Sashe 75
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lallai ma ya raina mata wayo wato ta bashi dama ya rungume ta bayan ya rik'e mata hannu ta nuna bata ji dad'i ba shine zai k'ara gaba, zatayi magana yace, "Sau d'aya tak my love, sau d'aya kawai daga yau bazan sake ba sai kin zama mallakina." Kafin ta bashi amsa ma ya matso kusa da ita sosai ya jawo ta jikin sa kanta ya kwanta a k'irjin sa ya rik'e ta gam yana sauke numfashi a hankali.
"Kar ki rabu dani my love, sonki zai iya yi min babbar illa. Ki zauna tare dani har abada, Ina sonki ina qaunar ki" ya furta har lokacin tana jikin sa idanun sa a lumshe. Jin tana k'ok'arin kwacewa ya saka ya sake ta suka had'a ido ta sakar masa muguwar harara yayi murmushi ya danna lock d'in motar ta bud'e zata fita yace, "zan dawo na d'auke ki." Bata bashi amsa ba ta wuce ta barshi yana kallon ta har ta shiga gidan yayi murmushi ya kunna motar yaja yana jin nishad'i a zuciyar sa.
A zaune ta samu Yaya Ummi tana kallo ta shiga da sallama ta amsa tana fad'in, "Ga amarya, ga amarya." Dariya Rauda tayi kad'an ta zauna tace, "Yunwa fa nake ji." Tace, "to acici, sai kije ki zubo ai." Ba musu ta ajjiye ledar da mayafi ta fita ta shiga kitchen ta debo shinkafa da wake ta dawo ta zauna tana ci.
Yaya Ummi tace, "Yarinyar nan kyau kike k'arawa wallahi, Anas zai more aure."
"Kuma shine ya kawo ni fa."
"Lallai, amarya ta ango yana ji dake sosai, gaskiya kinyi dacen me k'aunar ki tun baki wayewar haka ba."
Yaya Ummi ta d'auki sak'on Umman ta bud'e kafin ta tashi ta d'auko wata leda ta dawo kusa da ita ta zauna tace, "ajjiye abincin ga kaza nan ki cinye ta tassss." Rauda jin ance kaza ta ajjiye tace, "Yaya meyasa baki fad'a min ba kika bari na fara cika cikina da shinkafa?" ta fad'a tana fara cin kaza ta lumshe ido tace, "Dad'i na da Yayata ta iya dahuwar kaza."
Tsaki tayi tana kallon ta tana ji kafin taga ga ajjiye tace, "na k'oshi wallahi." Yaya ummi tace, "Sai kin cinye tass Rauda dan ke aka yita ta gyaran amarya, maza daure ki cinye ki shanye romon."
"Wallahi Yaya cikina ne zai fashe na kuma ci na k'oshi, sai dai anjima." Yaya tace, "to anjiman kya shanye. Yanzu kora da wannan ruwan in kin gama ga zuma nan ki sha koda cokali biyu ne."
Daman tana buk'atar ruwan tasha ruwan zuma kuma abar kwadiyi ce tana ta lasa suna hira kafin ta ajjiye ta had'a mata a leda tace, "in kinje gida sai ki dinga sha, amma ko bari sai nan da kwana uku sai ki kuma sha kar yayi miki yawa. Kina shan kaninfarin dai ko?." Rauda tace, "eh."
"Yauwa maganin sanyi ne kar kiyi sake."
"To Yaya. Ni na gaji wallahi baku da hira yanzu sai ta wad'annan abubuwan da kuke d'irka min keda su Yaya Shamsiyya, dan Allah muyi wata hirar na gaji da wannan." Yaya Ummi tayi dariya tace, "to aure na biyu ne Rauda dole mu dage, in kika tuna auren ki na farko ai ba'a baki wasu abubuwan ba sabida lokacin budurwa ce ke in aka baki da yawa zaki cutu ne sosai. Allah ya isan mu ma da wancan ne ya sami budurcin ki a banza ina ma Anas din ne ya mallaka tunda shine mai sonki da kin sha qauna."
"Hmmm!" Rauda tace kawai bata ce komai ba kafin su fara wata hirar su bar wannan.
Bayan la'asar Rauda ta baro gidanta da bayan ta cinye kaza tass dak'yar take takawa dan bata d'auko sak'on nata bama tace ta kawo mata baza ta iya rik'ewa ba ta k'oshi. Tafiya take sai take ji kamar ana kallon ta ta juya sai taga babu kowa ta cigana da tafiya har tazo titin da ba'a samun jama'a sosai.
Bak'ar mota ce ta tsaya a gaban ta har ga Allah ta d'auka Anas ne duk da taji dad'in ganin sa sabida wajan babu mutane amma sai ta basar ta kawar da kanta gefe sabida laifin da yayi mata, wuƙa taji an saka mata a baya ance, "kina yin ihu sai na soka miki ita a baya, shiga mota muje." Jikin Rauda ya hau rawa taga an bud'e bayan mota dole ta shiga a firgice a gigice aka ja motar da k'arfin gaske.......
*Aliyu ya dawo, Asad yana k'ok'arin dawowa daidai, An sace Rauda, wacece master planer...?*🏃🏼♀️🏃🏼♀️
Zan iya cewa yanzu aka fara fa🤣🤣
[17/12, 10:41 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*063*
Yadda suke kwarara gudu a kan titin hakan zai baka tabbacin basu da gaskiya Rauda na zaune tayi tsuru tana kuka gaban ta sai fad'uwa yake yi tsoro ya gama damalmale mata zuciya ta tabbatar sace ta akayi shikenan ta daina ganin Umman ta. Tuna hakan sai ya sake Sakata kuka hankalin ta ya tashi sosai cikin k'arfin hali tace, "Su waye ku? Meyasa kuka d'auko ni? Ina zaku...." duf tayi nuna mata wuƙa da na gefen ta yayi ta had'd'iye yawu ta sake fashewa da kuka.
