← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 131

Sashe 106

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mai martaba yace, "Sai kace min ka gama yanke hukunci ma tuni. Mahaifinta yazo d'azu bayan jana'iza da alama bai san duk abinda yake faruwa ba amma kawun ka yayi masa bayanin komai tashin hankali ya bayyana a tare dashi amma an sanar dashi ya kwantar da hankalin sa komai zaizo da sauk'i, kai kuma gashi yanzu ka lalata komai Asad."

Shiru yayi ya sunkuyar da kansa k'asa Mai martaba ya kuma cewa, "Ya kake so ayi yanzu?."
"Abba in ana so na d'auki abinda zata haifa zan d'auka har abada bazai san bani na haife shi ba, bayan wannan Abba bana tunanin akwai abinda zan iya."
"Yanzu kenan kana so kace ta fita daga cikin gidan nan matsayin ba matar ka ba?, ka tuna fa kowa kallon matar ka yake mata in akace yau bata nan me mutane zasu d'auka? Shugaba mai sakin aure ko kuma me?."

Asad yayi shiru ya kasa bashi amsa Mai martaba yace, "Mahaifinta ya sanar dani tayi haihuwar wata bakwai sabida rud'anin da ta shiga, kaga kenan yanzu auren ku ya k'are; koda yake daman babu idda a kanta." Shiru Asad yayi ya kasa magana kansa yana k'asa.

Mai martaba yace, "Yanzu ya za'ayi da ita Jiddan da mahaifiyar ta?, tayi yunƙurin kashe mahaifiyar ka ba sau d'aya ba ba kuma sau biyu ba, ita kuma Jiddan taso kashe ka kuma taci amana ta kuma aikata alfasha wanda inda za'a yi mata hukuncin addini da za'a jefe tane har sai ranta ya bar jikin ta." Asad ya gyara zama yace, "A ganina bazata amince da hukuncin addini ba, ni a shawarata kawai a k'yaleta yadda Allah yaji da Uncle Abban Suhail suma zai ji dasu."

Abba ya d'aga kai yace, "Hydar fa?." Asad ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi ya d'ago idon sa ya kalli hasken da yake falon ya sake mayar da kansa k'asa yace, "Ina son Hydar Abba, kaf cikin y'an uwana bani da wanda nake so nake ji dashi kamar Hydar. Zuciyata tana min ciwo in na tuna abubuwan da Hydar ya nufa a kaina sai naji da ina da iko dana goge su" yayi shiru alamun yana so ya d'an huta ne kafin ya cigaba da cewa, "Ina ganin kamar wasa duk abinda suka faru Hydar ne ya shirya sai naji zuciyata tana rawa Abba, bazan iya yiwa Hydar ko wanne hukunci ba a ganina a barshi shima Allah zaiji dashi kamar yadda yaji da Aliyu" ya k'arasa fad'a a sanyaye idanun sa yana cikowa da kwallah.

Tausayin sa ya kama Mai martaba ya d'ora hannun sa a kansa yace, "Zuciyar ka mai kyau ce Asad, shiyasa nake farin ciki da katagum ta mallaki shugaba kamar ka. Kayi hak'uri k'addarar ke kenan y'an uwan ka da kuma babar ka sune k'addarar ka kayi addu'a Allah ya kawo k'arshen wannan k'addarar domin ka samu sauk'i a zuciyar ka. Nasan kana son Hydar shi kuma yayi amfani da son da kake masa ya cutar dakai, har gwara Aliyu daman kowa yasan ba shiri kuke ba amma Hydar naka ne, kayi haƙuri ka fuskanci abinda yake gaban ka domin Hydar bai kyale ka ba."

