← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 131

Sashe 49

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

       "To ni Mum ya zanyi? In bai neme ni bafa?." A fusace tace, "ke baza ki neme shi ba? Ai naga igiyoyi uku ne na auren sa a kanki kina da hakki a kansa, kin san kalar bak'ar wahalar da nasha kafin a samu azo wannan ranar?. Cikon burina kuma shine kasancewar ki cikakkiyar matar sa." Jidda tace, "Na fad'a miki abinda ya faru ma fa jiya Mum in ta sake faruwa fa me zan masa?."

Mum tayi shiru tana tunani kafin tace, "Barni dashi ni nasan abinda zanyi amma duk da haka kiyi iya bakin k'okarin ki wajan ganin an wuce wajan matsala ce bana so Jidda." Jidda tace, "Zanyi." Mum tace, "ya dai kamata. Ga Eman nan ta tawo zata kawo miki magunguna da zaki sha ki shafa kiyi wanka dasu, ko wanne an rubuta yadda za'ayi amfani dashi a jiki ki karanta dakyau nasan halin ki bakya nutsuwa wani lokacin akan wannan maganin ki nutsu ki karanta sai kiyi amfani dashi."

Jidda tace, "Mum duka maganin nan na meye kike d'ura min?." Mum tace, "baki da hankali, a kaf duniya ina d'aya daga cikin wanda suka san halin uwar mijin ki zatayi k'ok'arin ganin ta mallake ki a yanzu sai abinda tace zakiyi ni kuma badan haka na bari kika shiga gidan nan ba dan a nuna mata akwai iyakar ta ne, shiyasa nake dafa ki yadda ya kamata ta yadda komai zata turo miki bazai same ki ba." Jidda tace, "Ina so nima yadda yake fizge-fizgen nan yana k'in yi min magana nan gaba ya dawo sai abinda nace zaiyi."

Mum tace, "to ki nutsu kiyi abinda duk na fad'a miki, babar sa tana da mugun wayo sosai da iya bakinta zata mallake ki sai kinyi takatsantsan." Jidda tace, "Toh Mum zanyi." Bud'e k'ofa akayi hakan ya saka ta kalli wacce ta shigo tayi murmushi kafin suyi sallama da Mum ta kalle ta tace, "Suhaima." Itama kallon ta take tace, "Amarya."

       Y'ar dariya Jidda tayi Suhaima tace, "In kin gama wayar Mama tana neman ki a apartment d'inta." Jidda tace, "na gama muje." Tare suka fito daga falon suka fito daga b'angaren ta jakadiyar ta tabi bayan ta da sauri duk inda ta gifta ana zubewa ana gaishe su hakan ya k'arawa Jidda girman kai take jin kamar ita kad'ai ce mace ma a duniya.

         A falo suka samu Mama tana zaune tana waya da Hydar akan jikin mai martaba suna k'arasa shigowa ta kashe wayar tana bin Jidda da kallon k'urilla tana son ta gano wani abu a tare da ita, a k'asa Jidda ta zauna tace, "Barka da Safiya Mama." Mama tayi murmushi tace, "Barkan ki dai Daughter, ya kwanan bak'unta? Duk da gidan ba bak'on ki bane amma mijin naki bak'on kine." Murmushi tayi kad'an kana tace, "Alhamdulillah."
"To yayi kyau. Kinga masu yi miki hidima na tura miki ko?."
"Eh Mama, na gansu har mun gaisa."
"Sunyi miki ko a canja?."
"Sunyi Mama ba laifi." Mama bata ce komai ba tayi shiru ranta ya b'aci domin kuwa ta fahimci babu abinda ya had'a Jidda da Asad a daren jiya.

       "Asslamu alaikum" Eman ta fad'a tana shigowa falon. Suka amsa a tare Eman ta k'araso ta zauna a k'asa ta gaida Mama ta amsa fuska a sake tana tambayar ta gajiyar biki. Ta kalli Jiddan tace, "ku koma can sai kuyi hirar." Daman haka suke so suka mik'e suka fita suka koma b'angaren Jiddan.
Suna fita ta d'auki waya ta kira number Asad amma bai d'auka ba sai ta share bata kuma kiran sa ba tana jiran ya kira ta taji dalilin da ya saka baiyi abinda tace masa ba.

     Shi kuwa Asad da ciwon kai ya tashi mai zafi bayan yayi mafarki da Rauda tana kuka sosai tana bazata yafe masa ba tuna mafarkin shine yake sake yautsina masa lissafi hakan ya saka shi zama waje d'aya ba tare da yaje ko ina ba. Yana zaune yake jin k'arar wayar sa bai samu ya d'auka ba dan bata kusa dashi hakan ya saka bai san wanda yake kira ba gabad'aya baya tare da nutsuwar sa. Sake kiran wayar da akayi ya saka shi ya mik'e dakyar ya k'arasa inda wayar take ya d'auka nan yayi karo da sunan Uncle Mubarak yana yawo a kan screen d'in nasa.

      D'auka yayi ya k'arasa ya zauna a akan kujera ya saka a kunne yace, "Barka da safiya Uncle." Yace, "Barka da safiya Ranka ya dad'e." Asad ya yamutsa fuska shi sam baya so yaji suna yi masa irin haka dan yana sarki ai gaba suke dashi kuma iyayen sane bai kamata su dinga girmama shi haka ba duk sai yaji wani iri, wannan dalilin yana d'aya daga cikin abinda ya saka ya tsani mulki.

