Sashe 122
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yatsu biyu ya saka ya d'ago fuskar ta yana kallon ta sai kuma yaja baya kad'an yace, "kinyi laifi ne?." Jin abinda yace sai tace, "Eh nayi, kamar yadda akayi min amma na hak'ura nake bada hakuri kuma ake wulaƙanta ni." Murmushi yayi mai sauti jin abinda tace ya girgiza kai dan yana mamakin ta gabad'aya bata jin shakkar fad'ar abinda yake ranta yace, "to me kike so ayi miki?."
"Gida zan koma."
"Ni na kawo ki?."
"Suhail ne kuma yanzu zan kira shi ya mayar dani" ta fad'a tana d'aukar wayar ta da niyar kiran sa.
Wutar gidan ce ta d'auke gabad'aya tayi k'ara ta saki wayar ta nufe shi a guje ta fad'a jikin sa ta kank'ame shi tana sake b'oye kanta a k'irjin sa. Ajiyar zuciya ya sauke babu ta yadda zai iya fushi da ita yana sonta son da bai son adadin yawan sa ba, yayi kewar ta kewar da bai san yawan ta ba, yana son kasancewa da ita fiye da tunanin ta. Cikin lokaci kad'an sai kuma hasken ya dawo ta buɗe ido a hankali tana kallon falon ta mik'e da niyar barin jikin sa amma ya rik'e ta ta baya yana kallon fuskar ta sosai.
"Fada min haushina da kike ji" ya furta yana kallon ta cikin murya mai dad'i. Tayi shiru batayi magana ba dan yadda ya rik'e ta yana yi mata magana ya fara canja mata yanayi, dak'yar ta iya cewa, "Kaina kake nuna ko in kula akan lamarin na, gabad'aya baka tani sai a tashi a wuni baka neme ni ba bayan kasan kayi min laifi tun a baya amma baka damu da baka rarrashe ni balle ka bani haƙuri." murmushi yayi ya cize baki yace, "Ya kike so nayi miki Muwaddaty? Bani da nutsuwa ko kad'an, bani da wanda zai bani shawara ke kuma kin nuna bakya son zama dani bazan miki dole ba."
Ta kalle shi shima ita yake kallo tace, "To ba kai bane baka son nazo inda kake in nazo sai ka share ni, tun ranar da Hydar yazo baka sake rarrashi na ba sai ma share ni da kake yi dan kawai baka so....."yatsan sa ya d'ora akan lab'b'an ta ya girgiza masa kai yana kallon idanun ta yana lumshe ido tare da bud'ewa.
Shiru yayi kawai kallon ta yake yi ta sauke saukar da ido k'asa tana jin wani iri a zuciyar ta sai daga baya yace, "Muwaddaty abubuwa sun min yawa baki gani ba? Nida ke waye ya kamata ya yayewa wani damuwa?." Tayi shiru tana jin wani irin abu na zaga jikinta musmaman lokacin da ya dawo da hannun sa cikinta ta sauke ajiyar zuciya mai sanyi cikin murya mai sanyi tace, "Nice, shiyasa nazo nace kayi haƙuri amma sai naga baka so ganina ba."
Zip d'in doguwar rigar ta gaba ya sauke gabad'aya tayi k'asa vest d'in jikinta ya bayyana ya d'aga vest d'in yana shafa cikinta a hankali yace, "waye yace bana so na ganki?." Ta kwanta a jikin sa tana lumshe ido tace, "gashi nan ko kula ni kak'i kayi." Numfashi shima ya sauke yayi shiru na wani lokaci kafin yace, "Nima kiyi haƙuri, shikenan?." Sai ta shiga jikin sa sosai tace, "Iya nan na haƙura banda na baya." Yayi murmushi tare da yi mata kiss a goshi baice komai ba yana sake rik'e ta gam.
"Ina sonki Muwaddaty." Ta rik'e shi kam tana jin soyayyar sa data binne tana tasowa amma bata amsa ba. A daidai kunnen ta yace, "anythings for me?." Juya kanta take a k'irjin sa yayi murmushi ya zare hannun sa daga cikinta ya rik'e ta a jikin sa ya d'auke ta kai tsaye sai cikin d'akin da yake.
Kwantar da ita yayi a hankali yana kallon idamun ta da yake a kulle yace, "I really missed you" ya fad'a yana kwanciya kusa da ita ya jawota jikin sa gabad'aya ta dawo saman sa shi yana k'asa, fuskar ta ya girgiza alamun ta buɗe ido ya goga hancin sa akan nata yace, "Buɗe idon ki."
Kanta ta mayar jikin sa sai kuma taji yace, "Zina!." A hankali ta bud'e ido suka had'a ido duk da babu haske amma tana kallon hasken idanun sa ta shagwab'e fuska zaiyi magana ta hana shi ta hanyar jefa bakin ta cikin nasa dan bata son abinda zai dakatar dashi a wannan lokacin. Sai kuma taji nauyin aikata hakan musmaman da idon ta yake a buɗe tana kallon sa yana kallon ta tayi k'ok'arin zamewa ya hanata yana sake binta da idon sa da yake kashe mata jiki a ko wanne lokaci..........
