Sashe 93
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Anas ya girgiza kai yace, "Haka ne Baba" Sai kuma yayi shiru ya sake sunkuyar da kansa k'asa ya danne raunin da yake ji a zuciyar sa baya so ya bayyana amma ya kasa, Baba yace, "Na baka Rahma halak malak Anas, za'a cigaba da shirye-shiryen biki kamar babu abinda ya faru in Allah ya amince. Kayi hak'uri nasan har abada baza k daina jin ciwon da kake ji ba; amma ka jure wata rana sai labari."
Anas bai amsa ba dan kansa sarawa yake yi zazzaɓi yana neman rufe shi bai san ya akayi bakin sa ya furta zancen k'anwar Rauda ba kawai taji ya fad'a ne hakan ya saka shi yin shiru bai ce komai ba. Baba yace, "Ya kake gani a sanar da iyayen ka abinda ya faru ko a'a?." Anas ya d'ago jajayen idanun sa ya kalli Baba yace, "A'a Baba, a cigaba da shiri kawai Allah yasa hakan shine mafi alkhairi." Baba yace, "A'a Anas in akayi haka kamar an mufurce su ne, kar nan gaba su samu labari suga kamar bamu kyauta musu ba."
"Babu komai Baba, basai an fad'a ba bazasu tab'a sanin ba ita bace" ya furta a hankali idanun sa a lumshe.
Baba yace, "To shikenan. Allah ya tabbatar da alkhairi yasa hakan ya samarwa da kowa farin ciki a zuciyar sa. Ya baka ikon jure abinda kake ji a ranka daga nan har lokacin da Allah zai kawo maka sassauci a zuciyar ka." Kai yake girgiza kai yace, "Amiin Baba."
Mik'ewa Anas yayi yace, "Baba zan koma." Baba ma ya mik'e yace, "Anas naga yanayin ka ya canja gabad'aya, Anya zaka iya tafiya kai kad'ai?." Anas ya murmusa yace, "Babu komai zan iya. Sai anjima Baba" ya fad'a yana fita Baba yabi bayan sa sai da ya tabbatar ya shiga mota ya tafi sannan ya koma cikin gidan jikin sa a sanyaye matuk'a.
Yana shiga wajan Umma ya wuce ya same ta ita da Inna ne a zaune Baba ya zauna yace, "Kamar kun san dukkan ku nake nema." Inna tace, "Lafiya na ganka a sanyaye haka?." Baba yace, "Yaron nan Anas shine ya karya min zuciya wallahi, kuka ya dinga yi k'aramar yaro k'arami jikin sa har rawa yake. Yana son Rauda amma Allah bai rubuta Rauda matar sa bace ba abin tausayi" ya fad'a a sanyaye yana sauke numfashi.
Umma tace, "Malam dan ka dage ne amma ni banga dalilin sanar da Anas ba tunda bamu da tabbacin sakin nan baiyu ba a kanta. Allah ya sani ni hankalina yafi kwanciya da Anas wallahi." Baba ya kalli Umma yace, "kina son maimaita magana guda d'aya, aure ne akwai shi akan Rauda dan babu yadda za'ayi mutum kamar Asad yazo yayi mana k'arya kawai dan cikar burin sa. Kina so muyi mata aure akan aure ne? Koda ma ace babu batun auren haka zamu bawa Anas auren ta da ciki a jikin ta?."
Jin Baba ya hasala sai Umma tayi shiru bata ce komai ba Baba yace, "Anas yayi tawakkali ya amimce da k'addara ni kuma na bashi Rahma a madadin Rauda dan haka biki baza'a fasa shi ba amma ya tashi daga kan Rauda ya koma kan Rahma" Baba ya fad'a yana kallon su. Inna ta bud'e baki tace, "Kamar ya kenan?."
"Kamar yadda kika ji na fad'a. Ya amince da maganar Rahma shine ya fara nema ni kuma na bashi, dan haka duk wani shiri da kuke akan Rauda ya tashi ya dawo kan Rahma dan yau saura kwana tara auren ta da Anas."
Inna ta kalli Umma itama ta kalle ta cikin mamaki tace, "Malam kenan auren cushe za'a yiwa Rahma kome?." Baba yace, "hukuncin dana yanke kenan babu ruwan ki dawai auren cushe ko akasin sa, Rahma Anas zata aura madadin y'ar uwar ta Rauda." Inna tayi dariya kad'an tace, "Ban damu da kud'in da Anas yake dashi ba abinda na sani shine wallahil azim babu wanda ya isa ya yiwa Rahma auren dole, in bata son Anas wallahi bazata aure shi ba dan ni ba ita bace da zan bari a d'auki y'ata a aurar ban sani ba sai dai kawai a kawo min sadaki" ta fad'a tana nuna Umma da take zaune tana kallon Baba da shima ita yake kallo.
Baba ya girgiza kai ya kalle ta yace, "Lallai Asabe ni kike kallo kike fad'awa ban isa na aurar da Rahma ba, shikenan mu zuba nida ke kiga in ban aurar da ita d'in ba." Inna tace, "Oho dai, ni ba irin ka bace da son kud'i zai rufe min ido nakai y'ata inda zata wahala a dinga yi mata kallon matar cushe, wallahi bazata sab'uba bingida a ruwa." Baba ya mik'e yaja k'wafa ya ware muryar sa yace, "Ke Rahma!." Daga d'akin Rauda ta amsa ta fito jikin ta a sanyaye dan duk taji abinda ake cewa ta fito ta tsuguna tace, "Baba gani."