Hawayen idon sa ya mayar ya danne zuciyar sa yak'i bari yayi kukan yace, "Haka ne Abba. In sha Allah zanyi abinda akace bazan bari tasirin wannan ya hanani gabatar da abinda yake gabana ba. Duk da ina jin tsoro mulki ya sake barin zuciyata, Allah ya k'ara maka lafiya ina ganin kamar mulkin nan zai kawo k'arshen rayuwata ne, bama kaina nake ji ba ina jin Muwadda zasu iya cutar da ita sabida ni" ya fad'a a sanyaye kansa yana k'asa.

Jin sunan da ya kira yasan Rauda yake nufi sai yayi murmushi yace, "Dukkan ku babu abinda zai same ku in sha Allah. Zata dawo gidan nan kwanaki kad'an masu zuwa babu abinda zai faru da kai ko ina da izinin Allah komai ya k'are. Babban tashin hankalina in maganar nan ta baza gidan nan ban san ya abin zai kasance ba. D'ana Aliyu yayi zina da matar aure ya zauna da ita tamkar matar sa, d'ana Aliyu ya had'a kai da maqiya domin ganin bayan mahaifin sa da d'an uwan sa, d'ana Aliyu yayi abubuwa da yawa wanda basu da dad'in ji balle dad'in saurare. D'ana Hydar yaso kashe ni da d'an uwan sa, ya aikata abubuwa masu muni, ya mutane zasu kalli wannan?."

Asad yayi shiru zuciyar sa babu dad'i sosai ya lumshe ido ya bud'e yaji Mai martaba yana cewa, "Amma baza'a bar Hydar ba yayi ta'asar da yaga dama ba, kuma in aka kyale shi yaci banza kenan, in za'a kyale kowa baza'a k'yale Hydar ba dole ayi maganin sa domin har yanzu babu nadama a tare dashi. Shi kuma Aliyu za'a yi masa magani in sha Allah duk sihirin da yake cikin sa zai warware."

Asad yayi shiru mai martaba ya kalle shi yace, "Soyayyar da mahaifiyar ka take yi maka itace ta jawo maka tsana a wajan y'an uwan ka." Asad ya girgiza kai yace, "Allah ya k'ara maka lafiya Mama tafi son Hydar a kaina, tana son Hydar matuk'a shiyasa abinda ake fad'a ya saka ta suma. Burin ta take so na cika mata amma bawai tafi sona bane."

Mai martaba yace, "Kuma ka kasance mai biyayya shiyasa take tauye ka a koda yaushe, bata duba abubuwan da ka bari sabida ita burinta kawai kayi abinda take so."

Mai martaba ya mik'e tsaye shima dole ya mik'e yana binsa a baya Mai martaba yana cewa, "kaje duba maman naka in ka dawo kazo dai ina neman ka." Ya amsa da girmamawa Mai martaba ya tafi shi kuma ya koma da baya dan ya shirya.

Shigar buzaye yayi riga da wando da babar riga ya nad'a rawani kalar kayan ya fito ya sauka k'asa nan ya tarar da masu zaman jiran sa ciki harda Suhail ya bada umarnin mota biyu kawai yake so banda kuma jiniya haka akayi kuwa ya shiga mota suka nufi asibitin.

Lokacin da suk shiga d'akin Suhaima na zaune hannun ta da canular ta dafe kanta, sallamar da akayi ya saka ta d'ago suna had'a ido dashi ta taso a guje ta fad'a jikin sa ta rik'e shi gam sai ta fashe da kuka. Kallon Suhail yayi da yake gefen sa ya kalli Suhaima zuciyar sa ta karye ya saka hannun sa a bayan ta ya bubbuga kad'an yace, "Ki daina kuka Suhaima."

Ta d'ago ta kalle shi tace, "Mama Yaya Asad, har yanzu bata farka ba ko motsi batayi. Babu kai babu Yaya Aliyu babu Yaya Hydar a kusa da ita,in ta farka taga haka zuciyar ta bazata yi mata dad'i ba." Yadda take kuka sosai ya saka shi ya rik'e kafad'ar ta yace, "calm down Suhaima! Babu abinda zai samu Mama Ina tare da ita a ko ina, relax please" ya fad'a yana wuce ta ya k'arasa gaban gadon Mama yana kallon ta.