The love birds 🐦❤️
[17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*091*
Tare suka fito daga bathroom hannun ta rik'e da kanta da kuma bayan ta ta wuce kan stool d'in mudubi ta zauna ta kifa kanta a akn mudubin tare da furta, "Wayyo Allah na." Kallon ta yake ganin kamar bata da lafiya ya saka shi ya k'araso ya tsaya a bayan ta yace, "Baki da lafiya?." Bata d'ago ba ta d'aga masa kai alamun eh kafin ta d'ago tace, "Kaina na ciwo dai bayana da ya rik'e."
"Let me call Dr" ya fad'a yana k'ok'arin wuceta ta rik'e hannun sa ta juyo ta kalle shi tace, "Zan ji sauk'i basai ka kira shi ba, dare yayi fa kalli kaga sha biyu har ta kusa; na gaji ne kawai."
Da kansa ya mata alama da ta tabbatar tace, "Eh babu komai." Ta fad'a tana sake kallon kanta a mudubin ta gashi sosai bayan ta kamar zai cire tasha wahala a hannun sa ba kad'an ba, yadda marar ta ta dinga k'ullewa ta d'auka ma cikin zai zube.
Kallon ta taga yana yi ta madubin sai ta sake sauke kanta k'asa ta kifa kai akan madubin tana murmushi, ya tako ya tsaya a bayan ta yana kallon gadon bayan ta da rabi yake a bayyane kasancewar towel ne a jikin ta. Tabbai ya gani guda biyu dogaye sun zagaya wuyan ta har kafaɗarta ya saka yatsan sa yana binsu a hankali.
Kamar tafiyar maciji haka yake yi da hannun sa fatar ta hakan ya saka ta d'agowa suka had'a ido ta madubin yace, "Kinji ciwo?." Tasan tabon yake nufi sai tayi murmushi ta girgiza kai tace, "Ba ciwo bane." Da ido yayi mata alamar to meye. Ta sake yin murmushi tace, "Duka ne."
Wara ido waje yayi ya sake kallon tabon ya sake kallon ta yaga tayi murmushi ta sunkuyar da kanta yace, "Duka fa." Ta d'aga kai tace, "Uhum. Baba ne ya zane ni lokacin da cikin nan ya bayyana duka jikina ya fashe, sauran tabon sun baje wannan ne dai dashi zan tafi lahira" ta fad'a tana d'agowa amma bata kalle shi ba.
"Oh Allah!" Ya furta a bayyane yana lumshe idanun sa ya buɗe ya koma kan gefen gadon ya zauna yana kallon ta amma baice komai ba cimin tsananin tausayin ta. Jin yayi shiru sai ta share itama tana zaune bata motsa ba balle tayi magana wasa take da zoben hannunta ba tare da ta kalle shi ba.
"Muwaddaty!." Jin yadda ya kira sunan ta sai ta kalle shi ya yafito ta da hannu alamun tazo inda yake ta taso tana takowa a hankali tana k'arasowa ta zauna kusa dashi tare da fad'in, "Cikina Sultan." Hannun ta d'aya ya rik'e ya d'ora daya akan cikin ta yace, "ciwo yake miki? Me kike ji a cikin?. Ki fad'a min na kira Dr" ya fad'a a rud'e yana kallon ta.
Hannun ta ta d'ora akan nasa da yake kan cikin tana kallon sa tace, "ciwon kad'an ne basai yazo ba." K'aramin tsaki yaja ya d'auki waya zai kira Dr, bata hana shi ba ya kira aka d'auka yace, "Yasir kana clinic?." Shiru yayi alamun yana bashi amsa kafin ya kalle ta yace, "Ina da patient."
A speaker ya saka wayar taji Dr yana cewa, "Me yake damun ta?." Ya kalle ta yayi shiru bai magana ba sai zuwa wani lokacin kafin yace, "Ciwon ciki." Dr Yasir yace, "Ranka ya dad'e sosai cikin yake ciwo? Wai dan nasan da wanne irin magani zan tawo mata dashi." Ya kalle ta suka had'a ido sai tace, "Ba sosai bafa Dr, kawai bana jin dad'i ne basai kazo ba yunwa ce ma."
Kallon sa tayi taga ita dai yake kallo bai d'auke ido daga kanta ba sai ya yanke wayar tace, "Bafa ciwo bane ba daka sani baka kira shi ba, babu abinda zai faru tunda wad'acan ranakun suka wuce banyi miscarriage ba bana tunanin akwai abinda zai saka ni yanzu. Yunws ce kawai." ta fad'a tana sunkuyar da kanta k'asa. Hannun ta ya rik'e yana murza goben da ya bata a Cairo yayi shiru na wani lokaci baice komai ba kafin yace, "Wanne lokaci?."
Ta kalle shi tace, "Lokacin da Baba yayi min duka akan cikin, lokacin da Umma ta dinga min fad'a har tace bata yafe min ba, lokacin da nake confusing akan tsakanin ka da Aliyu waye mamallakin cikin nan. Rana ta k'arshe da Umma ita kanta ta d'auka cikin zai fita shine ranar da Mai martaba ya kira mu. Sultan tunda cikin nan bai fita a cikin wad'annan kwanakin dana lissafa ba bana tunanin zai fita yanzu, ban tab'a shiga tashin hankali a rayuwata ba kamar na wad'annan ranakun."
Idon ta yake kallo tana magana sai yaga hawaye suna taruwa a ciki ya girgiza mata kai alamun kar tayi kuka ya furzar da iska yana sake murza yatsan hannun ta yace, "I'm deeply sorry Muwaddaty!." Batayi magana ba itama sai murmushi da tayi kawai ta d'aga kai tana kallon sama kamaar me neman wani abun.