Baba ya kalle ta yace, "Anas ya nuna yana son ki zai aure ki madadin y'ar uwar ki Rauda kin amince ko a'a?." Shiru Rahma tayi ta kalli Inna ta suka had'a ido ta dawo da kallon ta ga Baba tayi shiru bata amsa ba. Baba yace, "Malama magana nake miki kina kallona, kin amince a d'aura auren ki sati mai zuwa?."
Rahma ta sunkuyar da kai k'asa tace, "Baba a bani lokaci nayi magana da Inna ta."
"Babu lokacin da za'a baki malama, ki fad'i abinda yake ranki bamu da lokacin da za'a baki har kiyi magana." Rahma tayi shiru bata ce komai ba Inna tace, "Matuk'ar bata amince ba wallahi sai dai ka bashi Ummulkhairi amma badai Rahma ba, bazan lamunci auren dole a kanta ba haka kawai nan gaba bazai goranta mata yace ba ita yake so ba bashi ita akayi." Shiru Baba yayi yana kallon Inna yadda take fad'ar magana kamar ba shine yake mata magana ba yaja k'wafa ya fita baice komai ba.
"Jeka, wallahi bazan amince ayi mata abinda aka yiwa Rauda ba gashi ana ta samun matsala har yanzu bamu da tabbacin da gaske akwai auren a kanta ko babu ga ciki kuma. Ina! ni wallahi bazan amince ba, ke Rahma tashi muje" ta fad'a tana kallon Rahma kafin ta fita itama tabi bayan ta. Murmushi Umma kawai tayi dan bata da ta cewa dan ta lura hak'urin ta shine yamr cutar da ita wani lokacin ya zama dole ita ta dage akan sai an tabbatar da auren Asad a kan Rauda in ba haka ba itama bazata koma masa ba.
*☆☆☆*
Haka ya kwana babu walwala a tare dashi tunda yayi sallar asuba bai kwanta ba yana zaune yana lazumi har gari yayi haske sannan ya fara karatu bayan ya kammala yayi wanka ya shirya cikin shigar manyan sarakai yayi nad'in malamai akan hular da ya saka shigar ta amshe shi sosai ya sauko zuwa k'asa.
Falon shiru babu kowa yana bin wajan da kallo yana tuna inda Rauda ta zauna jiya kafin ya janye idanun sa daga kallon wajan ya zauna a kan kujera ya d'auko waya yana dannawa, ajjiye wayar yayi a gefe ba jimawa aka danna door bell ta jikin k'ofar cikin maganar sa mai d'auke da isa da k'asaita yace, "Shigo."
Da sallama ya shigo jikin sa har rawa yake yi ya zube a k'asa yana fad'in, "Barka da safiya Sarkin sarakuna, barka da tashi farar atafa, barka da fito taurarin sama sha ado. Allah ya k'arawa Sarki lafiya da tsahon rai, Allah ya k'arawa mai martaba lafiya yayi rik'o da hannun Fulani mai babban d'aki. Ranka ya dad'e" ya fad'a yana yi masa jinjina cikin girmamawa.
Asad ya sauke numfashi a hankali ya amsa da amin kafin yace, "Sarkin mota." Jikin sa har rawa yake yace, "Ranka ya dad'e."
"Kasan meyasa na zab'e ka a zaman gidan nan?."
"Ban sani ba Ranka ya dad'e."
"Sabida kana da amana, tun lokacin Abba na shaida hakan a tare dakai" yayi shiru kafin yace, "Bana son kowa yasan ina garin nan, bana so kowa yasan da abinda yake faruwa a gidan nan kana jina?."
"Ina sauraron mai martaba, in sha Allah mai martaba bazai same ni da cin amana ba, zan riƙe amanar mai martaba daga nan har na bar duniya." Kai Asad ya d'aga yayi shiru na wani lokacin kafin yayi masa alama da hannu da ya tashi yayi masa sallama ya fita da sauri.
Numfashi Asad ya fitar ya kalli sama yana kallon adon da aka yiwa rufin d'akin yana tunani, yana so Rauda ta dawo rayuwar sa a wannan tsaka mai wuyar da yake ciki ko zai samu sassaucin abinda yake ji a ransa amma kuma yana so ya bata hutu dan yasan akan gaskiyar ta take shima akan tasa gaskiyar yake. Hannun sa ya d'ora a kan cikin sa yunwa yake ji sosai amma baya tunanin zai iya cin wani abun da bashi da wannan nutsuwar ko kad'an.
Ido ya sauke daga k'asa wayar sa yaga tana k'ara ganin mai kiran sai yaja k'aramin tsaki ya d'auke kansa sunan Jidda ya fad'o masa a zuciyar sa, runtse ido yayi zuciyar sa na bugawa ya mik'e ya fita daga falon zuwa harabar gidan, zaga gidan kawai yake yi shi kad'ai yana takawa har ya gaji ya sake komawa ciki ya zauna ya fara aiki a laptop.
*☆☆☆*
"Sau nawa zan fad'a nace maka Aliyu bazai mana aikin komai ba gabad'aya ya canja dabi'ar sa mu nemi wani ya bawa Asad wannan maganin da yanzu mun wuce wajan" Hajiya ta fad'a tana kallon Waziri da shima ita yake kallo yace, "Kwarai da gaske maganar ki haka take, gashi ya kasa yin komai har kawo yanzu. Wasa da hankali yake mana ya mayar damu tamkar ball ta ko ina buga mu yake yi son ransa, muma zamu buga shi son ranmu kuwa."