Sashe 112
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hajiya tace, "Mune ya kamata muzo da kan mu ranka ya dad'e." Zama yayi ya nuna musu waje su zauna duk suka zauna Hajiya tace, "Ranka ya dad'e nazo da kaina ne neman afuwa akan abubuwwan da suka faru a baya, shiyasa na tawo da duka iyalana dan su taya ni baka haƙuri da kuma neman yafiyar ka."
Asad yayi murmushi yace, "Dan Allah Hajiya a bar maganar nan ta riga ta wuce."
"A'a Asad bata wuce ba, an cutar dakai da yawa ko nace mun cutar dakai Asad. Nayi abubuwa a kan ganin bayan ka ni kaina ban san adadin su ba tun ba'a je ko ina ba na fara ganin sakayyar da Allah yayi maka akan Yahuza. Wallhi tun ranar da kazo duniya nake son ganin bayan ka Allah bai tab'a bani nasara ba. Ina had'a ka da kyawawan sunayen Allah kayi hak'uri ka yafe min abubuwan dukka da suka wuce" ta kalli y'ay'an ta tace, "Ku taya ni rok'on sa."
Babbar yayar su tace, "A madadin iyalan Hajiya muna neman afuwa abinda ya faru a baya ranka ya dad'e, abinda aka aikata wanda aka fad'a da wanda aka aikata ba a fad'a ba muna rok'on mai girma sarki da ya yafe mana mun yi alqwari in sha Allah hakan bazai sake faruwa ba."
Asad yayi murmushi yace, "Dan Allah ku daina wannan maganar bana son ji, komai ya wuce ban rik'e kowa a raina ba." Hajiya tace, "Da gaske mai martaba sarkin mu ya yafe min?."
"Na yafe duk da daman ban rik'e ki ba Hajiya. Ina miki kallon mahaifiyata." Zata fara godiya yace, "Dan Allah kar kice komai, uwa kike a gare ni bazan jure ganin kina zubar da hawaye ba. Komai ya wuce dan Allah a daina kuka."
Ba musu ta goge idanun ta tana murmushi ya kalli y'an uwan nasa gabad'aya dukkan su fuskar su a sake yace, "Ina rok'on ku dukkan ku in akwai abinda ya faru a baya wanda ba'a ji dad'in saba a yafe. Sannan ina so duk inda akaga wani abu ba daidai ba a ciki da wajen masarautar nan ayi hanzarin sanar dani."
Dukkan su da farin ciki suka amsa kafin suyi sallama duk su tafi shi kuma ya tashi ya wuce saman sa Suhail yana bayan sa. A falon Suhail ya tsaya shima yana tsaye yace, "Ranka ya dad'e Hydar fa barazana ne ga rayuwar mai martaba bai kamata a sake dashi ba."
Asad ya sauke numfashi yace, "kar ka damu babu abinda zai faru."
"Haka muke fata, a kwana lafiya" ya fad'a yana juyawa ya sauka shi kuma ya wuce bedroom d'in sa. D'aki ya shiga sai ya tsaya a jikin mudubi yana kallon kansa kafin ya runtse idanun sa yana jin d'aci a zuciyar sa.
_ni kuma in ban zubar da cikin jikinta ba na amince ka kashe ni._ kalaman Hydar suka fad'o masa ya cire rawanin kansa ya kalli wayar sa ya d'auka da niyar kiran ta sai kuma ya ajjiye yaja k'aramin tsaki ta ko wanne b'angare haushin ta yake ji a zuciyar sa shiyasa yayi banza da ita bai sake waiwayon ta ba har yau. _Yana dakyau ka neme ta kodan abinda Hydar yace._ Zuciyar sa ta fad'a masa ya runtse idanun sa a bayyane yace, "In sha Allah babu abinda zai faru da ita, ina tare da ita a ko yaushe."
Fuskar Mama ta fad'o masa sai ya d'auki wayar sa ya kira Suhaima tana d'auka yace, "Mama."
Suhaima tace, "Har yanzu bacci take." Datse kiran yayi ya kama k'ugun sa sosai kansa yake masa ciwo har jiri yake ji yana d'aukar sa. "Hasbunallahu wani'imal wakil" ya furta a bayyane yana zama a gefen gadon ya dafe kansa lokacin da Jidda ta saka a kashe shi har ya kamata tana waya ya fad'o masa.
Saurin kawar da tunanin yayi ya tashi ya shiga wanka. Wankan ma da ruwan magani ya yishi bayan ya fito ya shafa mai da magani ya fesa turare mai magani ya saka kaya wanda aka turara su da magani. Hannun sa ya d'ora a cikin sa baya jin yunwa ko kad'an gashi shidan yasan tun daren jiya bai sake cin komai ba.
_Wallahi na tsane ka bana qaunar ganin mazinaci._ kalaman Rauda suka fad'o masa abinda yaji a zuciyar sa sai da ya datse labban sa da hakorin sa ya runtse ido yana sauke numfashi zuciyar sa na rawa. Bai san adadin lokacin da ya d'auka a haka ba sai da dare yayi sosai ya sauko kai tsaye b'angaren mai martaba ya shiga.
Kamar yadda yayi tunani yana zaune akan sallaya ganin hakan sai ya koma ya shiga d'akin da Aliyu yake kwance. A zaune ya same shi shima a kan gado idanun sa a waje ya yaga rigar jikin sa yayi tagumi ya zubawa waje d'aya ido kamar mai kallon wani abun.
Ganin Asad ya shigo ya saka Aliyu zabura yana kallon sa har ya k'araso inda yake ya zauna ya dafa kafad'arsa yace, "Allah ya baka lafiya Aliyu." Kai Aliyu ya fara girgizawa yana fad'in, "Ba sunana Aliyu ba sunana Asad, ni sarki ne ina hawa doki ana zagawa dani, ina zuwa na bawa yara y'an islamiyya allo a lokacin bikin sauka. Ka daina cemin Aliyu zan iyawa yin komai akan hakan."
