← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 131

Sashe 37

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama tayi murmushi ta kalle shi tace, "umarni nake baka yanzu ba anjima ba ka saki yarinyar nan!." Runtse idanun sa yayi daidai lokacin da zuciyar sa ta buga da k'arfin gaske ya cize bakin sa ya bud'e ido ya kalle ta yaga shi take kallo sai ya sauke ido k'asa ya kasa cewa komai.

Sautin kuka Rauda ya karad'e ko ina a falon kuka take yi sosai zuciyar ta nayi mata zafi ta kasa furta ko wacce kalma sai kuka sabida tashin hankalin da take ciki ba d'an kad'an bane. Mama ta kuma kallon sa tace, "Magana nake maka Asad indai ka d'auke ni matsayin mahaifiyar ka wacce ta haife ka ta raine ka ka sake ta, in kuma kana so ka nuna min ka zab'e ta a kaina bismillah Asad."

Idanun sa sun koma jajaye haka fuskar sa ya d'ago ya kalle ta ya sake mayar da kansa k'asa yace, "Dan Allah Mamaaaaa!." Abinda ya iya furtawa kenan Mama tace, "Wallahil azim sai ka sake ta matuk'ar na isa dakai.
Muryar sa har rawa take yi  har labb'an sa kana ganin yadda suke motsawa yace, "Allah da ya halicce mu shine ya halatta saki amma kuma baya son sa Mama, Mama tana da iko da Asad a koda yaushe amma dan Allah ta barni na gujewa abinda Allah baya so kar na aikata shi duk da kasancewar halak." Mama ta girgiza kai tace, "Da alama mallakar da aka yi maka har yanzu tana jikin ka kenan ko? To tunda nazo ko wanne irin asiri tayi maka wallahi sai na b'alla shi wallahi. Na riga na rantse ka sake ta Asad!" Ta k'arasa fad'a da k'arfi tana kallon sa.

Zubewa Rauda tayi a wajan tana kuka sosai hankalin Asad ya kuma tashi zuciyar sa na bugawa a guje kamar zata fito daga k'irjin sa ya kasa furta komai ji yake kamar shima ya zubar da hawaye sabida rad'ad'in da yake ji a zuciyar sa. "Kana yi min biyayya a ko wanne lokaci meyasa kake son b'ata min rai akan wannan mujiyar? Ka fifita ta a kaina kenan?." Da sauri ya girgiza kai yayi alamun a'a tace, "to sake ta."

Suhaima da take gefe tausayin d'anuwan ta ya kamata tace, "Mama dan Allah....." saurin dakatar da ita tayi tace, "ban saka ki a maganata ba." Ba shiri Suhaima tayi shiru Mama ta kalli Asad tace, "Zaka sake ta ko a'a?." Numfashi ya fesar ya had'd'iye yawu mai d'aci ya kalli Rauda da take zube tana kuka kanta na cikin cinyoyin ta ya sake sauke numfashi cikin tashin hankali da bugun zuciya.

      "Baza kayi ba kenan ko? To ka sani matuk'ar baka sake ta a yanzu ba bazan yafe maka ba Asad sannan kuma wallahi sai nayi maganin ta da ita da dangin ta gabad'aya." Da sauri ya kalli mahaifiyar tasa ta d'aga masa kai tace, "eh kaji ai me nace, in baka sake ta ba bazan yafe maka ba Asad." Lumshe ido yayi cikin zafin da yake ji jiki sa har idanun sa yana ji kamar ya zubar da hawaye amma babu dama.

Kai ya sunkuyar ya juya ya kalli Rauda da har lokacin kuka take ya sake kallon Mama da ta kafa masa ido ya cize bakin sa ya sake had'd'iye yawu bakin sa na rawa amma ya kasa furta ko wacce kalma. Dak'yar ya zame k'asa ya durk'usa yace, "Ni shugaba ne, Abba ya sanar dani komai Mama sakin aure hani ya kamata nayi dashi bana aikata shi ba. Dan girman Allah ina rok'on mahaifiyata da ta janye kalaman ta." Ganin yana b'ata mata lokaci ya saka taja tsaki tace, "Asad in bakayi abinda nace ba zaka had'u da b'acin raina wanda baka tab'a had'uwa dashi ba har abada. Ka sake ta ko na sallama mata kai har abada" ta fad'a a fusace domin ranta a b'ace a yake ganin yadda yake mata gaddama a gaban wata banza bare talaka yar talakawa.

Rauda ya kalla bashi da zab'i sai bin abinda mahaifiyar sa take so yace, "I'm sorry.....!" Mama ta fusata kamar zata dake shi tace, "au sai ka bata hak'uri? Kenan itace wacce ka fifita sama dani Asad? Ashe zaka iya nuna kafi son wata a kaina Asad?." Ya kalli Maman cikin girmamawa yace, "Ban kai wannan matsayin ba Mama, Allah ya wuci zuciyar ki zanyi abinda kike so" ya fad'a jiri yana d'aukar sa.
"To sake ta."

Ya kalli Rauda ya tuna ko cikakken mintina asihrin baiyi da d'aukar mata alqawari ba gashi tun ba'a Je ko ina ba ya karya bai cika mata shi ba daman yasan abinda take tsoro itama kenan gashi kuma ya faru, zai zama makaryaci a idanun ta maci amana mara cika alƙawari yace, "Na sake ki saki d'aya!."

