← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 131

Sashe 13

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana ji bai motsa ba yana kallon ta yana jin kukan nata wani iri a jikin sa ya lumshe ido ya bud'e a nutse ya kalle ta yaga ta d'ago tana goge idanun ta tana jan numfashi alamun kukan ya tsaya, wayar ta mik'a masa ya karb'a tace, "Na gode." Baice komai ba ya kalle ta suka had'a ido sai ya nuna mata abinci alamun taci ba musu ta zuba tea d'in tana sha a hankali.

Mik'ewa tsaye yayi ya kalle ta kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya fita, ganin ya fita ya saka bud'e bowl d'in dankali ta fara ci da sauri tana ci dan yunwa take ji kawaici kawai take yi bata so taci a gaban sa shiyasa yana barin wajan ta fara ci da sauri-sauri, had'a ido sukayi dashi ya dawo sai tayi sak ta kasa cinye abinda ta zuba a bakin ta sai kallon sa da take yi sai taga yayi murmushi mai sauti kad'an ya d'auki wayar sa ya fita ya barta.

Kunya taji kamar ta nutse dankalin da bata iya ci ba taji ya fita a kanta ta shanye tea d'in duk yunwar sai taji ta k'oshi ta ajjiye cup d'in tana raba idanu. Ba jimawa ya dawo ya kalle ta yace, "Wear your veil." Gani yayi tana k'okarin komawa d'akin ya dakatar da ita ya shiga da kansa yaga mayafin rigar a kan gadon ya d'auko ya bata ta yafa suka fita daga d'akin.

Inda aka tanada dan ajjiye mota a hotel d'in suka k'arasa wajan farar mota babba mai tudu da kyau ya danna remote d'in motar sai ya kalle ta ya bud'e gaban motar ya rik'e ta ta shiga motar ya nad'e keken ya saka a bayan motar ya shiga yaja suka fita daga hotel d'in, kallon sa take a zuciyar ta tana mamakin inda ya samo wannan motar a k'asar da ba tashi ba.

*Nigeria.*

"Finally Asad ya tafi ya bamu waje lokacin da zamu gabatar da abinda muke so yayi yanzu" Fulani Hajiya ta fad'a tana kallon Waziri da yake tsaye a kusa da ita. Murmushi yayi kana yace, "Anyi mai wahalar kam, abinda ya rage a gaba yanzu shine....." kafin yayi magana yaji ance, "Duk yadda za'ayi kar a barshi ya dawo Nigeria nan kusa, kar kuma Mama tasan cewa baya nan in ba haka ba komai ya dawo baya" Aliyu ya fad'a yana shigowa yana binsu da kallo one by one.

Dukkan su bin sa sukayi da kallo cikin tsantsar mamaki da tsoron ya akayi yasan inda suke har yazo ya kuma riski abinda suke cewa, ganin suna kallon sa da alamun mamaki sai ya murmusa yace, "Kar ku damu da ya akayi nasan kuna nan, ku san sani abu guda d'aya duk motsin ku a kan idona kuke yin sa a kuma cikin kunne na yake so kar ku yi mamakin ganina ba tare da kun sanar dani ba."
Hajiya zatayi magana Waziri ya katse ta da fad'in, "Yanzu ya kake ganin za'ayi kenan?."

Aliyu ya kalle su yace, "Ku san yadda zakuyi ku cire masa Mama daga zuciyar sa." Hajiya ta kalle shi tace, "Ban gane ba."
"Bana son sake maimaita magana kema kin san da hakan. Indai har zai yi magana da Mama tabbas hankalin sa zai dawo Nigeria, indai zaiyi magana da Mama nan kusa Asad zai dawo zai kuma iya rabuwa da matar tasa, dole a cire masa Mama a ransa ya daina neman ta a waya ta haka shine zamu samu cikar burin mu."

Cikin gamsuwa yake girgiza kai Waziri yace, "Very good idea our king, but ta yaya hakan zata kasance duba da irin son da yake yi mata?." Aliyu ya kalle shi yace, "Kuyi yadda kuka saba a raba shi da koda magana da Mama in ba haka ba aikin mu ya dawo sabo fil." Hajiya tace, "Wannan ba matsala bane, inda matsalar take aiki baya saurin kama Asad da sauri sai kaga ana ta abu d'aya babu nasara, bamu tab'a yin aiki munyi nasara a kansa ba ko sau d'aya."

Aliyu ya kalle ta yayi murmushi mai sauti yace, "Wannan karon zaiyi tasiri ku gwada, ina tabbatar miki da zaiyi nasara" yana fad'a ya fita da baya yana kallon su suna kallon sa. Waziri ya kalle ta itama ta kalle shi tace, "kana ganin abinda yace za'ayi?."
"Shi za'ayi mana ai maganar sa itace akan daidai."
"Anya ba kan keken b'era yake d'ora mu?."
"Wannan ba keken b'era bane gaskiya ce kuma abinda yace shi za'ayi."
"Ta yaya zamu yi aiki ya kama Asad bayan ba tun yau muka fara ba?."

Kallon ta yayi ya kalli k'ofa yace, "A wannan karon zamuyi nasara na fad'a miki, zamu cire k'aunar babar sa daga zuciyar sa zamu mayar masa da hankalin sa kan matar sa, daga wannan lokacin komai zaizo mana yadda muke so. Tabbas indai zaiyi magana da Rabi zai dawo Nigeria magana da itama tasiri ne a wajan sa ya zama dole mu dakatar da faruwar hakan" ya k'arasa fad'a da murmushi yana kallon ta itama sai tayi murmushin tana girgiza kai cikin gamsuwa da abinda yace.