Asad ya runtse idanun sa ya buɗe yana kallon Aliyu cikin tausayin halin da yake ciki ya zuba masa ido kawai baiyi magana ba. K'arar buɗe k'ofa yaji hakan ya saka shi ya juya ganin mahaifinsa sai ya mik'e tsaye har ya k'arasa ya dafa kafaɗarsa sa yace, "me ya fito da kai a daren nan?." Asad ya nuna Aliyu yace, "hankalina yak'i kwanciya."
Mai martaba ya kalli Aliyu yace, "zai samu lafiya da iznin Allah shiyasa na zab'i a barshi a nan yana karb'ar magani." Asad ya girgiza kansa yace, "Abba jikin Mama ma babu dad'i." Numfashi ya sauke yace, "dole ta samu gigita da rud'ani a wannan yanayin da ake ciki amma itama zata samu lafiya."
Mai martaba ya kalle shi yace, "Zuciyar ka a wanke take Asad kyakykyawar zuciyar da kake da ita Allah bazai bawa kowa damar cutar da kai ba." Asad yyi shiru ya sunkuyar da kansa mai martaba yace, "Ka koma kaje ka huta gobe akwai zaman da zaka gabatar domin gyara mulkin ka. Bana son a sake samun matsala a wancan karon ma kaine ka bada dama ka dinga karb'ar duk abinda babar ka tazo dashi. A wannan karon bazai faru ba." Kai ya girgiza kai kafin yayi masa sallama ya wuce ya koma yana ji kamar ana tura shi in yana tafiya sabida jiri.
*☆☆☆*
"Duk abinda kuka aikata yazo kunnena Sadiya, duk yadda kuke da Rabi'a ta d'auki aminci ta baki tun kuna makarantar secondary a Kano kuke tare amma ki rasa abinda zaki saka mata sai da cuta, cutar ma kuma wai kisa Sadiya? Yaushe kika zama y'ar ta'adda ban sani ba?" Daddy ya fad'a da alamun bacin rai a tare dashi yana kallon Mum.
Mum tana kuka sosai tace, "Ambassador ka tsaya nayi maka bayanin abinda ya faru, banyi hakan da....." dakatar da ita yayi ta hanyar fad'in, "Rufe min baki domin baki da wani kalami da zaki fad'a min na amince. Sabida tsabar son zuciyar ki aminiyar ki kike k'ok'arin kashewa bayan kin rabata da d'an da ta haifa sabida wani banza burin ki na iska. Kin d'ora y'arki a tafarkin zina da aure a kanta take zmaan fasiqanci da Yayan mijinta kuma duk kina sane kikayi shiru sabida cikar burin ki."
Mum tace, "Wallahi ban san ba Asad bane, bata fad'a min ba, ban san zaman fasiqanci sukeyi da Aliyu ba ka yarda dani."
"Babu abinda zaki fad'a na yarda dashi, kin cutar dani kin kuma cutar da kanki da rayuwar yarki. Baxan lamunta ba wallahi bazan iya cigaba da zama da mata irin ki ba, daga asibitin nan kar ki sake ki koma min gidana kije can ku k'arata dake da y'ar taki da kuma d'an shegen da ta haifar miki da aure a kanta, wannan bak'in zunubin bazai zauna a gidana ba domin wata rana kar fushin Allah ya shafe ni."
Hankalin Mum ya sake tashi ta zube a k'asa tace, "Kar kayi min haka Daddy wallahi duk abinda ya faru bada son raina ba ka tsaya nayi maka bayani."
"Ni na tsaya na saurare ki? Har abada bazan tsaya ba domin ban san me kika k'unso kike so ki kashe ba nima dan tunda kikayi yunƙurin kashe Rabi baki duba alaqar ku babu wanda zaki bari a duniya. Ga takardar sakin y'arki nan an bani sai kije da ita ku k'arata ko babu komai tahiri ya kafu a kanta wanda baza'a manta dashi ba a duniya. Mace ta farko da tayi zina da yayan mijinta y'ar kice, mace ta farko da taso kashe mijin ta sabida karta rabu da yayan mijin nata y'ar kice, mace ta farko da sarki guda shugaban al'amma ya fara sakin ta. Kar ki sake ki dawo min gida bazan iya zama da dake da kuma y'arki ba" ya fad'a yana cilla mata takardar hannun sa.
Har ya juya zai tafi yaga Eman na kuka sosai ya damk'o hannunta yace, "muje kar kema ta lalata min ke da bak'ar zuciyar ta!" Ya fad'a yana jan Hannun Eman suka bar wajan tana kuka sosai Mum tana kuka.
#FitattuBiyar
#Nanahaleema
[17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*086*
Gabanta yayi mugun fad'uwa ganin da wanda suka had'a ido ta sauke ido k'asa bata motsa ba shi kuma bai daina kallon ta ba da alamun b'acin rai a tare dashi. Suhail ne ya fito daga motar ya bud'e mata baya da hannu ya mata alamar ta shiga kafin yace, "Ranki ya dad'e bismillah." Ba musu ta shiga ya kulle musu k'ofar ya tsaya a bakin motar ba tare da ya koma ba.
Shiru babu wanda yayi magana cikin su ita shi yake kallo cikin tsantsar b'acin rai da takaicin abinda ya gani, d'ago kai tayi ta kalle shi suka had'a ido ta sunkuyar dakai k'asa ta sosa kanta kad'an kana tace, "Barka da dare." Banza yayi mata yana kallon ta ba tare da ya bata amsa ba sai tamke fuska da yayi yana hararar ta.