Sashe 29
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kallon ta yayi kamar zai kuma magana sai ya fasa sai yaga ta tashi ta shiga d'aki ta d'auko maganin ta ta dawo ta zauna, k'afar ta yake bi da kallo sai yaga kamar tafiyar ta ba daidai take yi ba hakan ya saka shi binta da kallon har ta zauna kana yace, "Are you okay?." Kai ta d'aga alamun eh kafin yace, "but bakya tafiya daidai ko k'afar ki na ciwo?." Sai gaban ta ya fad'i ta bata ce komai ba domin bata san me zata ce masa ba.
"Answer me." Rauda tasha maganinta bata kalle shi ba sai da ta shanye kamar zatayi kuka tace, "Babu komai."
Yadda ya kafe ta da idanu ko kiftawa bayayi hakan ya bata tabbacin bai yadda ba ta kalle shi sai ta kwab'e fuska tana shirin yin kuka tace, "Babu komai, dan Allah ka bar kallona kunyar ka nake ji wallahi" ta fad'a tana sake mayar da kanta cinyar ta. Sai yayi murmushi amma baiyi magana ba ya k'yale ta kusan mintina biyar yaga ta cigaba da kallon ta amma bata kalle shi ba.
"Kina jin zafin still?."
"Oh my god!" Ta furta a bayyane sai kawai ta fashe da kuka. Hankalin sa ya tashi ya jawota jikin sa gabad'aya ta dawo kan cinyar sa yana so yace wani abun amma kukan da take yi ya hana shi magana. "Please!" Shine abinda ya furta kawai yana shafa bayanta a hankali.
"Ni ka daina min maganar kunya nake ji." Murmushi yayi ya mata kiss a kumatu yace, "is okay, sorry."
Nishad'i yake ji a zuciyar sa in ya ganta a gefen sa sai ya rasa me yake masa dad'i kamar yayi ta kallon ta haka yake ji hakan ya saka shi cigaba da kallon ta kafin yace, "kina son zama y'ar jarida still?." Sai ta d'ago ta kalle shi ganin ba ita yake kallo ba ta wara idanun ta waje kafin tace, "ta ya akayi kasan ina son zama y'ar jarida?." Baice komai bai kuma kalle ta ba sai kallon tv d'in shima da yake yi.
Tace, "Ina da tantama daman ina so na tambaye ka tun ranar nan da naga katin magani na a d'akin ka. Kenan ranar da muka had'u ka d'auka? Kaine ka siya min magani kenan har ka biya bashin maganin da ake bina. Ya akayi kasan Baba yana son keke napep ka siya masa?, yama akayi kasan gidan mu?, meyasa ka b'oye kanka a lokacin?" Bata kallon sa take maganar dan bata so su had'a ido yana jinta amma kuma baiyi alamun da zata gane ma yaji ba balle ta saka ran zai amsa mata.
Shiru ya sake ratsawa a tsakanin su tana jiran amsa shi kuma bashi da alamar bata amsa sai ya murmusa kad'an har taji sautin murmushin nasa ta kalle shi sai taga ya d'auki waya yana dannawa alamun bazai bata amsa ba kenan. Rauda ta d'auke kai bata ce komai ba amma zuciyar ta cike take da son ya bata amsar tambayar ta hakan ya saka tace, "Ka amsa min please, a lokacin da hakan ta faru mun d'auka Anas ne ya bayar sabida shine kawai yake taimaka mana musamman a........" shiru tayi ta kalle shi taga kuwa kallon nata yake kamar yadda taji a jikinta bayan ya had'e fuskar sa waje d'aya kamar ba shine yake murmushi ba.
"Don't call his name again please" ya fad'a yana kallon ta. Kai ta sunkuyar tana mamakin yadda yake nuna yana kishin ta amma a bayyane ya kasa nuna mata soyayyar da take so, dan ita Allah ya sani macece da take so a nuna ana sonta a kula da ita kamar kwai. Shiru tayi bata kuma magana ba amma taci alwashin sai ya bata amsar tambayar ta ko yaushe ne.
"I'm sorry" ta furta a tak'aice tana cigaba da kallon ta.
Wayar sa tayi k'ara ya kalla yaga sunan Aliyu ya sauke numfashi a bayyane yace, "Aliyu!." Har ta katse bai d'auka ba aka kuma kira sai ya saka a speaker ya d'auka daga can b'angaren yace, "Hii Asad baka nema na ko?." Asad ya sauke numfashi yace, "how was your day?."
"I'm fine, ina missing d'inka ne shiyasa na kira ka."
Asad yayi murmushi yace, "thanks you." Aliyu yayi y'ar dariya yace, "kar ka damu. A gaida Madam" yana fad'a ya yanke wayar shima ya ajjiye tasa.
Ta kalle shi taga ba ita yake kallo ba amma sai taji yace, "What up?." Kai ta sunkuyar ya juyo yayi y'ar dariya amma baice komai ba.
"Maganar ku ma tana iri d'aya da Aliyu, ta yaya ake gane ku?" Ta furta ba tare da ta kalle shi ba. Ya shafa fuskar sa ya lura akwai ta da magana a haka ma wai bata da lafiya ya cize baki kamar bazai magana ba.