A tare zuciyar su ta buga Rauda taja numfashi ta d'ago fuskar ta tana murmushin k'arfin hali hawaye yan zuba amma bata iya cewa komai ba. Mama ta sauke numfashi tayi ajiyar zuciya mai tsaho har tana dafe tace, "Finally mun rabu da k'aya, sai ki fita ki koma gidan ku kije can ku cigaba da zama cikin talaucin da kuka saba zama. Ina miki warning akan y'ay'ana bama Asad kawai ba, kar na sake ganin ki a kusa da k'ofar gidan su ma balle na ki shigo gidan, in kuma ba haka ba zan d'auki mummunan mataki a kanki dake da dangin ki. In kunne yaji jiki ya tsira kin taimaki kanki da iyayen ki, in kuma kink'i ji kin cigaba da yi masa asiri wallahi!, wallahi!!, wallahi!!! Sai naga bayan ki keda iyalan gidan ku gabad'aya."

Rauda tana ji bata ce komai ba Mama ta kalle shi tace, "had'a kayan ka mu bar hotel din nan yanzu." Sai kuma ta kalli Rauda tace, "maza-maza tashi ki fita kije can ki karata ko yau a d'aura miki aure da wani dan nasan baki isa kiyi iddar d'ana ba." Rauda ta mik'e jiki a sanyaye dan hawayen ya tsaya cak Mama ta kalle shi tace, "Ina passport d'inta? Maza bata ta b'ace min da gani bana son ganin ta ko kad'an." Hankalin Asad yayi mugun tashi ya kalli Maman tasa yace, "bata san kowa a nan ba, bata an ko ina ba, ina zata je?."

"Ta tafi ko ina ma bai dame ni ba." Rauda jikin ta ya gama yin sanyi ta fara takawa k'afar ta ko takalmi babu zata gifta su Asad yayi sauri ya zube guiwar sa a k'asa yana kallon Mama ya rik'e hannunta kamar zaiyi kuka yace, "Dan Allah Mama ki barta ta zauna a nan nayi abinda kika ce na kuma barta tunda shine farin cikin ki na cika miki burin ki na rabu da ita, kiyi min wannan alfarmar yadda Allah ya taimake ki ki taimaki d'anki mai rauni ki amince ki barta ta zauna a nan in ta bar nan ina zata je?, babu wanda ta sani babu inda ta gani a k'asar nan. Ki barni na mayar da ita gida kamar yadda na d'auko ta cikin aminci dan Allah."

Mama kallon sa take da mamakin yadda yake magana kamar bashi ba kenan daman rashin maganar tasa iskanci ne yana sane tunda gashi indai akan lamarin tane yana magana yadda ya kamata hakan ya kuma fusata Mama tace, "Wallahi sai ta fita!." A daidai wannan lokacin Rauda ta fita daga falon ya saukar da kai kansa na mugun sarawa kamar zai fashe ya runtse idanun sa, zuciyar sa nayi masa ciwo tare da rad'ad'in da bai tab'a jin irin sa ba a rayuwar sa, ya d'ago kai yabi hanyar da ta fita da kallo ya sauke numfashi mai nauyin gaske..........

*Mama tayi mana yankan k'auna*😢
[17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*044.*

         A fusace ta juya ta kalle shi ta kama hannun sa ya mik'e tsaye tana binsa da kallo tace, "ban tab'a ganin raunin ka akan komai ba sai akan wannan kucakar yarinyar a lokacin raunin ka ya fara fitowa kan fuskar ka, ban tab'a ganin gazawa k'arara a fuskar ka ba sai da yarinyar nan da ta asirce ka. Duk wani ko wata da zai kawo min tangard'a a cikin cikar burina bazan barshi, ba'a san shugaba da rauni ba dan haka ka k'arfafa zuciyar ka ka manta da ita ka d'auka baka tab'a sanin ta bama a duniya domin ka barta kenan har abada."

Kansa na k'asa bai ce komai ba harta gama bai ce komai ba sabida yadda yake jin zuciyar sa na tafasa bazai iya furta ko wacce kalma jikin sa kamar anyi masa allurai na sagar da gangar jiki bashi da kuzari ko kad'an kana kallon sa kasan yana cikin damuwa mara misaltuwa yana k'ok'arin kawarwa ne amma hakan yaci tura. Mama ta bar kusa dashi ta k'arasa d'akin farko ta tura k'ofar ganin nasa d'akin ne ta dawo da baya ta kalli Suhaima tace, "Zo ki tattara min kayan sa mu bar nan." Jikinta a sanyaye ta taka ta shiga d'akin sun d'an jima a ciki kafin su fito da jaka a hannun su hannu Mama da passport guda biyu ta kalle shi tace, "Wuce muje."

A hankali ta tako yazo kusa da ita ya kalli Suhaima suka had'a ido cikin tausayin Yayan nata ta kalli Mama tace, "Mama akwai wasu kayan sa drawer da ban d'auko ba naga kuma kamar documents ne masu mahimmaci." Mama tace, "jeki ki d'auko" ta fad'a tana bud'e k'ofar ta fita ya biyo bayan ta.
Chapter 37 · 0% Book details