Sashe 101
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nan ma falon yayi shiru sai kukan Mama da ya fara tashi tace, "Nasan nayi duk abinda akace nayi dan ganin y'ay'ana sun zama sune gaba a masarautar nan, amma ban tab'a yunƙurin kashe wani ba, ban tab'a yunƙurin ganin wani ya cutu ta dalilina ba."
"Har matar Asad Rauda?" Ya jefa mata tambayar yana kallon ta.
Kai ta sunkuyar k'asa ta kasa magana ganin hakan sa yace, "ki amsa mana, kince baki tab'a yunƙurin kisa ba shine na tambaya har ita?." Nan ma shiru Mama tayi ta kasa amsawa sai hawaye da take tana sauke numfashi a hankali cikin tashin hankali.
Mai martaba ya kuma cewa, "Nasan baza ki amsa ba daman dan kin san kin aikata ba sau d'aya ba ba kuma sau biyu ba, ita kuma yarinyar tayi miki alkhairi ba sau d'aya ko biyu ba, domin ina so kowa yasan ta silar ta na samu lafiya har nake tafiya yau kuka ganni a zaune a gaban ku."
Asad ne ya kalle shi alamun mamaki yace, "Eh Asad, nasan kaima baka sani ba dan babu wanda ya sani daga ita sai Mubarak sai kuma Yayan mahaifiyar ta Baba Malam, ta silar sa da tata silar na samu lafiya. Ina so kusan duk dare sai anzo an kaini wajan sa yana min magani wanda nake jin dad'in sa sosai ba kad'an ba, duk cikin maganin da ake bani ban tab'a jin dad'in ko wanne ba sai nasa. akwai ranar na same ta a can gidan an kaini ita kuma Kawun nata ya kirata ta kawo ruwan da za'a bani magani a lokacin akwai allurar da ake min a hannu Mubarak ta nuna ta san allurar lokacin da suka je can Cairo nema mata lafiya ta nemi k'arin bayani a kanta an kuma tabbatar mata ana yiwa mutumnin da ba'a so ya motsa ne, kamar wanda za'a yiwa aiki ko kuma wanda ake som cutar dashi ta hanyar allurar" ya dakata da magana yana kallon yanayin fuskar kowa da yake wajan.
Mai martaba ya kuma cewa, "Nan take duk da dare ne ta kira likitan da ya sanar da ita a can ta d'auki hoton allurar ta tura masa ya tabbatar itace ya kuma turo mana maganin ta a lokacin ya kuma ce kar a sake yiwa wanda ake yiwa ita domin nan gaba zata kashe masa gab'obi ne dan bata sanar dashi nine ba, daga wannan lokacin aka daina yi min wannan allurar aka koma yi min wacce ta kasance maganin da take karya ta. Ta silar ta na samu lafiya ita da dangin ta domin badan ita ba da yanzu wataƙila ina kwance har yanzu."
Kowa yayi shiru babu wanda yake magana sai Suhaima tace, "Muma munje wajan sa ta silar ta Abba, domin munje ba sau biyu bama samun ganin sa sai da muka je har gidan su Mamata ta saka ta raka mu ya bamu magani lokacin da muke d'auka Aliyu Asad ne, mun karb'o masa magani mun kuma karb'o maka mun karb'owa Yaya Hydar ma. A hanyar mu ta dawowa akaso kashe Mama badan tayi hanzarin janye Mama ba da yanzu Mama ta jima da rasa ranta. Itace ta cece Mama a wannan lokacin ta silar ta Mama take zaune yanzu badan haka ba da yanzu mota ta markade ta tuni.'
Mai martaba yace, "Ta yaya ta iya zuwa gidan su neman alfarma bayan tarin abubuwan da tayi musu a baya? Ta yaya ta iya had'a ido da y'ay'an gidan har ta iya shiga ciki?. Koda yake jiya ma taje cikin gidan nasu ta silar Mahaifiyar ta ta sake karb'owa Aliyu magani gashi har zaune ana magana dashi, ko ina izza da raina na k'asa da ita d'in suka tafi oho" ya fad'a yana kallon ta Mama ta runtse idanun ta.
Falon ya sake yin shiru babu wanda ya kuma magana a cikin su Asad ya kalli Rauda suka had'a ido sai tayi saurin d'auke idonta daga kallon sa gabanta yana fad'uwa sosai ita har yanzu bata tabbatar da cikin wanda yake jikinta ba.
"Aliyu yayi mulkin katagum na watannin da suka wuce, Asad ya kasance baya tare damu a yanayin da muke d'auka shine a tare damu Aliyu ne baya nan, Aliyu ya goge duk wata alamar da ake gane su da tsakanin sa da Asad hatta k'aramin yankan allurar da yake hannun Asad wanda babu wanda ya san dashi daga shi sai matar sa Aliyu yayi irin sa dashi ya yiwa matar sa barazana har ya sake ta a madadin Asad ita kuma ta amince. Ta hanyar azurfar hannun Asad tana nan yaji lokacin da yake fad'a akwai alamar shi kuma yayi amfani da wannan damar da ya dawo yaga a hannun da yake shima yayi irin sa. Asad ya dawo shi kuma sai ya koma muku Aliyu duk dan sabida ya aiwatar da komai cikin sauk'i duk da Aliyu yasan shine haka Jidda ma amma basu nuna ba duk tunanin su hankalin sa ya bar jikin sa, babu wanda yasan ba Aliyu bane daga shi sai Aliyun sai matar sa Jidda sai kuma y'an bayan fage."
Ya kalli su waziri yace, "Dashi kuke meeting d'in kashe shi, badan shi ba da yanzu mahaifiyar jidda ta kai ga kashe Rabi shine yayi maganin abun dan ya gani da jakadiyar ta Ladidi suke yin komai. Shi Jidda taso a kashe bata san yasan shirin ta ba dan Asad d'in yanzu bana da ba bane ba."
