← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 131

Sashe 2

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A can gidan su Rauda lokacin duk sun kwanta kasancewar sun saba baccin wuri har Baba ya kwanta kowa yana muhallin da yake. Rauda tana zaune a gefen gadon da suke kwana ita da Ummulkhairi ta saka dogon wando da riga tana zaune tayi tagumi gabad'aya bata jin dad'in komai tunda ta karanta message d'in Anas har lokacin bata dawo walwalar ta ba. Abu taji an buge a falo tayi shiru tana sauraro sai taji shiru sai ta kawar da tunanin kafin ta fara jin motsi a hankali, ta d'auka Baba ne hakan ya saka bata fito ba jin magana k'asa-kasa ya saka ta k'okarin tashi ta d'auki abinda yake taimaka mata wajan tafiya tana takawa a hankali sabida kar suyi k'ara ta k'araso jikin k'ofar, kokwanto take ta bud'e ko kar ta bud'e zuciyar ta duk ta cika da tsoro haka kawai bata san dalili ba.

"Ban gane d'akin nata a nan ba kun san bama so a samu matsala." Abinda taji an fad'a kenan a hankali gaban ta ya fad'i ta zaro idanu waje kafin ta kuma ji ance, "Mu shiga kawai in kuga ba bata nan sai mu shiga wani duk wanda yaso yi mana gardama muga bayan sa."
Rauda ta dafe k'irji a hankali tace, "Wa suke nema?." Tsoro duk ya bayyana a tare da ita tana jikin k'ofa ta kasa kunne babu zato taji an turo k'ofar tayi baya ta fad'i k'asa tare da yin k'ara.

"Shiiiiiii" d'aya daga cikin su ya fad'a fuskar sa a kulle kafin ya kalli d'akin yaga Ummulkhairi a kwance tana bacci dan d'akin da haske yace, "Kika kuma yi mana ihu sai mun kashe kowa na gidan nan." Kai take girgizawa ta kulle hannun ta da baki tana kuka sosai jikin ta na rawa hankalin ta ya kai makura wajan tashi. d'aya ya kalli d'aya yace, "Mu aiwatar da aikin mu kafin azo a same mu." Ba musu d'aya yayi bayan Rauda ya saka mata igiya a wuya wanda yake tsaye a kanta yace, "Fad'i kalmar ki ta k'arshe domin kashe ki zamu yi."

Bakin ta rawa yake hawaye na zubowa daga idanun jikin ta na kyarma ta kasa cewa komai sai ido da take bin su dashi ganin mutuwa kusa "baki da abin fad'a kenan, kai ja igiyar" ya fad'a yana kallon bayan sa. Tamke igiyar yayi a wuyan ta idanun Rauda suka k'afe sukayi ja sai kakari take amma babu damar yin numfashi sun tokare shi sai bak'in idonta ya juya baka ganin sa sai farin da ya koma ja kawai ake gani, k'afa take jurawa tana k'okarin rike igiyar d'ayan da yake tsaye ya rik'e hannayen ta duka.

Su Asad kuwa duk yadda suka so shigowa gidan abin yaci tura an kulle gidan ta ciki gashi basu san hanyar da zasu bi su shiga cikin gidan ba, hankalin Asad ya tashi matuk'a har ya bayyana a tare dashi ya rasa abinda zaiyi ya shiga gidan gashi jikin sa yana bashi sun kashe ta ko suna gab da kashe ta. Tashin hankalin da yake ji tunda Allah ya kawo shi duniya bai tab'a jin irin sa ba, ji yake kamar ana daka naman jikin sa ana soya zuciyar sa a man da yake da mugun zafi.

Mahaukacin dukan da ya yiwa gate d'in har su da suke ciki sai da suka ji suka tsorata wanda ya matse mata wuya ya sake ta da sauri ya k'arasa wajan taga ya bud'e yana kallon harabar gidan ya kuma jiyo dukan gate d'in da akayi.

"Oga akwai mutane a waje fa ya kamata muyi sauri mu bar nan" ya fad'a yana kallon ogan nasu ya kalli Rauda da take kwance babu numfashi a tare da ita yace, "Muyi sauri mu fice" ya fad'a yana fita da sauri yana fitowa suka had'a idanu da Asad da yake tsaye bayan sa Hydar sai Baba da yake tsaye kusa dasu.

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" Baba ya fad'a hankali a tashe yana shiga d'akin da Rauda take ya ganta a kwance babu numfashi yace, "Shikenan sun kashe ta!."
[17/12, 10:39 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*027.*

Kalmar da Baba ya furta ta girgiza Asad, wani irin yammmmm yaji yana shiga ko wanne b'angare na sassan jikinsa take yaji duniyar tana juyawa kansa ya sara zuciyar sa na bugawa kamar ana dukan ganga, gaban sa ya fad'i irin wanda bai tab'a yi ba tunda yazo duniya kamar an zare masa kuzarin jikin sa ya tsaya sak yana kallon k'ofar ba tare da ya aikata komai ba.
"Bata mutu ba tana numfashi, da ranta" ya sake ji Baba ya fad'a bai san lokacin da ya sauke ajiyar zuciya ba sabida wani k'aton dutse da yaji ya sauka daga k'irjin sa hakan ya bada damar saukar numfashin sa daidai.

