Sashe 43
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Banda abin ki Rauda in da kud'i meye baza'a yi ba? Ai aiki akayi bana wasa ba kusan kwana suke ana aikin gidan nan lokaci kad'an aka gama ya bada umarnin zuba komai na gidan nan da kike gani cokali namu bamuyi amfani dashi ba duka sabo aka zuba mana namu bayarwa muyi wasu muka siyar. Kayan abinci kuwa kamar kasuwa dan wallahi zan iya ce miki akwai kayan abinci na shekara a gidan nan, banda kayan miya da nama da kaji da ake kawo mana duk sati. Ai mahaifin ki yaga amfanin haihuwar y'a mace da kullum k'orafin sa bai ga amfanin haihuwar mace tazo a babba a gida ba."
Rauda ta girgiza kai tana kallon gidan fanka tana ta juyawa a d'akin tace, "solar ce wannan ko nepa?." Umma tace, "Solar akayi mana Rauda, awa ashirin da hud'u da wuta a gidan nan sai dai mu gaji mu kashe. Ke y'an unguwar nan fa cewa suke wai mahaifin ku yankan kai ya koma shiyasa yayi arzuk'i lokaci d'aya, wasu kuma suce ya siyar dake ya karb'i kud'in magana dai kala-kala; kaf unguwar nan babu gida mai kyaun wannan fa."
Kafin tayi magana Umma tace, "Duk ranar juma'a kuma da aiken da za'a yo mana kud'in cefane, abinci baya yankewa a gidan nan Rauda madara, milo dasu ake shan shayi a gidan nan, duk baki ga mun canja munyi haske ba?. Sai yanzu na gano Asad ne ya siya miki magani ba Anas ba."
Ambatar Anas da Umma tayi sai da gaban Rauda ya yanke ya fad'i tayi shiru bata ce komai ba Umma tace, "Bamu da abinda zamu biya yaron nan ai sai addu'a, yayi mana abinda bamu kawo zai faru ba cikin rayuwar mu ba." Rauda ta girgiza kai hawaye na neman zubo mata tace, "Haka ne Umma."
"Ina Raudan take!" Yaya Ummi ta fad'a tana shigowa ganin Rauda ya saka ta tawo da sauri tana fad'in, "Mutanen Egypt." Umma ta kalle ta tace, "A daren nan kika fito Ummi?."
"Shine ya kawo ni a machine Umma, bazan iya zama har gobe banga Raudan ba" ta fad'a tana rik'e hannun ta cikin kewa.
"Kan bala'i, Umma kinji laushin da hannun Rauda yayi? Ke wai wankan madara kike a can ne naga gabad'aya kamar an sauya miki halittta."
Dariya kawai Rauda tayi amma ta kasa cewa komai Yaya Ummi tace, "Zama dashi ya koya miki rashin magana kema ko sarautar ce ta shiga jikin ki?." Rauda tayi dariya tace, "Haba Yaya sai kace chajin waya?." Sukayi dariya gabad'aya tace, "to gani nayi sai maganar da kika ga dama kike bada amsa. Rauda kalli wayar hannun ki a k'alla ta kusa miliyan; yarinyar nan Allah ya yarda, Baba me cewa waye zai d'auke ki yazo yaga ikon Allah."
Umma tace, "ya sakko ai yanzu, abin mamaki shine ya tafi siyowa Rauda kaza da kud'in sa." Yaya Ummi tayi dariya tace, "To Umma ai dole ki duba kud'in da suke shigowa hannun sa ta dalilin wannan napep d'in yana zaune sai dai a kawo masa balance. Me zamu ce da yaron nan mu in ba godiya ba? Abinci da gagarar ku yake a gidan nan, ga talla da yake d'ora musu ashe ta sanadin tallan Allah zai b'ullo mana da alkhairi."
Rauda tayi dariya tace, "Baba akwai drama ai." Yaya Ummi tace, "k'afa ta warke Rauda."
"Ta warke Yaya."
"Alhamdulillah, bamu da abinda zamuce sai dai mu gode Allah Rauda. Ina tsohuwar wayar taki a bani?." Rauda ta kalli wayar hannun ta kafin tace, "Wallahi tun a lokacin da wayar da tsohon layin ya saka su a shara."
"Shara! Meyasa to bai bar miki ba?." Rauda tace, "ban sani ba wallahi" ta fad'a a tak'aice dan kawai dauriya take. Umma tayi murmushi kawai bata ce komai ba Yaya Rauda tace, "kuma su a can babu wanda zai d'auka nasan bola za'a kai ba kamar mu Nigeria ba. Lallai yana da kishi dan nasan yasan Anas ne ya baki shiyasa ya yar da ita."
Umma tace, "Da kika ce Anas sai kika tuna min, bayan tafiyar ki baifi da sati ba yazo neman ki yake shaida mana matar da zai aura Allah yayi mata rasuwa ya dawo wajan ki a karo na biyu muke shaida masa auren ki. Baki ga yadda ya gigice ba Rauda har kuka sai da yayi ya bani tausayi sosai a nan take kuma yayi tawakali yayi miki addu'ar samun zaman lafiya tun daga ranar kuma bai yanke zumunci damu ba Rauda yana yawan zuwa mu gaisa har ya zama ma da yazo zai shigo gidan nan kai tsaye."
Rauda jikin ta duk yayi sanyi sun kasa gane bata son maganar sabida abinda take ji a zuciyar ta tace, "Allah Sarki, Allah ya gafarta mata." Suka amsa da amin. Yaya Ummi tace, "Ina shi mijin naki wai?." Rauda tace, "ya wuce gida bai zo nan ba."