*Tofa*🤭😂
[17/12, 10:39 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*033.*

*SAUDI GERMAN HOSPITAL CAIRO.*

Tun a farkon asibitin zaka tabbatar da girman sa da kyau da tsarin da yake dashi, iya tsayawa ka kalle shi ma abin burgewa ne balle kuma ka shiga cikin sa kana gani kasan ba'a k'asar ka kake ba tabbas kaje bak'unta wata k'asar Misra.
Rauda tunda ya ajjiye motar take bin asibitin da kallo ya kalle ta yaga hankalin ta nakan asibitin sai ya d'auke kansa daga kanta ya kashe motar ya bud'e ya fita ya zaga inda take ya bud'e baya ya ciro keken da take kai ya kawo shi kusa da k'ofar da take zaune ya bud'e sai a lokacin ta kalle shi.

Hannu ya mik'a mata alamun ta kawo nata tabi farin hannun nasa da kallo mai d'auke da azurfa guda d'aya kalar golden sai wani d'an abin hannu mai kama da jarbi bak'i a zagaye a tsintsiyar hannun sa na dama, hannun nasa ma kawai abin kallo ne, murza yatsun sa yayi suka bata sauti sai ta kalle shi ya motsa duka yatsun hannun nasa alamun ta tawo. A hankali ta d'ora hannun ta kan nasa tana kallo nan taga banbanci tsakanin fatar ta da tasa domin kuwa kamar an d'auko bak'in gawayi ne an d'ora shi a kan farar fulawa.

'In banda ikon Allah ina ni ina shi? Ji hannuna fa kamar na bokaye akan nasa hannun.' Ta fad'a a zuciyar ta a lokacin da ya fito da ita ta zauna akan keken suka shiga ciki har lokacin kallon asibitin take ganin sa hawa-hawa. Labarawa, turawa, Chinese, Japanese sune kawai suke kai kawo a cikin reception na asibitin wanda kallon sa ya kusa saka Rauda rud'ewa sabida ba komai ta gani a zahiri ba.

Wajan eveletor suka k'arasa taga ya danna ya bud'e suka shiga ya kulle ya danna hawa na biyu ba jimawa suka je ya sake bud'ewa suka fita yana gaba tana bin sa a baya. A bakin wani office suka tsaya ya danna door bell d'in jiki ta bada sauti daga ciki suka ji an bada ikon shigowa ya tura k'ofar ya shiga ya bud'e mata ta shigo sannan ya rufe.

Balaraben likitan yana ganin sa ya mik'e tsaye da mamaki da farin ciki ya tawo ya rungume shi yana murmushi shima Asad d'in murmushin yayi suka gaisa likitan cikin harshen larabci yace, "Sheikh Asad daman da gaske zaka zo d'in?." Asad ya murmusa ya shafa gashin fuskar sa cikin larabci shima yace, "gani kana gani." Likitan yace, "gaskiya nayi farin cikin ganin ka sosai dan uwana, zauna mana" ya fad'a yana nuna masa wajan zama da farin ciki a fuskar sa shima haka.

Asad ya zauna ya saci kallon Rauda da gefen ido yaga duk ta rud'e sai ya d'auke kansa daga kallon ta ya kalli Dr Asif yaga ya tashi ya bud'e fridge yana d'auko ruwa da lemo da kayan motsa baki ya dawo ya ajjiyewa Asad a gaban sa yana ta murmushi har lokacin shi kuma Asad fuskar sa dai kadaran kadahan, "Bismillah" ya furta yana kallon Asad bai yi magana ba ya d'aga masa kai kawai sai yayi dariya yace, "Har yanzu kana nan da rashin son maganar ka kenan?." Murmushi kawai yayi bai amsa ba.

Asad ya d'auki dabino d'aya yaci dan kar yaji babu dad'i ya bashi abu bai ci ba sannan ya nuna masa Rauda dake zaune yace, "ga patient d'in da mukayi magana dakai." Asif ya kalle ta ya kalle shi yace, "Ya sunan ta?." Asad ya kalle ta kana tace, "Rauda." Sai da gaban ta ya fad'i rana ta biyu kenan da taji ya ambaci sunan ta sai taji wani iri musamman yadda yake fitar da harafin R d'in kamar a bakin sa aka halicci harafin, ta kalli likitan dan ba larabci take ji ba ta dai d'an fahimtar abu kad'an irin dai na islamiyya dake koyawa.

Dr Asif ya jawo computer gaban sa yana danne-danne kafin ya juyo ya kalli Asad yace, "bata iya tafiya ne?." Asad ya d'aga masa kai alamun eh ya d'aga kai ya danna wani abu a kusa dashi sai ga nurses mata guda biyu kyawawa sun shigo cikin uniform d'in su.

Da harshen su yayi musu bayani da aje da Rauda ayi bincike k'afar ta, ba musu suka kalli Rauda d'aya daga ciki tace, "Muje" cikin harshen larabci ta fad'a kuma kalmar daman ba wani wahala ne da ita ba Rauda taji me tace sai ta danna madannin tafiya suka fita suna rik'e da keken ya bisu da kallo a zuciyar sa yana tunanin da wanne harshe zata yi musu magana in sun tambaye ta?.
Chapter 13 · 0% Book details