Mutanen Asad yake kalla ya gansu a zube a gaban Hydar ko wanne guiwa a k'asa ya kalli sauran mutanen falon yaga gabad'aya iyalan gidan su bayyana a wajan Rauda ce da mahaifiyar ta kawai babu da alama tana waja Rauda a d'aki, Baba ya kalli Asad ya kalli mutanen ukun da suke zube a wajan yace, "Kashe Rauda suka so suyi ban san dalilin su ba, me Rauda tayi muku zaku kashe ta? Kisa fa da muke kallo a film itace yau har gidan mu..? bazan lamunci wannan abun ba dole maganar nan taje kunnen hukuma sabida gaba."

Asad ya kalli Hydar shima ya kalle shi suka kalli mutane ukun a tare babban ciki yace, "Ranka ya dad'e wallahi Allah turo mu akayi mu kasheta, batayi mana laifin komai ba alqawari aka yi mana in muka kashe ta za'a bamu kud'i masu yawa, ba'a san ran mu bane ba biyan mu akayi akace mu tabbatar bata numfashi."

"K'arya kuke yi, wanne mak'iyi Rauda take dashi da zai aiko a kashe ta?, me take dashi da za'a aiko har cikin gidan su a kashe ta?. Ita ba y'ar film ko y'ar siyasa ba akan me kuke neman rayuwar ta?" Umma ta fad'a tana fitowa daga d'akin tana goge idanun ta cikin tashin hankali. D'aya daga ciki ya kuma cewa, "Hajiya Sadiya ce ta saka mu, itace tace muzo mu kashe Rauda kada mu bar wata shaida da za'a gane hakan. Mun jima a cikin gidan nan b'uya mukayi sai da dare yayi muka shigo nan."
"Wacece Sadiya?" Baba ya fad'a yana kallon su shi kansa hankalin sa ya tashi.
"Mu dai da haka muka santa bamu san sunan da zamu fad'a maka nata ba."

Baba yace, "Zakuyi bayani a gaban y'an sanda dan wallahi sai nayi k'arar ku bazan zuba ido akan wannan lamarin ba dan ba k'aramin case bane ba." Hydar yace, "kwantar da hankalin ka Baba za'a yi musu hukunci daidai dasu baza mu bari su sha ba zamu tabbatar sun girbi abinda suka shuka. Abu na farko a d'auko ta a kaita asibiti a duba lafiyar ta."

Umma ta kalle shi tace, "Bama buk'atar hakan mun gode basai anje asibiti ba ta farfad'o" Umma ta fad'a ranta a jagule tana kallon su.
Shigowar y'an sanda guda biyu ya saka suka juya suna kallon su suka k'araso kusa da Asad suna yi masa alamun jinjina yace, "Ranka ya dad'e, Allah yaja zamanin ka, gani na fito kamar yadda ka buk'ata." Asad bai tanka masa ba sai Hydar ne yace, "wad'annan zaku tafi dasu a kaisu kotu a tabbatar anyi musu hukuncin da ya dace dasu, kisa suka so kisan ma akan mutum mai mahimmaci a wajan Asad." D'aya daga cikin su yace, "An gama ranka ya dad'e zamu tabbatar sun girbe abinda suka shuka. ku tashi muje shigar dare ce yau zakuyi" ya fad'a yana kallon su da suke durk'ushe akan guiwar su.

"Dan Allah kuyi hak'uri wallahi ba laifin mu bane saka mu akayi akace muzo muyi amma ba aikin kaimu bane ba. Ku yafe mana dan Allah kuyi mana rai, wallahi zaman gidan yari babu dad'i dan Allah ku tallafa mana daga yau baza mu sake irin wannan kuskuren ba" D'aya ya fad'a yana kallon su kamar zai zubar da hawaye.

D'an sandan yace, "yi mana shiru; k'aramin yaro ne kai ko kuma baka da hankali da za'a saka ka wannan d'anyen aikin kayi? Zaku girbe abinda kuka shuka gobe za'a tura case d'in ku kotu zaku gane baku da wayo, ku tashi muje" ya fad'a da tsaya ba shiri suka tashi suka tasa su a gaba suka fita.

Sai a sannan Asad ya lumshe idanun sa ya bud'e yace, "Mama za'a a kaita asibiti." Umma tace, "Bama buk'ata na fad'a muku, abinda muke so a gare ka dan girman Allah ka janye maganar auren Rauda tunda ba itace mace ta farko a duniya ba. ban san dalilin ka na cewa zaka aure ta ba amma ni jiki na yana bani akwai dalilin ka nayin hakan domin ruwa ba sa'an kwando bane. In kana so za'a iya kawo maka mata d'ari koda dga k'asar larabawa ne in badan kana da wata manufa ba meyasa zakace sai ita?. Tunda ka furta maganar nan muke ganin tashin hankalin da bamu tab'a gani ba tunda muke har ya kawo da neman rayuwar ta akan abinda bata furta ta amince bama, dan ni nasan a akan ka akazo kashe ta in kuma tace ta amince kenan a ranar sai an k'ona ta da ranta kenan. Ina rok'on ka dan Allah ku janye maganar nan a bar Rauda ta huta da ranta da kuma lafiyar ta, bana son rasa ta dan Allah ka janye maganar nan a bar mu ji da talaucin mu" Umma ta fad'a tana hawaye tana kallon Asad.
Chapter 2 · 0% Book details