Sashe 17
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hannu Dr ya bashi shima Asad d'in ya bashi suka gaisa kafin ya kalli Asad yace, "Sister nan naka tana da kirki sosai akwai saurin sabo ba irin ka bace." Banza Asad yayi masa shima kuma bai damu ba ya kwashi kayan sa ya fita Asad dake tsaye hannun sa cikin aljihu ya kalle ta ya kalli kujerar da Dr ya tashi ganin ta gab da Raudan ya sake kallon ta suka had'a ido tace, "Ina kwana."
Banza yayi mata bai amsa ba ya zagayo inda kujerar take kamar zai zauna ya tsaya yana kallon ta yace, "last warning kar na sake ganin hakan." Da mamaki ta kalle shi taga ya sake tamke fuskar sa sai ta kasa tambayar sa me yake nufi ta sauke kanta k'asa ba tare da tasan akan abinda yake magana ba.
Wayar ta taga ya d'auka yana juya ta a hannun sa kafin taga ya zare sim card d'in ciki ya raba shi biyu ya saka a shara ya d'auko sabuwar waya a aljihun sa ya ajjiye mata a kusa da ita ta hannun sa kuma yayi danne-dannen da zaiyi sannan ya saka a shara.
Rauda kallon ikon Allah kawai take yi gashi ya had'e fuska yayi mata kwarjini ta kasa kallon sa balle tayi magana, kamar a mafarki taji yace, "in akwai sauran abinda kika san ya baki throw it away" ya fad'a yana kallon ta.
Rauda tayi shiru cike da mamakin sa dan in ta fahimci me yake nufi kenan yasan Anas ne ya bata wayar shiyasa ya cillar?, yasan shine ya bata sim card d'in shiyasa ya karya?, kenan kishi yake da ita kome?.
Shiru ya ratsa tsakanin su kafin a shigo d'akin Rauda ta kalli wajan banda Asad da ya fara danna wayar sa, "morning beautiful face" Muhibba ta fad'a tana kallon sa da murmushi a fuskar ta. Tsaki yaja domin shi ya tsane ta gabad'aya baya son ganin ta amma ta nace masa duk inda yaje sai tayi masa magana ya rasa dalilin hakan, bai d'ago ba balle ya amsa ta k'arasa kusa dashi tana k'are masa kallo tace, "how was your day?." Nan ma yayi mata Banza ta sake yin murmushi tace, "I like your acting prince, ko baka ce komai ba indai zan kalle ka is enough."
Tana fad'ar hakan ya fita daga d'akin ta bishi da kallo har ya b'ace ta kalli Rauda tace, "Ina son brother d'in nan naki Rauda, yayi min ta ko ina class d'in sa na burge nu over, I feel like naje nayi hugging d'in sa ko zanyi dad'i a zuciya ta." Kallon ta Rauda take yi itama ita take kallo tana murmushi Rauda taji babu dad'i a ranta amma in ta tuna wata k'ila shine yace musu y'ar uwar sace sai taji shi take jin haushi daman tasan ba sonta yake yi ba.
Muhibba tace, "promise me zaki sanar dashi sak'ona zaifi sauraron ki a kaina dan naga yana ji dake, please sister help me before nayi loosing hankalina." Rauda ta k'ak'alo murmushi tayi amma bata ce komai ba ganin hakan ya saka muhibba tace, "Thanks you Sister, ina jiran feedback duk abinda yace ki sanar dani please. I'm coming" ta fad'a tana ficewa Rauda ta bita da kallo bata san lokacin da ta fara jin hawaye na sakko mata ba.
Idanun ta ta goge ta hana kuka a zuciyar ta tace, 'Meye naki na kuka Rauda?, daman kin san ke ba tsarar shi bace ba irin su sune daidai dashi; ta ya zaki had'a kanki da ita...? kalli kyawun ta fa ba dole ma ya so ta ba, ke kuwa kalle ki kowa yasan baku dace ba gwara ki samarwa kanki lafiya kar kiyi asarar hawayen ki.' Bata san ya shigo ba sai ganin sa tayi a kanta a tsaye yana kallon fuskar ta da mamakin meya saka ta kuka lokaci d'aya.
D'ago kai tayi ta kalle shi da hannu yayi mata alama da kukan me take yi, bata iya bashi amsa ba ta sake goge idanun ta tace, "Wacce ta fita yanzu Dr muhibba naji suna ce mata tace na fad'a maka tana son ka." Wara idanu yayi ya zauna a kan kujerar da take kusa da ita yana kallon ta sai kuma ya saki fuska annuri ya bayyana a kai yace, "Shine kike kuka?." Batayi zaton zaiyi magana ba ta d'auka zaiyi banza ne sai taji yayi sai ta kalle shi ta girgiza kai had'i da tab'e baki tace, "A'a wannan daban wancan daban."
"Ohhh!" Ya furta ba tare da yace komai ba yana kallon ta.
Duk sai ta tsargu ta kasa sakewa jin idanun sa a jikin ta sai ta sunkuyar da kanta jikin ta nayi mata wani iri abinda bata tab'a ji ba, hannun ta taji ya rik'e guda d'aya bata kalle shi ba sai abinda take ji a jikin ta taji ya k'aru. Baiyi magana ba itama batayi ba bai kuma ce komai bai kuma saki hannun ba yana rik'e dashi laushin hannun sa yana ratsa ta sosai, wani lokacin har bata so ya rik'e ta dan tasan zaiji hannunta da tauri ba irin nasa ba amma ya riga ya saba yana son rik'e hannun ta. Sun jima a haka kafin ya saki hannun nata ya koma danna wayar sa ba tare da yace komai ba itama kuma batayi karanbanin cewa ba.