Gani yayi gabad'aya ta canja kamar ba ita ba ya rik'e hannun ta da babu ruwa a jiki ya zauna a gefe yace, "I'm sorry Mama." Likita ne ya shigo ganin Asad ya saka ya k'araso yana fad'in, "Barka da zuwa ranka ya dad'e." Asad ya kalle shi yace, "Me yake damun Mama?."

Ya kalli Mama yace, "jinin tane ya hau sosai har yanzu bai sauka ba, sannan zuciyarta na bugawa sosai har bugun yayi yawa har yanzu bai daidaita ba hakan kuma matsala ne ga zuciyarta. Akwai firgici sosai a tare da ita shiyasa dole aka yi mata allurar bacci dan ta samu hutu" ya nuna Suhaima yace, "Itama sai da aka bata magani dan ta firgita sosai sai da tayi bacci ta samu lafiya."

Asad ya girgiza kai yace, "in aka fita da ita outside country fa?."
"Ranka ya dad'e ban tari numfashin ka ba, amma duk inda akaje hutu zasu bata dan shi take buk'ata a halin yanzu."
Asad ya girgiza kansa yana kallon Mama da take bacci ya kalli Suhaima yace, "Zauna." Ba musu ta zauna Dr yace, "tak'i zama yadda ya kamata, tana buk'atar hutu itama sosai amma tak'i zama ta huta d'in." Asad ya kalle ta alamun meyasa hawaye ya zubo mata tace, "Bazan iya kwanciya na huta Mmaa tana cikin wannan yanayin ba, zuciyata bugawa take in na tuna abinda aka fad'a d'azu akan Yaya Hydar da Yaya Aliyu. Bazan iya jurewa ba" ta fad'a tana fashewa da kuka.

Likitan ya fita Asad ya rik'e hannun Suhaima duka biyun yace, "Ki daina kuka ki kwantar da hankalin ki komai zai wuce." Kai ta d'aga yace, "wipe your tears." Ba musu ta goge hawayen ta yayi murmushi dan shi yaga k'okarin tama in shine a matsayin ta gani yake sai ya suma sau goma.

Suhail ya kalle shi yace, "Ranka ya dad'e sai nake ganin kamar akwai matsala barin Mama ta kwana da Suhaima tunda dukkan su babu lafiya." Asad ya girgiza kai dan tabbas gaskiya ya fad'a amma bai amince da kowa ba balle ya d'auko hadima d'aya ta zauna dasu, ga y'an uwan Mama duka a nesa balle ya nemi wata a cikin su.

Suhaima ta kalle shi tace, "Babu abinda zai faru zan iya." Asad ya kalle ta yace, "kin tabbatar?." Kai ta d'aga alamun eh yace, "duk abinda ya faru ki kira ni." Ta amsa da to shi kuma ya yi waya aka kawo security mata da maza wanda zasu kula da Maman ya yiwa Mama addu'a suka fita zuciyar sa duk babu dad'i musamman halin da ya tarar da Maman a ciki.

Tunda ya shiga mota ya dafe kansa baya ganin inda suke nufa kawai yayi shiru zuciyar sa na sake hargitsewa in ya tuna abubuwan da suka faru sai yaji kamar ya d'auki bindiga ya harbe kansa, yadda yaga Mama ya sake dagula masa lissafi kuka kawai yake son yi amma babu dama.

Tsayawa yaji anyi duk da hakan bai d'ago ba sai ji yayi Suhail yana fad'in, "Allah yaja da ranka Hydar ne ya tare hanyar." Jin hakan ya saka Asad d'ago kai ya kalli kan titin duk da baya ganowa sosai amma yaga mutum a tsaye ya tare musu hanya. Suhail yace, "Ranka ya dad'e zan ji dashi."
Chapter 106 · 0% Book details