Basu jima sosai suna tafiya ba suka iso k'aton gida mai bak'in gate tafkeke suka danna horn da k'arfi aka bud'e musu gate d'in suma jefa motar cikin gidan suka faka suka fita aka bud'e mata wanda yake kusa da ita yace, "fito." Cikin kuka tace, "Bazan fito ba sai dai ka kashe ni."
Cikin tsawa yace, "ki fito nace!." Ta sake cewa, "Sai dai ka kashe ni amma bazan fito ba." Wuƙa ya nuna mata yace, "in baki fito ba zan farka hanjin cikin ki yanzu."
"In ka farka ka yanka ka soya kaci amma wallahi bazan fito ba." Hannu yasa zai finciko ta wanda yake bayan sa yace, "Kaii! Dakata mana." Juyowa yayi yana kallon wanda yake maganar yace, "kana jin abinda take cewa? Wai bazata fito ba."
"To shine zaka saka hannu ka d'auko ta? Kai kasan wacece ita kake k'okarin yin wannan gangancin...? Wallahi hakan ta faru ka tabbatar ranka sai yayi mugun b'aci" ya kalli Rauda yace, "Dan Allah ki fito ranki ya dad'e baza mu cutar dake ba." Rauda tace, "Bazan fito ba!, bazan fito ba!" ta fad'a tana curewa a waje d'aya tana fashewa da kuka. Sake tausasa murya yayi yace, "Dan Allah ki daure ki fito wallahi baza mu cutar dake ba, ki amince damu bamu kawo ki nan da mu cutar dake ba."
Bata kula su ba sai kukan da take yi sosai domin bazata fito ba sai dai duk abinda ya zasuyi mata suyi mata, shiru taji ba wanda ya kuma yi mata magana ta d'ago taga duk basa wajan ta juya taga babu kowa sai ita kawai a zaune a motar tsoro ya mamaye mata zuciya ta sake curewa a waje d'aya tana sake fashewa da kuka.
K'ofar da take gefen ta taji an bud'e kafin ta kula da waye ko wace taji anyi sama da ita ta kurma ihu tana wuntsila k'afa hakan bai saka an ajjiye ta ba har cikin k'aton falo aka ajjiye ta akan carpet.
Yunk'urawa tayi zata zura a guje taji an rik'e hannunta cikin kuka tace, "Dan Allah kayi hak'uri ka mayar dani gida me nayi maka aka kawo ni nan?." Juyowa yayi ya kalle ta amma bata gane waye ba domin gabad'aya fuskar a rufe take ya saka face mask kuma ya saka glass ga picap a kansa hakan ya saka bata gane shi ba.
"Dan Allah kayi hak'uri ka mayar dani gidan mu dan Allah....." ta fad'a tana zubewa a wajan tana kuka shi kuma ya zuba mata ido kawai yana kallon ta duk da tarin haushin ta da yake ji a zuciyar sa amma ganin ta ya saka yaji nishad'i a zuciyar sa sosai.
"Relax!" Ya furta a hankali cikin muryar sa mai d'aukar hankali wacce bazata manta da ita ba yana kallon ta. A firgice ta d'ago da idanun ta da suke jik'e da hawaye tana kallon sa jin muryar wanda ya daki kunnen ta, murmushi yayi kad'an ya zare glass d'in idanun sa ya cire hular ya cillar ya cire face mask d'in yana kallon idanun ta. Idanu ta zaro waje ta mik'e tsaye tana kallon sa shima ita d'in yake kallo fuskar sa tamke babu alamun walwala a kanta.
Bakin ta rawa yake yi tana so tayi magana amma ta kasa sai kallon sa da take yi tana kifta ido cikin mamaki da tsoron da ya mamaye mata zuciya, kafin tayi magana yace, "Surprise." Kanta ta daka ta runste ido ta sake bud'ewa tana kallon sa ta tabbatar shi d'in ne a gaban ta ba wani ba.
Fuskar sa a tamke yake binta da kallon sai yaga itama ta juya fuskar ta daga ta tsoro ta koma ta zallar rashin kunya tace, "Meye dalilin ka na kawo ni nan?." Wara idanu yayi yana girgiza kai jin tama raina masa hankali shi zata kalla ta yiwa wannan tambayar dan taga makwancin sa.
Banza yayi mata ya samu waje ya zauna ya binta da ido itama shi take kallo tace, "Magana nake maka fa malam, meyasa aka akwo ni nan..? Me kake nufi dani eyeeee?." Kai yake girgizawa yana kallon ta cikin mamaki sai ya cize bakin sa ya murza idanun sa ya shafa sajen fuskar sa har lokacin bai daina kallon ta ba.
"Mtswww in baza kayi magana ba ni bazan iya jira ba domin bani da lokacin ka ko kad'an ina da abin yi" ta fad'a tana juyawa zata fita taji muryar sa yace, "kar ki sake ki motsa daga nan." Juyowa tayi ta galla masa harara tace, "in nak'i fa akwai abinda zakayi min ne?."
Kai ya girgiza dan shi mamaki ma take bashi ya kwantar da kansa a kan kujerar yace, "Okay, kiyi u shall see." Tsaki ta kuma yi ta k'arasa wajan k'ofar ta murd'a amma tak'i bud'ewa ta jijjiga duk da haka bata buɗe ba ta dawo da baya ta kalle shi tace, "Ka buɗe min k'ofa ina da abinyi, banga dalilin da zai saka ka kawo ni nan ka ajjiye kamar wata baiwar ka ba."