← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 131

Sashe 128

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Eman ta rik'e ta tana kukan itama bata ce komai ba Jidda ta kuma cewa, "Sabida Mum ta mayar da kisan rai ba komai ba nima na koya na dinga k'okarin kashe Asad kawai dan kar asirina ya tonu Eman, Mum ta cuce ni wallahi itace ta koyar dani hanyar da za'a kashe mutum domin mun sha yunƙurin kashe Babar Asad d'in kawai dan kar ta bamu matsala akan kudurin Mum. Dole ma hakkin Mama dana Asad ya dinga bibiyar mu gashi nan Daddy ya barmu kema ya raba ki damu babu wanda yake zuwa wajan mu dan abinda muka aikata ba k'aramin sabon Allah bane."

Eman ta girgiza kai tace, "Daddy fushi yayi amma In ya wuce zai dawo Jidda."
"Gwara karya dawo Eman domin mu ba irin wanda za'a rab'a bane nan gaba kad'an shi d'in ma Mum zata iya kashe shi. Eman ina so na kai kaina kotu a yanke min hukuncin da musulunci ya tanadarwa Irina na karb'i hukuncina tun a duniya kafin naje wajan mahalicci na."

Eman tace, "Jidda za'a jefe kine fa har sai kin mutu shine hukuncin wanda ya aikata Zina da aure a kansa." Jidda tace, "Meye amfanin rayuwata Eman? Gwara ace na mutu d'in kowa ya huta dan rayuwata bata da amfani Kwata-kwata. Mum ta gama cutata sai Allah ya tsayar dani da ita yayi mana hisabi."

Kuka take Mum d'in ma haka, sun cika d'akin da kuka babu mai rarrashin wani kafin Jidda tace, "Ina so naga Asad ya yafe min wallahi na tuba, na kuma taya shi murna da bai zauna da mace Irina ba Allah ya kawo masa mafita da yake ya kasance mai bautar Allah. Mu kuwa da babar mu ta d'ora mu akan turba mara kyau ga inda k'arshen mu ya kasance a wulaƙance a lalace. Eman koda an jefe ni na mutu kar ki biyewa son zuciyar Mum ki bi Allah da abinda ya umarta wanda yace a bari ki bari Eman in ba haka ba zakiyi k'arshe irin nawa mara kyaun gani da kyaun ji."

Rungume ta Eman tayi tana kuka sosai itama tana kuka Mum ma tana kuka sosai, Jidda tace, "Tun Mama da Mum suna makarantar secondry school a Kano aminan juna ne har sukayi aure a waje d'aya suka cigaba da aminci, Mama ta amince da Mum amma ita kuma cutar da ita take yi. Ina ma kafin ta haife ni cikina ya zube na huta da wannan bak'ar rayuwar da ta saka ni a ciki."

"Eman ki cewa Mama ta yafe min, ki cewa Asad ya yafe min dan Allah nasan babu lallai na kuma ganin su dan yau d'in nan zan kai kaina inda za'a jefe ni na mutu." Eman tana kuka matuk'a itama haka. Mum da take gefe tana kuka tace, "Kwarai son zuciyata ne ya jawo min, tabbas nice na jefa ki a wannan hali Jidda kiyi haƙuri ki yafe min dan Allah."

Jidda tace, "Babu yafiya tsakanin mu Mum, sai Allah yayi mana hisabi nida ke." Eman tace, "haba Jidda meyasa kike cewa haka? Yanzu kike cemin na fad'awa su Asad su yafe miki meyasa ita bazaki yafe mata ba?." Jidda tace, "Haka ne kuma, na yafe mata Eman amma ta cuce ni wallahi."

Tari Jidda ta fara tana dukan k'irjin ta ganin yadda idon ta yake k'afewa ya saka Eman fita a guje ta kira likita ya shigo a guje aka fitar da Eman aka rufu akan Jidda dan ganin a ceto rayuwarta dan yanayin nata yayi muni sosai ba kad'an ba amma abin yaci tura rai yayi halin sa lokaci ya riga yayi tafiya ko baka shirya ba sai kaje.

Fad'a musu ta rasu Eman ta zube a sume Mum ma bata sake sanin inda take ba. Daddy aka kira aka sanar dashi duk da abinda yake ji a kansu sai da hankalin sa ya tashi rasuwar Jidda ta tab'a shi gama jana'izar abinda ta haifa kenan itama ta bishi, ya rud'e sosai haka akazo aka d'auki gawar ta a safiyar akayi jana'izar Jidda wacce ta tara mutane dama dan shi kansa Daddy bai san za'a cika haka ba aka kaita makwancin ta Mum bata sani ba Eman ma tana sume.

*☆☆☆*

          K'arar wayar sace ta tashe shi ya tashi yana yamutsa fuska ya kai kallon sa kan agogo yaga k'arfe d'aya daidai na rana ya wara idanun sa ya sakko daga kan gadon ya zauna ya d'auki wayar ganin mai kiran ya saka shi ya d'auka ya saka a kunne, "Zaki ina ka saka waya haka?." Asad ya gyara murya yace, "Barka da safiya Abba."
"Safiya! Da alama yanzu ka tashi kenan."

Asad ya dafe kansa yace, "Na kwana bana jin daɗi ban samu bacci da wuri ba. Ina fatan Abba ya tashi lafiya." Mai martaba yace, "Alhamdulillah. Ya zaman Abujan?." Asad ya shafa kansa yace, "Alhamdulillah."
"Ina ta kiran ka tun d'azu na sanar dakai rasuwar matar ka Jidda da ita da abinda ta haifa duka Allah ya karb'e su."
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Yau akayi jana'izar ta?" Ya furta cikin bugawar zuciya.