Kallon ta yayi suka had'a ido sai ya mik'a mata hannu ta saka nata a ciki ya dawo da ita jikin sa gabad'aya ya hade hancin su waje d'aya yana goga nasa a akan nata idanun sa a buɗe ita kuma nata a kulle. Wuyanta ya yiwa kiss sannan yace, "Akwai different between Aliyu and i." Har lokacin hancin sa yana kan nata bai d'ago ba a haka yake magana khamshin vanilla flavor d'in da yasha na ice cream yana dukan hancin ta.
Fuskar ta ya rik'e yace, "open your eyes please." Kai ta girgiza tace, "I can't." Murmushi ya sake yi baice komai ba ya kwantar da ita a k'irjin sa ya mayar da hannun sa ya kulle ya lumshe idanun sa. Bugun zuciyar sa take ji a k'irjin ta ta saka hannu ta dafe saitin zuciyar sa taji muryar sa yace, "sabida ke take beating very fast." Ya d'ago ya kalle ta suka had'a ido ya wara ido yace, "ana ahibbaki."
Tasan me kalmar take nufi da hausa ta sake mayar da kanta k'irjin sa tana ji kamar ita kad'ai ce mace a duniya. Kusan mintina goma suna haka har bacci yana neman d'aukar ta jinta a jikin sa taji ya d'ago ta ya zare agogon hannun sa ya nuna mata wani bak'in zane kamar ciwo ya zagaye tsintsiyar hannun sa yace, "wannan shine banbanci na da Aliyu, duk lokackn kika ga wannan it's me not Aliyu ko Mama bata san dashi a hannuna ba because...." Sai kuma ya dafe kansa tace, "Sorry."
Shiru yayi na wasu sacanni kafin yace, "Because ban jima sosai da samun shi ba, ciwo ne na same shi a madina shine banbancin kawai." Kallon hannun nasa take sai zanen ya masa kyau a hannu kamar irin mutum ya karce d'in nan wajan ya warke tace, "But voice d'inka dashi yana da banbanci wani lokacin." Ya girgiza kai ya sake mayar da ita jikin sa yace, "In yaso zai magana kamar ni ko Mama bazata gane ba." Rauda tace, "Ikon Allah! Ban tab'a ganin masu kama da juna kamar ku ba." Ya sauke numfashi kusan mintina biyu kafin taji yace, "Even me." Daga nan bai sake magana ba tana jikin sa kuma bai sake ta.
*After two days.*
*Nigeria.*
Rana d'aya aka tashi da rashin lafiyar Mai martaba sarki hankalin iyalan sa ya tashi domin lokaci d'aya jikin sa ya birkice yayi tsanani sosai. Kasancewar litinin ce ranar zaman fada ce da safe ko wanne mai rawani ya bayyana a fada an cika mak'il ana jiran isowar sa.
Ba jimawa ya bayyana Hydar yana rik'e da hannun sa suna takawa a hankali, take kowa ya mik'e tsaye masu kirari suna fad'in, "Barka da fitowa Dawisu sarkin ado, barka da fitowa dubu jiran mutum d'aya, barka da zuwa fari mai farar aniya. Allah ya watsa mak'iyan ka, Allah ya k'aro lafiya ya sake ninko ta fiye da wacce muke rik'a. Kauce ga inuwar alkhairi nan ya tawo manya da yara na gudu don shigar ta, kai kad'ai ne wallahi, wallahi kai kad'ai muka sani bayan kai babu wani. Wane mutum balle aljan? Aljan da kasa in kazo waje kaucewa sabida magana ake ta saurata da mulki da kuma k'asaita!" Da k'arfin gaske yake fad'a ko tsayawa baya yi har aka kare mai martaba ya zauna Hydar ya koma gefen sa ya zauna a kan carpet.
Kusan mintina biyar aka d'auka kafin liman ya bud'e taro da Addu'a mai margaba kawai ake jira yayi magana ya kalle su d'aya bayan d'aya yace, "Alhamdulillah, yau shekarar mu talatin har da wani abun akan karaga, muna yiwa Allah godiya da ya nuna mana wannan rana."
"Allah ya k'ara lafiya, yasa a gama da duniya lafiya. Ya jikan mai babban d'aki ya raya mana zuri'a!" Aka sake fad'a mai martaba ya amsa da amin kafin ya d'ora da fad'in,
"Shekaru sun ja k'arfi ya k'are ga ciwo da muke fama dashi, bamu san gobe ba amma Allah zai iya yin ikon sa a koda yaushe. Kamar yadda na ambata a kwanakin baya zan bayar da karaga mulki ga Asad a lokacin kuma duk kun bada goyan bayan hakan, ina fatan har yanzu kuna kan ra'ayi irin nawa?."
Kallon kallo aka shiga yi idanun waziri sukayo waje ya share gumin da ya fara tsatstsafo masa kowa ya d'aga kai alamun suna nan kan matsayin su mai martaba yace, "To ma sha Allah. Duba da shawara da mukayi da makusanta da kuma yanayin ciwon bana so a bar talawa cikin rashin shugaba mai lafiya dan haka, A yau litinin zan mik'a kujera ga Asad duk da baya nan zan bada rok'on kwarya ga kawun sa da ya dawo a mik'a masa abin sa koda bana raye." Jin an ambaci kawun sa Waziri ya fara washe baki jikin sa ya fara tsuma yace, "Allah ya k'ara maka lafiya duk abinda kace namu shine mubi."