu kallo Muhibba take yi kafin ta tab'e baki ta k'araso tace, "Ban tab'a karo da couples wanda basu dace da juna ba sai wannan, koda yake maybe akwai manufar da ya saka ya auri wannan abar amma ba so ba" tana fad'a ta wuce su babu wanda ya tanka mata jiran elevator sukeyi suna tsaye.

Elevator ya danna suka shiga suka sauka k'asa suka fita daga asibitin suka shiga mota, yayi niyar su d'an yi yawo but baya jin dad'in jikin sa suka koma hotel suna shiga ya cika hannun ta ya shiga d'aki itama bata damu ba ta wuce inda take. Yana shiga wayar sa tayi k'ara ya duba ganin sunan mahaifinsa ya saka shi zama ya nutsu sosai kana ya d'auka da sallama.

Bayan sun gaisa daga can b'angaren yace, "Zaki nasan zaka samu labari abinda ya faru a nan Katagum, yau dai Allah ya nufa na sauka daga kan karaga na kuma tamk'ata a hannun kawun ka Mubarak shi kuma da zarar ka dawo Nigeria zai baka domin rik'on kwarya aka bashi kaine shugaba ba shi ba." Gaban Asad ya fad'i har sai da ya runtse idon sa ya sauke numfashi a hankali jin hakan mai martaba yace, "ka zauna har matar ka ta samu lafiya Asad, in ka gama komai da ya kaika sai ka dawo kayi abinda nace."

Cikin murya mai sanyi da rawar murya yace, "Amma Abba....." ya dakatar dashi ta hanyar fad'in, "Kayi min alqawari zaka dawo ka karb'i karagar mulkin katagum, kayi min alqawari zakayi k'okarin sassauta wannan dabi'ar taka ta rashin son magana babu ta yadda za'ayi shugaba ya kasance a haka shiyasa nake makaa addu'a a ko wanne lokaci, nasan halittar kace amma zaka iya k'okarin ganin ka d'an gyara wani abun kana shugaba kamata yayi ka zama mai magana akan komai in ka kasance haka na k'asa dakai ya kenan?. Kayi alqawari min zaka canja; kayi min alqawari kome zai biyo baya baza ka hak'ura da karb'ar mulkin nan ba. Zaki kayi min alqawari zaka tafiyar da shugabancin katagum fiye da yadda nake tafiyar dashi, bana jin ka ta b'angaren abubuwa da yawa nasan talakawan ka zasu ji dad'in mulkin ka ko mutuwa nayi nasan na bar su a hannu wanda zai kula dasu ya taimaka musu ya kuma jiqan su. Abu biyu nake ji daman a tare dakai mahaifiyar ka da kuma wannan dabi'ar nan taka ta rashin magana. Babar ka zatayi k'ok'arin ganin ta takwara ka kayi abinda bashi kake son yi ba shima kayi min alqawarin kome zata zo maka dashi indai ya sab'a tsarin ka kar ka amince mata."

Mai martaba yayi shiru kafin ya cigaba da cewa, "kana saurarona Zaki?." Asad muryar sa tayi sanyi yace, "ina sauraron Mai martaba." Mai martaba ya cigaba da fad'in, "komai zaka dawo ka tarar a katagum kayi hak'uri ka jure masa ka fuskanci abinda yake gaban ka. Asad duk runtsi duk wahala karka bari mulkin katagum ya sub'uce maka duk hannun wanda ya fad'a ba kai ba masarautar da wanda suke k'arkashin ta gabad'aya ta lalace, za'a shiga hali mara dad'i a duk sanda mulkin ya bar hannun ka, kayi min alqawarin duk dana roka a wajan ka?." Asad yayi shiru yana tunani ta Ina zai fara gudanar da abin baya so?, ta Ina zai fara mulkar al'umma?, wanne irin sarki za'ayi?, kurma ko bebe?.

"Na Amince Takawa, nayi yiwa mahaifina alqawari in sha Allah zanyi iya bakin k'ok'arina nayi abinda akace, ina rok'on mai martaba daya taya ni addu'a Allah ya bani ikon gudanar da komai cikin ilimi da nutsuwa" ya furta a hankali.

Takawa yayi murmushi yace, "Allah yayi maka albarka Zaki, Allah ya kare ka daga sharrin duk mai nufin ka da sharri, ya baka ikon bawa mak'iyan ka mamaki wanda suke ganin baza ka iya gudanar da sarauta ba ka basu kunya. Ka cigaba da addu'a Asad akwai wanda suna nan suna yi maka mummanan aikin da baza ka kuma dawowa Nigeria ba, amma mu da Allah muka dogara ka cigaba da rok'on sa zai baka kariya a ko ina."

Jin farin ciki a muryar mahaifin sa sai yaji sanyi a zuciyar sa shima yace, "Amin Takawa. Allah ya k'ara lafiya da nisan kwana."
"Amin Zaki, ina jiran dawowar ka nan da wasu kwanaki." Daga haka sukayi sallama ya yanke wayar Asad yayi tagumi yana tunanin ta inda zai fara.