"Tun safe akayi ana ta mamakin rashin ganin ka." Asad yace, "Hasbunallahu wani'imal wakil! Allah ya gafarta mata ya yafe mata yasa tana aljanna. Abinda ta haifa yasa ya kasance mai ceton ta." Abba yace, "Amin ya rabbil alamin. Babar ta da K'anwar ta har yanzu basu farfad'o ba suna sume, ita kanta babar ka mutuwar ta tab'a ta sosai."

Asad yayi shiru yana girgiza kai kafin Abba yace, "In ka kammala abinda kake yi dai zuwa gobe ko jibi ka dawo akwai abubuwan da suka taru suna jiran ka dawo ka aiwatar dasu." Asad yace, "In sha Allah." Daga nan sukayi sallama ya kashe nan ya duba yaga missed call d'in Mama dana Suhail.

Mama ya fara kira ta d'auka yace, "Barka da rana Mama." Mama tace, "Barka Asad."
"Ina neman afuwa ban d'auki kiran Mama ba."
"Babu komai Asad. Ka samu labarin rasuwar Jidda ko?" Ta fad'a muryar ta na rawa sosai. Kafin yayi magana tace, "Asad duka abinda Jidda ta aikata nima ina da hannu a ciki gashi ta rasu bata yafe min ba ya zanyi?."

Jin tana kuka sosai sai hankalin sa ya tashi ya sassauta murya yace, "Kiyi haƙuri Mama ki mata addu'a" ya fad'a dan bai san me zaice ba kuma. Kuka take sosai yana jinta sai da tayi kusan mintina bakwai tana kuka a waya shi kuma yayi shiru bai kashe ba yana jin kukan har zuciyar sa kafin yace, "Kiyi haƙuri Mama haka Allah ya rubuta abinda zaiyi silar rasuwar ta kenan." Yana ji ta sauke ajiyar zuciya kafin tace, "Ka gaida Rauda" tana fad'a ta yanke wayar yabi wayar da kallo zuciyar sa tana bugawa sosai.

Mutuwar yaji ta a jikin sa sosai bazai manta lokacin da suka je dubata ba duk da abinda ya faru yana yi mata fatan samun rahamar Allah, Rauda da tunda ya fara waya ta tashi tana jin duk abinda ake cewa tace, "Waye ya rasu Sultan?." Kallon ta yayi ya sauke numfashi yace, "Jidda ita da yaron ta." Rauda ta mik'e zaune tace, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, yaushe?."
"Yau" ya bata amsa a tak'aice.
"Allah ya gafarta mata yasa yaron ya zama mai ceton ta."

Numfashi ya sauke yace, "Amin. Mama tana gaishe ki" ya fad'a yana mik'ewa tsaye.
"Ina amsawa" ta fad'a jin wani iri wai Mama tana gaishe ta lallai duniya ta ishi kowa riga da wando harda babbar riga.

Agogo ta kalla ganin d'aya ta wuce sai ta sakko daga kan gadon ta tsaya itama kamar yadda yake a tsaye bai motsa ba sai k'asa da yake kallo, numfashi taga ya sauke ya juyo ya kalle ta ya mik'a mata hannu yace, "Wanka." Kafaɗar ta nok'e tace, "Zanyi ni a wani d'akin kayi kai a nan."

Duk da babu walwala a fuskar sa haka ya tako inda take ya rik'e hannun ta bai magana ba ya jata har cikin band'akin babu yadda zatayi dan babu fuskar musawa a tare dashi. Tare sukayi wankan suka fito ta zauna gefen gado tana kawar da fuska har gobe kunyar sa take ji shi kuma taga ya sakawa idanun sa toka baya jin kunyar ta ko kad'an kamar ba shine sarkin Katagum ba.

Sabuwar doguwar riga taga ya d'auko mata a leda irin mai laushi da babban mayafi ya mik'a mata ta kalli doguwar rigar tace, "Bani da undies fa." Tab'e baki yayi baice komai ba ya k'arasa inda take ya zira mata doguwar rigar ta sama ya zame towel d'in jikinta yace, "Sallah."

Shima doguwar rigar ya saka suka tayar da sallar azahar, bayan sun idar ya kalle ta yaga sai yanutsa fuska take ganin yana kallon ta tace, "Wallahi bana jin daɗin zama haka babu komai a jikina, ni zan koma gida kawai yau." Bai tanka mata ba taga dai ya d'auki waya bata san me yayi ba taga ya ajjiye sai kuma ya kuma d'auka ya kira Suhail.

Yana d'auka yace, "Allah yaja zamanin mai martaba, Allah ya kiyaye mai martaba ya kare shi."
"Suhail" shine abinda ya furta kawai. Suhail yace, "Allah yaja zamanin ka ina cikin gidan tun safe na kawowa mai martaba abinda yace a kawo." Kai kawai ya girgiza kafin ya yanke wayar ya kalle ta yace, "Ina zuwa." Ya tashi tsaye itama ta tashi tana kallon sa tace, "tsoron gidan nan nake ji fa bazan iya zama ni kad'ai ba, nidai zan bika muje inda zaka gaka."

Kallon ta yayi sai yaga kamar ana ganin komai na jikin ta dan yadda ta motsa komai na jikinta motsi yake tunda babu komai a jikin nata, d'aure fuska taga ya sake yi amma duk da hakan bata hak'ura ba zai wuce ta tace, "Wallahi tsoro nake ji." Ganin a tsorace take sosai sai ya kira Suhail yace ya k'araso falon ya fita ita kuma ta zauna a d'akin.
Chapter 128 · 0% Book details