Ganin kowa ya kasa motsi sabida abinda suke ji kamar almara ya saka yace, "Lokaci yayi da ya kamata kusan wacece master sannan kuma su waye wad'anda nake kira y'an bayan fage."
Ya kalli k'ofa yace, "A shigo min dashi." Nan take aka shigo da Hafiz duk an d'aure shi jikin sa duk ya b'aci haka fuskar sa tayi bak'i matuk'a sabida wahala. Umarni ya bawa wanda suka kawo shi da su koma suka koma suna godiya ya kalli kowa yaga kowa kallon Hafiz yake yi.
Mai martaba yace, "Nasan kowa yana mamakin ganin Hafiz, kowa yasan Hafiz da Asad abokai ne shine manager director a company sa, shine yake k'okarin kare shi daga masu son ganin bayan sa a zahiri kenan. Tsakanin sa da Suhail ba'a shiri a zahirance Hafiz yana nunawa Asad Suhail yana so ya cutar dashi ne shiyasa baya so ya ganshi a kusa dashi, amma a bad'ini shine yake k'okarin cutar da Asad shiyasa baya so yaga Suhail a kusa dashi. Suhail yayi kwantan b'auna dan cimma nasara a b'angaren kare lafiyar abokin sa na yarinta Asad. A yayin da Hafiz yayi kwantan b'auna ya cimma cutar da abokin sa na yarinta Asad."
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!" Aka fad'a baki aka fad'a gabad'aya ana kallon Hafiz. Mama da take kuka tace, "Hafiz! Hafiz kai da kanka?." Ya d'ago ya kalli Mama cikin muryar sa da ta d'an yi k'asa yace, "kar kayi mamaki mama, jin wad'anda zan ambata yanzu sai yafi jefa zuciyar ki cikin mamaki."
"Kenan yasan master planer?" Fulani Hajiya ta fad'a tana kallon sa. Yace, "Kwarai na Santa domin ita nake yiwa aiki, ku bakwa ganin ta ni kuma kai tsaye nake magana da ita, bama iya ita kad'ai ba hatta wanda suka bayan ta na sansu."
"Fad'a mana muji wacece" ta fad'a tana kallon sa. Yayi murmushi yace, "kun shirya jin wacece master planer?."
Mai martaba yace, "Fad'i abinda yake bakin ka kai tsaye." Ya kalle su dukkan su ya saukar da ido k'asa yace, "Duk wad'annan abubuwan da suke faruwa ba kowa ne yake shirya su ba face...........!"
Guess who?🏃🏼♀️🤔😂
[17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*080*
K'irjin kowa motsawa yake a cikin su burin su suji abinda Hafiz zai fad'a dukkan su sun zuba masa ido suna kallo hankali a tashe tsoro da al'ajabi ya bayyana k'arara akan fuskar su. Hafiz ya sake yin shiru ya kalle su dukkan su yace, "Kuna tunanin wacece master planer..? Hmm abinda ya dace kuyi tunani shine waye master planer dai domin ba mace bace namiji ne."
Fulani Hajiya tace, "kar ka raina mana hankali mana, ta yaya zai kasance namiji bayan ni nasan macece." Hafiz yace, "murya kike ji amma kin tab'a ganin ta a zahiri?." Shiru tayi ta kalli waziri suka had'a ido ta dawo da kallon ta ga Hafiz tace, "Ban tab'a ba." Hafiz yace, "ta tab'a amincewa kunyi video call?."
Ta girgiza kai alamun a'a ya sauke numfashi yace, "Shiyasa nace miki namiji ne ba mace ba."
"To waye ka fad'a mana ka tsaya kana rainawa mutane hankali, ka fad'a way......."
"Hydar ne!" Ya katse Mama da ihuu yana kallon ta idanun sa a waje.
Dummmmm zuciyar kowa ta buga a wajan nan duk suka juya suka kalli Hydar da yake zaune kansa a k'asa tunda aka fara wannan abin baiyi magana ba kuma bai d'ago kansa ba har lokacin, mamaki kwance a fuskar su dukkan su Mama ta kalli Hydar ta kalli Hafiz tace, "Wanne Hydar d'in kake nufi?."
"Hydar da kika sani Mama, Hydar da yake tare dake a ko yaushe, hydar da yake kwanciya rashin lafiya, Hydar d'in Asad, Hydardai naki shi nake nufi" ya fad'a yana kallon ta itama kuma shi take kallo idanun ta a waje gabad'aya.
Suhaima ta kalli mahaifin su dan tana so tayi magana amma tana jin tsoro shima ya kalle ta yace, "kowa yana da ikon yin magana a wannan lokacin." Jin hakan ya saka Suhaima tace, "K'arya kake! Kwatankwacin wannan abinda aka lissafa Yaya Hydar bazai aikata shi ba. Kowa ya shaida son da Yaya Hydar yake yiwa Yaya Asad bazai cutar dashi ba, ko yaushe ciki bashi kariya yake taya zaka ce shine master planer?."
"Da kariyar yake amfani yake cutar dashi a ko yaushe, Hydar ya wuce tunanin ki yadda kuke kallon Aliyu mai wayo da makirci Hydar ya dame shi ya shanye" ya sake fad'a yana kallon Suhaima da itama shi take kallo fuskar ta ta jiqe da hawaye. Fusata Mama tayi ta zabura ta mik'e ta tsinke Hafiz da mari ta nuna shi da yatsa tace, "In ka sake furta magana makamanciyar wannan a kan Hydar sai na saka anyi maka hukuncin da har ka mutu baza ka manta ba."