"Ai gobe dole na dawo ko dan na ganshi dan nasan dak'yar in ba goben zai zo ba." Murmushin yak'e Rauda kawai tayi bata ce komai ba domin tasan bazai zo ba har abada.
Umma tace, "Ummi tashi ki tafi dare yana kuma yi." Yaya Ummi tace, "ya zan tafi ba tsaraba? Ke Rauda yanzu baki tawo min da komai ba?." Umma ta rik'e baki tace, "Amma anyi yayar banza, ita da taje jinya ina ita ina yo tsaraba?." Rauda tace, "bara muga akwai dogayen riguna Allah yasa suyi miki naga kin zama k'atuwa" ta fad'a tana tashi ta janyo akwatin ta ta bud'e tana fito da kayan.
Cikin ikon Allah duk wad'anda ta siyo musu matsayin tsaraba duka sune a ciki har dana Baba nata ne babu sosai sai guda biyu; ta d'auko ta Umma ta bata ta bawa Yaya Ummin ta sauran tace, "Gata Baba, gata Inna, gata Rahma. Wannan takalmin na Ummulkhairi ne dana na Khalil da Sammani, wannan doguwar rigar kuma ta Yaya Shamsiyya da Yayar mu da Yaya Nafisa da Yaya fariha." Umma tace, "Kice kud'i kika saka ya kashe haka." Rauda tace, "A'a Umma ni bance zan yi tsaraba bama shine ya saka ni."
Yaya Ummi tayi dariya tace, "wannan doguwar rigar gobe da ita zan fito na yiwa talauci barazana ko babu komai na saka rigar Egypt. Allah ya barku tare Rauda ya k'ara muku zaman lafiya me d'orewa; shiyasa kake murna in k'anwa mace ta samu jin dad'i domin gabad'aya iyalan gidan kune suka samu." Umma tace, "Gaskiya kam. Allah ya k'ara muku zaman lafiya ya saka mutuwa ce zata raba ku."
Sharrrr hawaye suke fara zubowa daga idanun Rauda tayi sauri ta goge Yaya Ummi da ta kula tace, "Dole kiyi kuka Rauda jin dad'in duniya kin same shi ke kam sai dai fatan ki samu na lahira." Murmushi kawai tayi zuciyar ta nayi mata ciwo tana sake goge idanun ta.
Umma tace, "Ummi ki tashi ki tafi itama a barta ta huta dare yayi." Rauda tace, "Ai a can Umma ba'a bacci da daddare sai da safe dare shine lokacin zuwa kasuwa da yawo." Umma tace, "haka akace su can daman dare shine rana." Yaya Ummi ta mik'e tace, "Rauda na wuce gobe zan dawo da wuri na sha labari" ta fad'a tana ficewa Rauda tayi dariya kad'an. Umma ta kalle ta tace, "ki kai musu tsarabar sai kizo ki huta kin dawo Nigeria nan ba can bane."
Tashi tayi ta kwashi kayan ta fita dasu ta kai musu suka dinga ihu ana murna, Baba ma a lokacin da ya shigo ta bashi tasa ya bata kaza yana ta saka mata albarka kamar bashi bane yake kiran ta da mujiya ba.
Lokacin da ta koma Umma bata d'akin ta zauna ta bud'e kazar da Baba ya bata amma sai taji ta kasa ci gabad'aya ta rufe Ummulkhairi ta shigo ta bayar ta bawa Umma. Kwanciya tayi a kan gadon tayi lamoo kamar marainiya hawayen da take riƙewa suka sakko mata ta fara kuka mai sauti ko zata samu sassaucin da take ji a zuciyar ta.
"Me zance musu ni Rauda? Nace musu ya sake ni sabida Maman sa bata sona?. Suna ta fad'ar hidimar da akayi dasu sabida ni, suna tayi min addu'ar cigaba da zama dashi ya zasu ji in nace musu ya sake ni? Ya zasu ji in nace musu na zama bazawara a cikin sati hud'u kacal?, ya zasu ji in na fad'a musu irin wulaƙancin da akayi min?. wa'inna ilaihir raji'un, ya zanyi ni Rauda nayi shiru ko na fad'a musu?. Daman can nasan sai hakan ta faru dole ya rabu dani daman akwai dalilin yin auren" Ta kuma fashewa da kuka mai tsuma zuciya.
"Anty Rauda kukan me kike yi?" Ummulkhairi ta fad'a tana shigowa tana kallon ta.
Goge idanun ta tayi da sauri ta kalle ta tace, "kaina ne yake min ciwo kad'an, karb'o min magani wajan Umma in akwai." Da to ta amsa ta juya Rauda ta tashi ta goge idanun ta sosai Khairi ta dawo da magani ta bata tasha ta haɗa da ruwa, Ummulkhairi tace, "Ki kwanta to Anty zaki ji dad'in ciwon kan Umma tace gajiya ce." Ta amsa da to ta tashi ta canja kaya ta saka na bacci ta kwanta zuciyar ta cike da saqe-saqe.
*☆☆☆*
_Love you girl no get holiday, I do am all day everyday uhmmmm I need no one like oh no no, love you girl i get pom pom shey if u go know how I want pom pom shey ooo I need no one like i need you oh no no mmmmm, shower body down and come my lover mmmmm make i dirty you well with my love la la la, and I say hop on my bed let's sin, baby coman good sin good sin, no be bad sin good sin good sin._ wakar da take tashi kenan tun daga farkon estate ake jin sautin ta da muryar y'an mata da suka had'a baki suna yi kamar karatu.