       Bud'e k'ofar da akayi bai saka ya kalle ta ba ta k'araso tana kallon sa ganin gabad'aya ya canja kamar bashi ba tace, "Prince Lafiya?." Sai sannan ya kalle ta ya rik'o hannun ta guda d'aya ya dawo da ita kusa dashi ya zaunar da  ita a akan cinyar sa ya d'ora kansa a wuyan ta d'umin wuyanta yana shiga jikin sa idanun sa kulle yana jan numfashi yana saukewa. Gabanta ya fad'i domin tun ranar da wani abun ya shiga tsakanin su bai sake koda rungume ta da wata niya ba ganin abinda ya faru a yanzu sai taji fad'uwar gaba bashi yadda yake sauke mata numfashi a wuyan ta jikinta sai yayi sanyi.

"Baba ne yace kwana biyu baku gaisa ba" ta furta a hankali ba tare da ta kalle shi ba dan kar ma ya d'auka wani abun ne ya kawota. Sarai ya jita amma bazai amsa bane ya zaga da hannun sa cikin ta ya rik'e ya sake had'a ta da jikin sa zuciyar sa na gudu sosai yana buk'atar rarrashi a halin da yake ciki. Lup dup, lup dup, lup dup, haka take jin bugun zuciyar sa a jikin ta ta kalle shi taga idanun sa a kulle suke har lokacin fuskar sa ta canja alamun akwai abinda yake damun sa.

Kam taji ya rungume ta a jikin sa kamar zai b'alla mata k'ashin baya kafin jikin sa ya fara rawa a hankali zazzab'i ya mamaye fatar jikin sa, zafin taji yana shiga har cikin jikin ta kalle shi gashi ya matse ta sosai ta kasa motsin kirki a jikin sa. A hankali taji ya sassuta mata rik'on ta tab'a wuyan sa tace, "Jikin ka da zafi prince" ta fad'a da kulawa tana kallon sa.

Ya sake ta ita kuma bata tashi ba ta saka hannu ta tallafi hab'ar sa tana kallon idanun sa da suke a lumshe tace, "Me yake damun ka?." Bai magana ba bai kuma bud'e ido ba ta saka hannu ta shafi gashin fuskar sa sai ya bud'e idanun sa da suka koma jajaye ta wara ido waje tace, "me yake damun ka dan Allah?." A hankali ya ya dawo da fuskar sa kusa da tata ya had'a goshin sa da nata ya furta, "Bana so! bana so!."  Yadda bakin sa yake motsawa ya saka tace, "meye baka so?."

A wuyan ta ya sake kifa kansa yana juya fuskar sa kafin ya tsotsar fatar wuyan ta da zafi-zafi, lumshe idanun ta tayi duk da tana jin zafi kad'an-kad'an a fatar ta tana jin sa bata da abinda zatayi ta hana shi sai daga baya ya d'ago kansa ya kalli idanun ta yace, "Bana so, bana so su raba mu dake, kiyi wani abun kar su rabu. Ina sonki Muwadda." ya fad'a a sanyaye tare da lumshe idanun sa yana ji kamar yayi kuka. Nan take taji gabanta ya fad'i jin abinda yace baya so a raba su tace, "Waye zai rabu mu? Meye baka so?, kayi min bayani pls."

Bai amsa mata ba yayi shiru ta sake cewa, "jikinka da zafi sosai kana buk'atar san magani." Kamar zaiyi magana sai yayi shiru ta kasa gane shi ba magani yake so ba kwantar masa da hankali yake buk'atar ayi ba magana ba, da baya ya kwanta ya zama daga k'ugun sa zuwa kansa na kwance guiwyoyin sa suna yadda suke a tsaye har lokacin tana zaune a jikin sa. Ganin yak'i magana sai tayi niyar tashi ba zato taji ya jawo ta ta fad'a jikin sa gabad'aya ya saka hannun sa yana tattare rigar jikin ta. Motsawa tayi zata hana ya sake matse ta sosai a haka ya zare rigar ya saka hannun sa a bayan ta ya b'alle hook d'in brezia ta ta cire ta baya.

Bai juyo da ita ba ya sake matse ta sosai a jikin sa yana sauke numfashi a hankali hannun sa na fatar bayan ta ya rik'e ta gam kamar za'a kwance masa ita. Bata kuma yunƙurin kwace kanta ba tayi lup a cikin sa tana jin yana yawo da hannun sa jikinta.

A hankali take jin saukar numfashin sa alamun yayi bacci ta kalli fuskar sa ta tabbatar yayi baccin sai taji ya bata tausayi a zuciyar ta domin bata gane abinda ya jefa shi a cikin wannan yanayin ba lokaci d'aya. So take ta tashi amma ya hana hakan har lokacin tana rik'e a jikin sa kuma bacci yake yi a haka sai ta mayar da kanta ta kwanta a k'irjin sa itama baccin ya d'auke ta.

      Sun jima suna bacci sai da akayi la'asar ta riga shi tashi ta samu ta zare jikinta bata tsaya mayar da rigar mata ta fita bata son ya farka ya ganta. Wanka tayi ta shirya cikin riga da wando wanda basu kamata sosai ba ta saka dogon hijjabi tayi sallar la'asar bayan ta idar tayi azkar. Yunwa take ji sosai hakan ya saka ta fito falon nan ta same shi ya fito amma kafin su kai ga had'uwa ya fita. Tasan abincin ya tafi d'aukowa ta koma ta zauna sai kuma ta tashi ta had'a tea tana sha domin yunwar ta d'an kwanta kafin ya dawo.
Chapter 31 · 0% Book details