*Bayan Kwana biyu.*
Haka suke zaman asibitin shiru babu wanda yake magana daga gaisuwa ya amsa babu abinda yake had'a su kuma kullum a wajan ta yake wuni har dare bata ma sanin lokacin da yake tafiya. Ranar saturday kwana biyar kenan da yi mata aikin k'afa sosai take jin dad'in ta bata jin ciwo ko kad'an a cikin ta har ji take ma zata iya takawa in aka barta, kula sosai take samu a asibitin tun ranar da sukayi magana da Muhibba bata kuma ganin ta ba sai taji dad'i a ranta domin har ga Allah haushi take bata.
Tana kwance da safiyar asabar likita ya shigo tare da Asad bai yi mata magana ba ya k'arasa ya d'ago ta ta zauna sosai yace, "Zaki fara tafiya." Dad'i taji a ranta sosai ta rik'e hannun sa sosai ya mik'e da ita aka zare k'afar daga cikin abinda take ta tsaya da k'afar mara ciwo likitan cikin harshen larabci yake sanar da Asad da ta taka gabad'aya ta tsaya ya gani.
Kasawa tayi sai a lokacin take jin zugi a k'afar wanda bata jishi sa ba farkon aikin Dr Khalifa da ya shigo yace, "Gwada tsayawa mu gani zaki iya." Ba musu take k'okarin mayar da nauyin jikin ta kan waccan amma ta kasa sabida zafi take mata.
"Kina jin ciwo?" Dr Khalifa ya tambaye ta. Kai ta d'aga alamun eh Dr Khalifa yace, "sake gwadawa zaki iya." A hankali ta tsayar da ita ta tsaya sai kuma tayi saurin d'agawa ta jingina da jikin Asad ya rik'e ta yana kallon su, wani iri take ji in ta had'a jikinta da nasa duk sai ta rud'e daurewa kawai take.
"K'afar tayi kyau amma zata dinga amfani da sanda before ta warware gabad'aya" babban likitan ya fad'a da larabci yana kallon Asad. Sandar aka kawo guda d'aya mai kyau a lokacin aka bata akace tayi tafiya da ita Asad ya koma gefe cikin ikon Allah sai gashi tana takawa da duka k'afar tata a hankali.
Asad yaji dad'in hakan ganin anyi nasara k'afar ta ta dawo akace ta zauna amma ta dinga yawan tashi tana takawa, ita kanta murna take na dawowar k'afar dan bata d'auka zata dawo d'in ba sai murmushi take tana jin dad'i Asad yana lura da ita ganin nata farin cikin sai nasa yaji ya k'aru.
*Nigeria.*
Mama an sauka a katagum ita da Suhaima tun daren juma'a ta wayi gari asabar a gidan aka dinga zuwa ana mata gaisuwa wanda basu samu damar binta can ba. Hydar ya shigo Aliyu ya shigo amma mamaki take da bata ga Asad ba bata tambaya ba amma ta baza idanu tana jiran ganin ta inda zai shigo.
Hydar ne ya kuma shigowa ta kalle shi tace, "Tun safe nake zaman jiran ganin Asad ban ganshi ba har azahar tayi, na kira shi bana samun sa yana ina?."
Hydar yace, "baya nan Takawa ya aike shi."
"Ina ya aike shi?."
"Ban sani ba" ya bata amsa a tak'aice yana fita da mamaki ta bishi da kallo kafin ta mik'e ta kimtsa ta nufi b'angaren mai martaba dan bata amince da wannan batun ba. Tasan daman weekend ne shi kad'ai yake zaune yana karatu kamar koda yaushe ta zauna bata ce komai ba har sai da kai inda zai tsaya ya kalle ta yace, "Ya akayi? Naga kamar akwai magana a bakin ki."
"Allah ya k'ara maka lafiya wani abu ne ya d'aure min kai, Naga kowa ne banga Asad ba na tambayi Hydar yace min mai martaba ya aike shi amma bai san inda ya tafi ba shine nazo na tambaya naji in babu damuwa." Mai martaba yayi murmushi yace, "Kina son Asad sosai, bakya so ya matsa daga kusa dake amma kuma bakya son abinda yake so." Shiru tayi bata amsa ba yace, "K'warai Asad baya nan baya Nigeria gabad'aya na aike shi Egypt."
Gaban ta ya fad'i jin ya ambaci Egypt ta kalli mai martaba tace, "Takawa me yaje yi Egypt?."
"Aiki na."
Tayi shiru tana jin abinda yace tunani ta rasa abinda zatace a haka ta taso ta fito haka kawai zuciyar ta bata amince da abinda yace mata ba.
Da yamma tana zaune Suhaima ta shigo ta zauna a k'asan carpet tana kallon ta tace, "Mama wani abu nake ji a gidan nan ana fad'a but ban sani ba ko Mama ta sani." Mama tace, "meye shi?."
"Ji nayi ana cewa Asad yayi auren sirri ya tafi Egypt shida matar tasa, haka ne?." Gaban Mama ya fad'i ta kalli Suhaima da sauri tace, "wa kika ji yana maganar nan?."