       "Uncle zamu iya magana dakai?." Daga can b'angaren yace, "Ina sauraro."
"Uncle please ko zaka shigo cikin gida?."
"Umarni za'a bayar aikin na cikawa, gani nan ranka ya dad'e." Asad ya sauke wayar ya kalli missed call yaga sunan Mama ya danna kira ya saka a kunne ta d'auka da sallama kafin yace wani abun tace, "Asad akwai damuwar data hana ka kasancewa da matar ka jiya?."

_Hasbunallahu wani'imal wakil_ ya furta a zuciyar sa jin tambayar da take yi masa ya lumshe idanun sa ya bud'e baiyi magana ba tace, "Ba magana nake maka ba? Ko baka ji bane?."
"Tuba nake Mama."
"Fad'a min dalilin hakan."
"Maamaaaa" yaja sunan ta sosai sai kuma yayi shiru tace, "Amma kace min babu matsala a daren jiya ko? Wulaƙanci ne ya saka ka aikata hakan kome?."

"Kaina ciwo yake min Mama, Allah ya wuci zuciyar ki bada son raina ba nima." Numfashi ta sauke kafin tace, "Kasha maganin ciwon kan?." Kamar yana gaban ta ya d'aga kai kafin yace, "nasha."
"Allah ya k'ara lafiya. Amma ka tabbatar ka sauke nauyin da yake kanka bana son a sake samun matsala matuk'ar kana son na daina yi maka maganar nan. Ko akwai matsala?." Ya girgiza kai alamun a'a kafin yace, "Babu."
"To kayi abinda nace." Shiru yayi hakan ya saka tace, "Yaushe zaka yi zmaan fada ne?."
"Ranar Monday in Allah ya kaimu."
"To yayi, Allah ya kaimu. Akwai wanda ya kawo maka wani abun ne kaci?."

          "A'a." Tace, "to ka nutsu da ka san abinda hannun wanda zaka dinga ci, masu abincin ka na ware su daban na amince dasu baza su cutar dakai ba in kuma matar kace zata dinga yi maka fine." Shiru yayi bai amsa ba jin bai bata amsa ba sai ta tuna yace yana ciwon kai sai ta yanke wayar ya sauke wayar yana sauke numfashi kamar wanda yayi gudu.

"Ya zanyi da Mama? Ya zanyi da yarinyar nan?" Ya furta a bayyane yana dafe kansa jijiyoyin kan suna harbawa. _Ina buk'atar neman magani_ ya furta a zuciyar sa yana shafa fuskar sa cikin rashin sanin abinda zaiyi.

        Wayar sace tayi k'ara ganin mai kiran sai ya d'auka tare da tashi ya fita daga d'akin ya sauka zuwa falon k'asa ya tarar da Uncle d'in sa a zaune yana ganin sa ya mik'e tsaye Asad ya k'araso ya zauna a akan kujera Uncle zai zauna a k'asa yace, "dan Allah Uncle ka zauna akan kujera, bana jin daɗin hakan ko kad'an." Uncle ya zauna akan kujera yana murmushi yace, "to ya za'ayi ranka ya dad'e? Mu talakawan kane dole mu girmama ka yadda ya kamata. Baka ji karin maganar da ake cewa a banza wai talaka ya girmi mai mulki ba?."

Asad yace, "Uncle i need your help." Wambai yace, "wanne irin taimako?."
"Ka kasance a kusa dani ko yaushe Uncle, ban san komai na sarauta ba ina buk'atar ka a tare dani please" ya fad'a yana dafe kansa da suke harba masa sabida ciwo. Uncle yace, "bank'i taka ba zaki, amma ni bani da sha'awar cigaba da mulki gaskiya jira nake litinin tayi ranar da zaka fara zaman fada zanyi resining daga kujera ta zan bi d'an uwana naje naga yanayin jikin sa ko hankalina zai kwanta."

Asad kamar zaiyi kuka yace, "Nima ina so naje jikina yana bani akwai abinda yake faruwa a can d'in, dan na amince da Hydar ne da zan iya cewa bai mayar da hankali wajan nema masa lafiya ba, gangar jikina ne a nan Uncle amma zuciyata tana tare da Abba." Yayi shiru yana had'd'iye yawu na wani lokaci alamun ya gaji da magana Uncle yace, "samu nutsuwa sosai, Sannu."

        Ya cigaba da fad'in, "Ban san komai a nan ba Uncle in ka barni waye zai nuna min yadda abin yake? Ina so ka kasance a side d'ina always please." Uncle ya sauke numfashi yace, "Wannan aikin Uncle d'in kane Yahuza waziri kenan, shine yake da hakkin binka duk inda kake domin a sarautar ma daga sarki sai waziri."
"Ta ya zan iya tafiya dashi Uncle? Kai d'in dai please."
"Ai bazai yu bane Asad, na farko ni na ajjiye sarautar nan, na biyu kuma Yaya Yahuza shine yake da wannan hakkin."

Asad yace, "Uncle nasan definitely Abban Suhail zai ajjiye sarautar nan sabida zai ce bazai yi mulki dani ba kaga sai ayi replacing dinsa dakai." Uncle yayi shiru alamun tunani Asad yace, "Please Uncle kar kace a'a dan Allah badan ni ba dan Allah, ina so mu cikawa Abba burin sa na inganta masarautar nan in ka barni ni kad'ai I can't."

Uncle yace, "Shikenan Allah ya shige mana gaba." Asad yayi murmushi yace, "Amin. Na gode Uncle." Asad ya sake cewa, "Ban san me zance ranar Monday ba Uncle." Yayi murmushi yana kallon sa yace, "Kar ka damu duk abinda yazo zuciyar ka shi zaka aiwatar, kar kayi shayi ko tsoron kowa, kar ka d'auki shawarar kowa, kayi abinda kaga shine daidai a haka mulkin ka zai tafi yadda ya kamata."
Chapter 49 · 0% Book details